TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Wanne magani kenan ake bata yanxu?” Tambayar da tazo kansa kenan,ya kuma miqe a nutse ya sanya flip flops slippers dinsa yana baro sashen.

Tuni ta gama cin nata abincin ita da fadeelan, nadeeya ce tayi saura,don haka suka barta a falon suka wuce daki don ta shiryata ta bata maganinta tasha. Toilet ta kaita, kamar ko yaushe yanzu ta fara canza pattern na wankanta, zata hada mata kayan wankan gaba daya,tayi mata tsarki ta wanke mata bayanta da sauran inda hannunta bazai kai ba,sauran kuma saita tsaya tana kallonta tayi da kanta, tanayi tana gyara mata har su kammala. Sanda yayi sallama dakin basuji shi ba,suna bandakin tanata tsokanar fadeelan saboda yau ta dage bayan nata ma zata wanke da kanta.

A nutse ya garasa shigowa,ya maida murfin qofar ya rufe, idanunsa suka sauka akan dressing table din fadeelan inda kayan baccinta maganin nata da sauran tarkacen kayan nata suke.

Kai tsaye ya dauki robar maganin yana dubawa,sak irin maganin da yasan yana siyowa da kudinsa va damgashi ga hajiva garama har na tsahon watanni shid,bayan wata shidan kuwa baya taba batan lissafi zai sake kawo wani na wata shidan. Bude robar yayi ya zazzago maganin. Shine asin da asin babu banbamci, sai ya maida murfin maganin ya rufe ya maidashi inda vake vana fadin

“Hasbunallahu wani’imal wakil” wane sashe na zuciyarsa kuma na tambayar sa,waye yake bata kudin siyan maganin?. Lokaci daya komai ya rikice masa,lissafi yaso qwace masa,ga hajiyan da wani magani sabanin wanda ake baiwa fadeelan, ita kuma gata da irin maganin fadeelan ba tare da yasan waye yake siya ba.

Komawa yayi ya zauna saman sofa bed,har ta gama wankan suka fito tana tsane mata gashinta da hoodie towel din data rataya mata saman kanta.

“Abby….” Fadeela ta fadi, abinda ya jawo hankalin sãahar sal tadan ja da baya tana boye jikinta a qofar.

“Abbyyy…” Maganar yarinyar ta magale mata a maqoshi,a hankali yatsun hannunta dana gafafunta suka fara motsawa suna shacking. Dukkaninsu suka fahimci abinda ke shirin faruwa da ita,lokaci guda kuma kowanne ya taso da mugun hanzari suka nufo fadeelan,shi ta gaba sãahar ta baya,suka kuma isa gareta lokaci guda tare da rarumota cikin jikinsu saboda kada tayi mummunar faduwar da zata ji ciwo.

Shi yayi nasarar rungume fadeelan,yayin da säahar ta saki wani irin kuka mara sauti cikin narkewar zuciya tana kiran sunan fadeela

“Shshshsh” ya fada yana dora yatsansa saman lips dinsa duk da cewa shima cikin tashin hankalin yake

“Stop crying” ya sake fada da muryarsa da taynkaushi.va mige a nutse ya kaita saman sofa bed ya kwantar da ita sosai yana ambaton sunan Allah a ransa. Ta dauki tsahon kwanaki masu dama rabon da ta samu wannan attack din,kusan zai iya cewa harma ya manta,ya kuma tsammaci lalurar ta tafi kenan. Idanunsa suna kan agogo yana yana lissafa adadin mintunan kamar yadda ya saba,yayin da sautin kukan säahar ke shiga masa kunnuwa,sai ya dinga jin kamar ana soka masa allura cikin qwaqwalwarsa,wani irin ciwon kai ya fara saukar masa kadan kadan har cikin idanunsa.

Wannan karon bata gara ba akan mintunan data saba yi, ta bude idanunta a hankali tana kallonsu.

“Aunty N,faduwa nayi ko? ‚na dauka na warke na daina faduwa” furucin da ya sanya sãahar tsananta kukanta,hawaye masu yawa suka jige mata fuska ta kasa controlling dinsu, gaba daya hannuwanta suna cikin na fadeela ta rigeta tsam

“Zaki daina daughter, zaki daina in sha Allah very soon, in sha Allah,in sha Allah, i promise” duk da yadda kansa yake sarawa hakan bai hanashi dubanta ba,bai taba ganin hawayenta da kukanta ba kamar yau, kamar ma ta fishi shiga tashin hankali. A nutse ta mige ta dauko tissue ta dawo ta zauna a gefanta tana share mata majinar data zuba daga bakinta hade da yawu. Hannu fadeelan ta miga tana share mata fuska

“Ki daina kuka anty N,na dauka na warke ne, amma ai na saba” migewa tsaye yayi yana saka hannunsa a aljihun wandonsa kansa yana sake sarawa,yanajin kalaman fadeela har cikin zuciyarsa,yana jin kamar ya gaza.

