TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Yaa moha” ta fada da muryarta me tsananin sirantaka, muryar na dan rawa kadan alamun kuka takeson saki. A nutse ta maida jikinta ta kuma maida qofar dakin nata ta kulle,kwanyarta nason tuna mata wacece ita?. Gefan gado ta koma ta zauna tana qarshe cikon hailalarta da take guda dari duk rana safiya da maraice 200 kenan. Gefe daya kuma yarinyar na mata yawo a idanunta

“Haseena,’yar hajiya qarama” wani lungu daga qasan zuciyarta ya cillo mata amsar,bayan ta gama qirga kwanakin da hajiyan tace mata zata dawo,haka yake,indai lissafinta yayi dai dai kenan. Qaramin murmushi ne ya qwace mata a fuskarta,tadan girgiza kai kawai,wanann itace haseena din da hajiyar keta kururuta zuwanta?,saita girgiza kai kawai,ta sauka a hankali ta dauke fadeela ta maida saman gadon itama ta koma ta kwanta tana jan musu duvet. Dakin ya dauki shuru na wasu sakanni,tana ci gaba da salati qasan ranta idanunta a lumshe,dukka hallway dinma shuru,babu alamun motsin mutum kwata kwata.

Sanda ta maida qofar ta rufe duka akan idanunsa,a nutse yana kuma qarawa fuskarsa rashin walwala ya sauke dubansa akan yarinyar. Idanunta cike suke taf da qwalla,ta ritsashi da idanunta tana kallonsa da kyau,sai kawai ta zame jakar dake rataye a kafadarta ta ware hannunta da zummar rungumarsa. Da sauri yaja da baya yana jifanta da wani kallo

“Meenal,meye hakan?” Ya furta a mugun dake,tsaiwa tayi sak tana kallonsa,hawayen da take maqalewa na gangarowa

“I want to be in your arms yaa toufeeq please” ta furta tana sake sakar masa kuka. Tsaiwa kawai yayi yana kallon ikon Allah,yadda qanqanuwar yarinyar da aka haifa ta taso a gabansa ta zama haka,totally ma ta canza,tun daga yanayin halittarta kawo dabi’unta,tayi wani irin girma kamar sa’arsa,duk da cewa ‘yan watanni ne tsakaninsu da nadeeya,amma sai ka rantse gaba take da nadeeya. Ganin baice komai ba sai hannunsa sa ya goye kawai a qirji yana mata wani kallo da batasan inda ya dosa ba,saita sulale a gurin ta duqa saman qafafunta tana sake sabon salon kukan

“Yaa toufeeq,i can’t take it anymore,duk tsahon wanann lokacin da naqi kula kowa kai nake jira,na saka raina da duka burina a kanka” sai taci gaba da gaya masa abinda ke ranta kai tsaye ba kunya ko kwana kwana,gaba daya kansa sake daurewa yayi,yaushe ta zama mara kunya haka?.

“Look meenal” ya kirata yana sake hade ransa da kyau,a hankali ta daga idanunta da suka jagale da hawaye ta kalleshi

“Dama ina wasa dake?” Ya fadi da wani irin tone da ya fidda kwarjininsa har ya kusa bugar da ita,qoqarin tattaro dukka dauriyarta tayi,da gasken gaske takeson toufeeq fiye da lokacin baya kafin dawowarta da ganin da tayi masa yanzu,a wannan lokacin da tayi ido hudu dashi,bawai cikin hotunansa da take faman wallafawa ba,ta sake jin cewa a shirye take ta karba toufeeq din daga hannun kowacce mace

“Kaga alamar da wasa nake yaa moha?,kaga alamun wasa cikin soyayyar da nake maka?” Ta tambayeshi idanunta cikin nasa hawaye na sake wanke mata fuska. Abun sai ya koma bashi mamaki qwarai,yayi shuru yana karantarta

“Yaa toufeeq please say something,kayi magana mana,da gaske nake maka,bazan iya jurar rasaka ba,i can do anything a kanka,ciki kuwa harda kashe kaina muddin na rasaka!” Cikin ‘yan mintuna qalilan ya gama fahimtar da gasken take fa,duk abinda take fadi din da gaske ne zata aiwatar,shi sai yake ganin ma kamar ba cikin saitinta take ba.

