TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Idanunsa ya lumshe tsigar jikinsa na zubawa lokacin daya tuna abinda ya farun mintunan da suka shude,yana ji a ransa inama lokacin ya sake dawowa,yayita kuma tabbata a haka ba tare sa ya wuce ba. Ido suka hada dashi,wani qasaitaccen murmushi da yayi matuqar qara masa kyau kwarjini da cikar kamala ya sakar mata yana lullumshe mata idanunsa. Sai take ga kamar dariyar mugunta yake mata,wannan yasa ta langabar da kanta gefe tana jifansa da harara, abinda ya zama kamar wani wasan soyayya ko cusa haushi a zuciyar hajiya da kuma haseena.
“Ina zuwa madam?” Ya fada cikin matuqar girmamawa,kanta tadan juya kadan,ta cije tana qoqarin tauna maganar da zata gaya masa,saboda cikin jikinta takejin akwai idanu a kanta
“Zanje duba fadeela”
“Uhmmmmm” taji muryar hajiya qarama na fadi, idanunta kuma a kanta.
Kai tsaye ya miqa mata hannunsa,ta gane me yake
da bugata,kuma a lokacin taji ba zata iya wofantar da
abinda yayin ba,duk da zuciyarta cike take da
haushinsa, amma wani abun kana yinsa ne ko ka barshi saboda wasu idanu masu guda da illa.
Cike da mamaki yaga ta garaso a hankali ta dora zara
zaran yatsunta cikin nasa,wani irin abu me dadi ya saukahar tsakiyar zuciyarsa,ya maida hannun ya rufe ruf ya kuma jawota a tausashe ya zaunar da ita a kusa dashi cinyoyinsu suna gogar na juna
“Ba yanzu ba,bakijin dadi,Dr raheema na hanya” ya fada yana sake game hannuwansu guri guda. Cikin nacin kallo da son tantancewa hajiy qarama ke garewa säahar kallo, gabanta na wani irin faduwa,tana hango canji muraran daga fuskarta,lokaci daya ta qara wani haske da sheqi
“Innalillahi,na shigesu” ta furta lokacin da zucivarta ta
ayasa mata
“Kodai ciki ne?”
“‘Ina fatan haka” taji muryar toufeeq yana sake matse
hannunsa cikin nata. Sai a lokacin ta fahimci a fili tayi maganar kuma a bayyane. Cikin sauri da son gyara takunta ta saki murmushi
“Ameen Allah,lallai da duk duniya na kasance mutum ta farko wadda zatafi kowa farinciki,fatana ko yaushe ahalina su qara yawa,don haka nake qoqarin ganin samun dai daito tsakaninka da ‘yar uwarka” yadda hannuwansu ke cikin na juna yaci gaba da taba zuciyar meenal din,bata da zarrar cewa toufeeq din komai,saboda ayau din kwarjinin dake kan fuskarsa kamar ya zarta na kullum,sai gani sukayi kawai ta miqe ta fice da sassarfa tana toshe bakinta saboda sabon kukan da yake shirin qwace mata.
Hadiye wani abu me tauri hajiya qaraman tayi cikin murmushin yaqe
“Allah ya raba lafiya” banbarakwai sahar taji, mamaki ya sake kamata lokacin da taji yana amsawa da ameen, sai ta faki idanun hajiyan ta zame hannunta daga nashi, saboda yadda yake yamutsa hannun nasa cikin nata tamkar yana amfani da damarsa ne.
Zaman bai dauki lokaci ba Dr raheema ta qaraso,cikin girmamawa ta gaida hajiya qarama,ta amsa mata cikin izzar nan tata amma faran faran
“Ki dubamin ita da kyau don Allah” tace da Dr raheema.
Murmushi ta saki kawai
“To hajiya,in sha Allah” ta fadi tana maida hankalinta a kansu
“Ku qarasa ciki,ko da clinic zakuyi amfani?” Kai Dr raheema ta girgiza
“Inajin basai munje ba, indai ba worsening matsalar tayi ba”.
Tana zaune daga gefan gadon ta rasa ta yadda zata yiwa Dr raheema bayani,wannan wanne irin abun kunya ne shikam,yana neman bata kunya da tona mata asiri.
Sai kace wata virgin zai dauko mata likita?.