_WASHEGARL

Cikin jikinta fadeelan ta kwana a daren jiya,da safe ma tace yau ba school, tunda juma’a ce ta zauna a gida ta haqura. Da safer tayi mata duk abinda ya kamata, duk da cewa Zuciyarta babu dadi,haka gangar jikinta babu kuzari, amma haka ta daure ta koma sashensu.
Me share share ta samu yana aikinsa,kamar yadda toufeeq din ya maidashi akin sassafe, shida zuwa bakwai ya gama komai,idan kuma ya makara saidai ya bari kuma sai bayan sun fita office. Gefe yaja yana sadda kansa gasa sanda yaji sallamarta

“Good morning maa” ya fada ba tare daya kalleta ba

“Morning”‘ ta amsa masa tana wucewa. Samun kanta tayi da kallon gofar dakin nasa, ba alamun da mutum a ciki,duk da cewa daman kusan kullum kamar haka qofar yake, amma yau sai taji abun yadan ja hankalinta, duk da haka ta watsar ta isa nata dakin tana shiryawa a hanzarce don kada tayi late.

Ta zarta lokacin shirin nata, amma ga mamakinta har ta kammala shiryawa ta fito bataji wanann sassanyan qamshin nasa da duk safiya yake gaya mata kammala shirin boss din ba. Ta iso parlor babu kowa, dama jacob ne zaka samu ya raya falon da qamshin abincinsa, shima tunda yaje gida wanna yayi qaura. Yankewa tayi ta fita farfajiyar gidan saidai kafin ma ta qarasa duka taga babu motocin da suke fita din ko guda daya

“Good morning madam,ya jikin oga din?” Muryar jibril dake magana cikin girmamawa ya furta. Da dan sauri ta waiwayo

“Jikin oga kuma?” Ta tambayi kanta da kanta,ta tambayi jibril din kamar zubewar kimarta ne, saita amshe kawai

“Jiki da sauqi alhmdlh”

“Allah ya qara afuwa”

“Ameen” ta amsashi. Qafafunta babu qarfi sam ta koma ciki, taja burki a falon ta tsaya tana tunanin meye abunyi?, at last taga babu wani abu da ya rage illa ta shiga dakin da kanta.
[25/09, 8:56 am] +234 703 451 7171: “HUGUMA*

“_TABARMAR KASHI_’

Book 02 Page 30

Sau biyu tana dora hannunta akan handle din tana janyewa. Tana tunanin yadda zata shiga dakinsa yau a karon farko, tana kuma tunani da tsoron kada ya fasarata.

To amma kuma zuwan ya zame mata tamkar wajibi,don kowa a gidan da zai buqaci jin yanayin lafiyarsa ita zai fara tuntunba daga bakinta kuma za’a so aji komai. Uwa uba fadeela, data tashi ta tabbata abby din zata nema.

Kuma ko babu komai rama alkhairi sai dan halak, shine mutum na farko daya fara kulawa da kuma lura da sauyawarta lokacin da ciwon kanta ya motsa.
Sama sama ta soma jin kamar muryar meenal daga falonsu,wanda daga shi sai hallway din da kuma bedrooms dinsu. Bata sake tunani na biyu ba ta murda gofar kawai ta shige. Dai dai lokacin da yake kwance cikin duvet, bai jima da komawa ya kwanta ba,saboda a jiyan bai samu wani cikakken bacci ba,gaba daya idanunsa ne suka soye yanata hada lissafin da bai samu nutsuwa a kansa ba sai da zuciyarsa ga bashi gamsuwa da rinjaye akan bangare guda. Koda ya samu baccin sai tashi farkawa ba sai qarfe shida na safe, alfijir ya fara ketowa sosai. A razane ya sauko, hanzarin da ya sanya kanshi sarawa ya rige kan yana takawa a hankali ya wuce toilet. Alwala ya daura ya zauna yayi sallarsa,ya duba first aid kit ya balli maganin ciwon kai yasha. Yana gama lazumin ya lallaba ya koma gadon yana sake qudunduna a duvet din. Idanunsa ya lumshe a hankali,yanayin da vake tsintar kansa kowacce asuba ya fara sauka ga jikinsa, abinda bai taba tunani ba saboda ganin yadda ya kwana yana fama da tunani bacin rai da kuma ciwon kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected