TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“AUNTY N,don Allah ki dawo, Allah bazan zauna ba nima idan baki dawo ba,kinmin alqawari amma shine baki cika ba? kullum kuka nakeyi,amma abby yace bazanzo ba,a nan zan zauna,kema kiyi zamanki”. Dukkansu ita da nadeeya basuga shigowarsa ba,bare baaba ramatu dake sallah saman abun sallah.
Kai tsaye ya sanya hannu ya zare wayar dake magale a kunnen fadeela,ya juya a nutse yana fita a dakin,ransa na zafi.
“Hello..
…hello,nadeee” sautin lallausar
muryarta ya sauka a kunnensa lokacin da yake magala wayar a kunnensa,ya lumshe ido yana jin tsanar
“Nawa kike da bugatar a biyaki ki dawo cikin ravuwar da kika riga kika shigeta cikin shirin faruwar hakan?” Cak komai ya tsaye mata,cikin mamaki ta kalli number,ta sake tabbatarwa number nadeeya ce,don dama ita din bata taba ajiyar number dinsa a wayarta ba,saita sauke wayar daga kunnenta kawai ta katse kiran,saboda bata jin zata iya tsaiwa ta saurareshi.
Komawa tayi ta lafe a gado,zuciyarta na wani bugawa a jejjere,kwata kwata ta manta da sautin murvarsa cikin kwanyarta,don bata sake iinta ba sai a yau din. Idanunta ta mayar ta kulle,sautika biyu na tsalle tsakanin qirjinta da kunnuwanta,sautin innocent fadeela,da kuma sautin deep and husky voice dinsa.
Labbansa na qasa ya cije lokacin da ya fahimci ta kashe masa waya ne,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa,sai ya sake tunzura ya kuma dannawa number din nata kira.
Karar wayarta a karo na biyu ya
sanyata bude idanunta,ta kalli wayar,kamar ba zata daga ba sai kuma taga nadeeya dince,ta dannan Koren shudi ta sanya kiran a handsfree
“Muddin kika sake kashemin waya sai na baki mamaki,don har cikin gidanku zan iskeki,nace nawa kikeso a biyaki ki dawo bakin aikinki?”
Yayi maganar cike da wata izza da gasaita.
Tunawa tayi da matsayinta a rayuwa,da kima da kuma darajarta ta diya mace,wannan ya bata qwarin gwiwa,ta mige ta zauna sosai saman gadonta
“Bazan dawo ba!” Ta gaya masa kanta tsaye,ta kuma dakata tana jiran abinda zaya fadi. Har tsakiyar kansa yaji saukar muryar tata da kalaman da suke nuna rashin toro ko daga gafa
“Dole ki dawo,ki qarasa abinda kika fara shiryawa,dole ki dawo inason naga iya gudun ruwanki na kuma qurewa wasanki gudu donki tabbatar da banbamcin dake tsakaninmu” ya fadu a zafafe. Katse wayar kawai tayi saboda yadda deep voice dinsa ke shiga kanta sosai,tana ratsa jijiyoyin jikinta tana jin kamar yana a cikin dakinne. Ba iya katse kiran ta tsaya ba,gaba daya wayarma ta kashe,ta koma ta kwanta rub da ciki idanunta a lumshe,muryarsa naci gaba da yawo a kanta.
Abu guda daya data sake amincewa dashi,yana da izza izgili da girman kai,ta fahimci akwai damuwa sosai cikin muryarsa, damuwar kuma bata rasa nasaba da ciwon fadeela daya sanyasu dukka a damuwaryanaso ne ta dawo taci gaba da kula da fadeelan duk da ransa baiso hakan ba.amma shi baisan hanyar da zai lallaba mutumin da yake neman abu a gurinsa ba,a haka zata koma? kai koda da sigar lallashi yazo mata bata jin zata koma,bare a yadda yazo mata cikin izza da gadara,sai ta gyara kwanciyarta ranta na turereniyar abubuwa guda biyu,tausayin fadeela da kuma takaicin kalamansa.