Dai dai lokacin ya buda qofar dakin ya shigo yana sauke boyayyar ajiyar zuciya sanda idanunsa suka sauka a kanta,tsaida shi hajiya qarama tayi tana masa kukan tare da fadin yan wulagantata,ya canza totally mace na son rabasu,shi kam bai iya wannan jidalin ba, bugu da qari a yanzu ma shi bashi da wani guarantee a kanta,tana cikin suspect, bazai kuma taba nutsuwa ba har sai ya samu yaqini da tabbacin komai
“Sir batace komai ba” Dr raheema mai yawan fara’a haquri da sanin ya kamata ta fada. Hannuns a qirjinsa ya tako ciki
“First night ko first day dinta zance,shi tayi a dazun, so kamar yanayin tafiyarta nake gain ya canza,and jikinta akwai dumi sosai tun dazun, duk da taqi yarda da hakan” ya furta dukka bayanan idanunsa a kanta,yanajin kamar ya hadiyeta. Idanunta fal da qwalla ta dubeshi, tanason sake harararsa ne ko zata zamu relief din abinda yayi mata
“Nifa bazawara ce Drya za’a ce saboda na samu wani ciwo dalilin hakan?” Ta fada cikin dan zafin rai. Idonsa ya lumshe murmushin nan nasa dan kadan me taushi na subuce masa,can qasan ransa kuma yana jin babu dadi,don da alama kalmar BAZAWARA din ta tsaye mata a rai.
Cikin kulawa Dr raheema ta ajjiye kayan aikinta,ta dawo dab da ita ta zauna tana game hannunta cikin nata
“Ba abun mamaki bane yadda kowacce mace ta banbanta haka suma mazan suke da da banbanci kin gane?” Tayi mata bayanin a taqaice,jin tayi shuru sai ta dora
“Yadda muka banbanta a halittar jikinmu hama suma mazan suka banbanta,kowacce mace akwai yanayin halittar ta,jikin wata jikinta yafi na wata tsukewa,kamar yadda suma mazan halittarsu ta wani tafi ta wani,zai iya yiwuwa a auren mace na biyu ta fuskanci jin ciwuka da sauransu, saboda qila ta qara samun tightness,sannan shi kansa mijin nata data sake aura wala’alla yafi na farkon cikakken.
“Don Allah Dr” ta fada da sauri tana rufe idanunta.
Wannan karon sai da dariya ta qwacewa Dr raheema
“Kin fahimta kenan ba sai na garasa ba?” Kai ta gyada mata sau biyu da saurinta. Shima murmushi yayi mai sauti wannan karon, wanda ya tsaye ma säahar,taji kamar da biyu yayishi,sai ya juya yana nufar qofa don ya basu guri.
A nutse ta sake mata bayani yadda zata fahimta,hakan ya sanyata tunani me yawa
“What a difference?” Ta samu kanta kanta da fadin hakan,sai kuma taji haushin kanta ya kamata
“Difference din ganiya” ta sake fadi tara fada ita da zuciyarta har tana tsuke garamin bakinta.
“HUGUMA*
_TABARMAR KASHI_
Book 02 Page 33
Dr raheema na fita ta maida key jikin qofarta,ta koma ta kwanta saman gadonta tana sauke numfashi, idanunta a lumshe bacci ne fal cikinsu. kuma shi take da bugatar vi saboda a jiyan tashin ciwon fadeela bai bari ta samu isashen bacci ba yau din kuma ta tashi da wuri da zummae zasu fita aiki,wannan gaddarar ta fada mata.
Wasu hawave suka sake zarto mata idanunta a lumshe tana bitar abinda ya faru tsakaninta da shi,tun daga sanda ya sanyata cikin jikinsa har zuwa lokacin data wuce bandaki.
Kadan kadan taji ana taba gofar, sau biyu aka murda,sai kuma taji an juya an bar gurin ba tare da anyi knocking ba.
Wayarta dake saman kanta ta jawo tavi kiran nadeeya
“Fadeela ta tashi ne?”
“Eh ta tashi, abbynta ya shigo yanzu suna tare, ashema bakuje office din ba” kai ta gyada
“Eh”
“Amma lafiya?, anty N naji muryarki wani iri?”
“Ba komai kawai inajin kasala ne,please ki kula da fadeela, kada ki bari ta fita gaba daya daga sashen,sannan kada kowa ya bata komai sai abinda kika girka da hannunki, shima kaemi motsa daga kitchen din har sai kin gama,idan ta rage kuma a zubar, kada a ajjiye” Nadeeya ta danyi mamaki, amma kuma tasan sahar din kulawarta ga fadeela ta musamman ce, don haka ta amsa mata da
“To,in sha Allah, sannu Allah ya bada lafiya,ki huta sosai don nasan akwai rashin samun cikakken bacci ma jiva,gwara ma da yaa toufeeq ya hana zuwa aikin yau,kya samu ki huta”