TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Dariya sosai ta fara qyaqyatawa wanda hakan ya tabbatar mata itace ta sauyawa takardun guri daga dakin Mahmud din zuwa nata dakin
“Idan asiri baici ba,ai ita kissa bata da magani” ta furta kai tsaye
“Fauziyya” maji dake hawaye ta kirayi sunanta
“Alfarmar sayyadina rasulillahi S A W,yadda kika birkitamin rayuwar aure na,kika hanamin jin dadin gidan mijina,ina rogar ubangijin sammai da gassai ya hana miki jin dadin aure har gaban abada” daga haka batà qara ba ta wuce dakinta.
A daren taso tabar gidan,saidai kuma abubuwa biyu suka hanata,na farko tunanin yadda zata hada kudin ticket din da zai maidata Algeria,sauqinta daya babban yayanta yayi mata visa ba dadewa ta shekara biyar, kuma shekara biyu kacal taci a ciki,abu na biyu kuma tana tsaka da hada kayanta jini ya balle mata, koda ta isa bandaki sai ta iske bari ne tayi,barin dan tayin cikin da jini ne zalla,ko ubansa baisan dashi ba, dole ta haqura ta kwana tana bigin kanta da jinin barin da take zubarwa,cikin taimako da dafawar Allah zuwa asubah ya tsagaita.
Kafin gari ya waye ta gama shirya komai nata dana yaran,a daki suka iskota ta kamasu ta shiryasu tsaf tana shirvasun toufeeg yace
“Jiya abba baiyi bacci ba maji,kije ki bashi magani”
“Zaiyi toufeeq” abinda ta iya ce masa kenan.
Ga kaya ga murdawar mara ga yara haka ta ratso
falon gidan zata fice a gidan
“Ina zakijemin da yara?” Ta tsinci muryar mahmud
JARMA yana fadi. Kafin ta waiwayo ya iso gabanta,yasa hannu ya zame hannun toufeeq da nadeeya
“Ba dasu kika zo ba ina ke ina tafiyar mana da zuri’a?”
Fauziyya dake tsaye a gefe ta fada, ranta fes duniya yau sabuwa a gareta. Gaban fauziyya ya isa da yaran
“Na mallaka miki su halak malak”
“Na gode yaaya,na tabbatar ko ranar qiyama ummee zatayi alfahari da kulawar da ka bani” tayi maganar tana goge hawayen munafurci. Cikin dakiya da zallar jarumta maji ta tako gaban yaran, ta dora hannuwanta duka biyun saman kawunansu ta furta
“U’izukuma bi kalimatillahit tammat min kulli shaidanin hammah wamin kulli ainin lammah” ta maimaita sau uku sannan tace
“Ya ubangijin sama da gasa,ina neman alfarma daga gareka cikin karamci da adalcinka tare da isar ga bugatar wanda aka zalunta,wannan addu’ar da nayi musu koda ta zama ta qarshe, koda nisan dake tsakanin uwa da ‘ya’vanta ya wanzu a tsakaninmu kasa addu’ar tayita bibivarsu har garshen rayuwarsu,na damqa amanarsu a hannunka ya mijibancin al’amarin bayinsa” daga haka ta miqe,ta kuma kalli idanun fauziyya
“Zan sake miki addu’a a Karo na biyu kafin na wuce, yadda kika shiga tsakanina da farincikina,ina roqon
Allah ya gimtse naki farincikin a sanda baki taba zata ko kawowa ba, addu’ar da nayi miki rannan,da wadda nayi miki yanzu kadai sun wadatar, ba zan sake kai qararki gaban Allah ba,sai kuma jiran sakamako”.
Bata tabajin furucin da ya shiga jikinta yayi mugun kassarata ba irin wannan,amma sam batason majin taga kamar ta karaya,wadan nan addu’o’i biyu suka kasa barin ranta,suka kuma sanyata qudurar anivar kassara duk wani abun da zai zamewa maji farinciki a rayuwarta daga nan har zuwa garshen numfashi,wannan ne kuma ya sanya FADEELA a target na hajiya garama tun ba’a san da wanzuwar mahaifiyarta a duniya ba bare ita kanta.