Hannayensa ya yarfar,nadamar karbar kiran dayi mata tayin dawowa na lullubeshi,tunda yake babu wani mahaluki daya taba masa abinda tayi masan, ji yayi kamar yayi jifa da wayar,ya juya wayar a hankali yana qare mata kallo
“Ta yimin dai dai, kuma haka shike nuna baka shirya samarwa ‘yarka lafiya ba” sautin murvar Dr jarma ya ratsa kunnuwansa. Da sauri ya waiwaya bayansa yana duban mahaifin nasa,sam baiyi zato ko tsammanin ganinsa a gurin ba,tunda ma tun wancan satin sukayi sallama dashi ya tafi china,kuma a galla zai kwashe wata guda bai dawo ba. Rusunawa yayi ya rage tsahonsa
“Barka da warhaka”
“Aikai za’a yiwa barka muhammadu” daga furta hakan da yayi sai ya juya kawai ba tare da yace dashi komai ba. Da hanzari ya rufa masa baya sukaci gaba da takawa yana qoqarin cimmasa,abinka da sabon jini nan da nan ya tarar dashi,suka jera kafada dashi ya sake russunawa yana gaidashi sanda suke shiga verandar da zata sadasu da dakunan
“Barka kadai,ya goqari?” Ya amsa masa cikin salon gatse, kafin ya samu amsar mayar masa nadeeya ta fito daga dakinsu riqe da hannun fadeela wadda ke takawa da gafafunta,fuskarta a washe matuqa,tamkar ba ita ya fita ya bari da hawaye shabe shabe ba
“Yauwa,ku qarasa mota ku jirani ina zuwa” Dr jarma ya fadi yana takawa zuwa office din likitan. Hankalinsa rabuwa yayi biyu,sallamarsu akayi ko kuma Dr dinne ya sallami fadeelan da kansa?,ganin zai batawa kansa lokaci sai kawai yabi bayan dr jarma da tuni ya isa office din Dr anwar.
“In sha Allah nan da gobe ma zakuga ta mige sarai, damuwa ai matsala ce a zuciya,ita kuma zuciya idan ta samu cikakkiyar lafiya ta kubuta daga damuwa,to dukka gangar jiki ma zata samu cikakkiyar lafiya da kuzari” kai dr jarma da yaga shigowar toufeeq ya gyada
“Gaskiya ne dr,zama da damuwa dama a zuciya saidai idan kai kaso,sai kayita zamanka a haka tunda haka ka zaba,kowa kuma yayi rayuwarsa cikin farinciki” sarai dr anwar ya fahimci magana ce me harshen damo, tunda bawai yau ko jiya yasan familyn JARMA ba,kusan abubuwa da dama tare dashi akayi.
Hannu dr iarma ya bawa dr anwar yana masa godiya,sannan ya tako yana fita. Kallo daya touteeq yayi masa sai yayi masa nuni da zasuyi waya,yabi bayan abban nasa.
Motocinsa hudu ne a parking lot na asibitin, motar da yafi zama a ciki yaga ya nufa ya bude,sai yabi bayansa. Har ya sanya kai ya tsaya ya waiwayo yana kallonsa
“Af,bari na maka bayani don sauke haqqinka na uba ko? zan kaita inda aka saba kula da ita,idan ta samu lafiya kaje ka daukota,idan kuma kaie din,ba ita kadai nakeso ka dauko ba,har wadda ta kula da ita din zataci gaba da kulawa da ita nakeson su dawo cikin gidan suci gaba da rayuwarsu yadda suka saba” daga haka ya shige motar sajjad ya rufe,ya sanya drivers suka tashi motocin suka bar harabar asibitin.
Sam kanshi ma a sanann a daure yake,bai kawo masa tunanin inda dr jarma din zai kaita ba
“Sir….zamu tafi ne?” Muryar jibril ta shiga kunnensa,sai ya amsa alamu da hannu,ya matso da motar ya bude masa ya shige ya rufe suma nasa motocin sukabi kwalta.
[11/09, 3:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI *
Book 02 Page 03
Fitowarta kenan daga kitchen bayan ta gama shan coffee ta maida mug din,qofar falon da taji an bude da sauri ya sanyata waiwayawa da sauri,cikin zallar mamaki ta tsaya cak,tana duban fadeela dake takowa da gudu tamkar almara ta cukukiyeta tana kiran sunanta da garfi. Zubewa tayi saman gwiwarta tana riqe yarinyar da kyau tare da tattaba likinta a rude
“Fadee,waye ya kawoki? kinsan gidan nan? ya jikin naki? kin warke ne?”
“Babu wani ya jikinta,kamar dai irin da gasken nan kin damu da ita” muryar afifa da sautin muryar fadeela ya fiddota daga daki ya wanzu a falon
“Wallahi,gashi mu mun laluboki mun kawo kanji” nadeeva ta fadi tana takowa Sosai cikin falon,tare da kallon kusurwoyinsa,mamaki yana saukar mata tare da tarin tambayoyi fal cikin kanta. Migewa tayi dauke da fadeela tana murmushi
“Babu yadda zanyi ne sister nadeeya,kada kiji haushina” ta furta tana mata tayin gurin zama