[02/10, 2:56 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 41
Sosai zuciyar maji tayi wani irin nauyi,girman kaidai da dabi’ar fauziyya maras kyau tana ratsata,saidai kuma
ta tuna da wata magana guda daya na cewa
MURMUSHINKA GUDA DAYA TAK NA IYA SANYA
FADUWAR GABA GA MAQIYINKA don haka fa waiwayo tana dubanta da murmushi saman fuskarta
“Kin riga da kin makara,saboda bana tunanin lokacin da za’a rubuta littafin qaddarata kina gurin,na tabbatar da cewa kedin baki da matsayi a wajen Allah da kike da qarfin ikon canza qaddarata,na rigaki tsayawa a gaban Allah,na kuma rigaki ambatonsa” dariya fauziyya ta saki
“To sannu sufiya”. Kasa ci gaba da tsaiwa maji tayi a kitchen din,ta juya ta fice a hankali, zuciyarta cike da mamakin wanne abu ta aikatawa fauziyya haka data cancanci irin wannan sakamakon?.
Ranar hatta da yaran basu wuni gurinta ba,sun wuni gurin fauziyya ne tana nan nan da su, sakamakon a ranar mahmud yana gida,saidai yadan fita ya dawo. Fauziyya ita tayi girkin rana da dare, kamar yadda tayi girkin dare,a lokacin idan ka shigo gidan zakayi tsammanin itace matar gidan idan ba kasan cewa matar gidan shifa bace.
Tana daga daki tana sauraren dabdalarsu, yadda suka wuni suka kai kawo haka ta wuni kwance a daki. Sai bayan magariba lokacin da mahmud din yake zaune a parlor suna kallo da yara fauziyya ta shirya komai saman tray ta shigo dashi falon
“Yaaya,don Allah kayi magana da maji,tayi haquri ta tashi taci abinci, yau duka bataci komai ba” dubanta yayi yana jin tausayin fauziyyan yana kama zuciyarsa tare da kallon kyawun halayenta
“Ke kamar baki da zuciya?,kamar baki damu da abinda ta aikata miki ba?,har yanxu fa bandage ne a kanki fa na abinda ta aikata miki” cike da kissa da kisisina tayi gas da kanta
“Bazan manta kyatatawarta a kaina ba,shi yasa bazan iya fushi da ita ba” Numfashi yaja sannan yace
“Ni dai bazanje ba,idan kuma ke zaki iya bismillah”.
Hawayen da suka wanke mata fuska ta share,duk abinda suke tattaunawa a tsakaninsu tana jinsu. Zuciyarta ta gama amanna da cewa abinda fauziyya ta shirya aiwatarwa a kanta me girma ne, abu guda ne zai zame mata garkuwa tsakaninta da ita shine addu’a. Bata ko marmarin gain fuskarta,don haka salin alin kafin ma ta kai ga shigo mata daki ta miqe ta murza key ta koma ta kwanta. Tana jinta sanda take knocking da magyar ta bude, zallar kukan dake cin zuciyarta ya hanata koda qwaqwaran motsi. Fauziyyan da koda wasa bata tana kama mata aiki ba koda ciwo zai kayar da ita, fauziyyan da sautin INA KWANA da sunan sun kwana gida daya bai taba hadata da ita ba,fauziyya da bawai ta girka ba,wanda ita ta girka dinma qoqari take ta juye ta cinye, amma wai yau saboda zallar kissa ita ke biyota daki da abinci?.
“Ki gyaleta,ta hadiyi baqar zuciyarta ta mutu ita kadai” shine abinda mahmud ya fada yana sake qufula, tare da garin yarda da dukkan maganganun da fauziyya ta gaya masa.
Har dare ya raba tana kwance tana kuka,sanda agogo ya nuna mata qarfe uku na dare ta yiwa kanta fada,ta sauka daga saman gadon ta bude gofarta a hankali ta fito bandakin dake tsakanin dakunanta guda biyu dake manne da parlor. Ta kammala alwalar tana shirin fitowa mahmud ya shigo. Cikin sanyin jiki da karyewar zuciya take kallonsa, amma sai ya dauke kansa gefe ya rabata ya shige bandakin yana turo mata qofa.
Da qyar ta qarasa dakinta, ta zube saman abun sallar tana bude sabon shafin kuka,abin ya fara wuce tunaninta,ko a lokacin da Mahmud din ke ganiyar karayar arziqinsa wani abu makamancin wannan bai taba hadasu ba,ko da yaushe cikin gogarin kwantar masa da hankali take tare kuma da yin amfani da dukkan abinda take dashi saboda aci gaba da tafiyar da hidimar gidan yadda aka saba.
Sallar data kwana tana yi ita ta sanya sassauci cikin zuciyarta,a washegarin kuma ta tashi da wata irin dakiya tawakkali tare da qarfin zuciya,ta sameshi a tsakar gida yana bawa fauziyyan kudin cefane a madadinta. Ko a fuska bata nuna masa komai ba,ta tsugunna cikin girmamawa ta gaidashi yadda ta saba,yana fiffisgewa ya amsa mata,sai itama fauziyya ta rusuna tana gaidata.