“Muje parlor” ya fadi yana nuna mata hanya,dole tana buqatar guidance and council,ya kamata ta fahimci shi din a matsayin yaaya yake a wajenta bawai masoyi ko mijin aure ba. Kamar ba zata tafin ba har sai da ya maimaita mata yana sake hade fuska,sai tayi gaba tana qoqarin tsaida hawayen nata.

A hankali ta bude idanunta saboda gajiya da tayi da rufesu din,baccin kuma da take sanya ran zuwansa baizo ba,batasan me zuciya da kunnuwanta suke jira ba,sai ta miqe a nutse tana gyara top din rigar baccin jikinta me rubi biyu,ta jawo dankwalinta me santsi daya dace da rigar ta daure kanta ta zuro qafafunta ta sauko daga saman gadon. Gaba daya ta manta da batun shan ruwan duminta,ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofa. Duk yadda taso ta dauke kai daga kallon qofar dakin da a dazun yarinyar ke tsaye amma ta kasa controlling din idanunta. Ba kowa yanzu a qofar dakin,saidai kamar a bude take bawai a rufe yadda ta saba ganinta ba kullum. Batasan dalili ba amma sai ta samu kanta da jan qaramin tsaki,ta juya tana fita a gurin.

Muryarsa a tausashe kunnuwanta suka fara jiyowa,a lokacin da yake magana da haseena cikin son kwatanta mata abinda ke cikin zuciyarta ba me yiwuwa bane

“Ka fahimceni yaa toufeeq,nima ba yin kaina bane,bansan lokacin da zuciyata ta kamu da matsanancin sonka ba,a yanzu kuma ba abinda kunnuwana zasu iya fahimta sai yaren sonka kawai” daidai lokacin idanunsa dana sãahar dake qoqarin wucewa kitchen suka hadu waje daya. Har tsakiyar kanta taji kalaman yarinyar da muryarta me bala’in sirantaka,ta lumshe idanunta tana daukesu daga kan toufeeq din,wani tsanarsa na darsuwa a ranta. Shikenan shi bashi da aiki sai jefa soyayya a zukatan ‘yan mata?,su kuma basu da aiki sai zub da kima da martabarsu?,shin wai basajin kunyar roqon soyayya daga gurin namiji?, namijin ma irinsu toufeeq din me zafin kai izza da jin cewa shi din wani ne?.

Bata sake bari kunnuwanta sun jiye mata komai ba ta daga qafarta ta shige kitchen din da dan sauri kadan,sai a lokacin ya dauke idanunsa daga kanta,baiga komai saman fuskarta ba kamar yadda ya saba gani a baya akan fuskar AMEESHA a duk lokacin data fahimci wata mace tana ra’ayinsa,koda kuwa bata furta ba,a ranar babu zaman lafiya ko kuma kwanciyar hankali. Idanunsa dake dauke da wani irin maganadisu wanda ke sake dasa mata kakkaifar soyayyarsa cikin zuciyarsa ya zube mata cikin kowanne lungu na jiki da zuciyarta.
[21/09, 2:02 pm] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 22

• “Kije ki huta tukunna” ya fadi wa meenal din yanason shawo kan matsalar ta lumana,bayason akai ga ta qure dan garamin haqurinsa a kanta.

“I will be back to you koda baka nemeni ba” bai iya cewa komai ba don shi har yanzu yarinyar na bashi mamaki ne.
Banda ita din itace tabbas inda watace bata isa ya tsaya bata lokacinsa wai yana saurarenta ba. A abinda ma tayi masan na binsa har bedroom dinsa,abinda fadeela ce kawai ke da wanna damar, tabbas zafafan maruka ya kamata ya bata,to ko a yanzun ma baisan meye ya sanyayashi har haka a kanta ba.

Iska ya furzar a bakinsa,yana shirin migewa
Jacob ya shigo. Cikin matuqar girmamawa ya gaidashi

“Sir do you need something b4 i prepaid breakfast?”
“Warm water as usual” ya furta yana murza yatsansa a goshinsa.

“Jacob” ya kirashi da wani hanzari wanda har sai da
Jacob din ya dan zabura,sam ya sha’afa tana cikin kitchen din,sannan idan ya tuna da kyau sleeping dress ne kaman a jikinta,duk kuwa da cewa ko ina nata a rufe yake, amma ya tabbatar indai silky clothes ne dole su fidda wani abun koda baka sani ba.

“Come” ya fada yana gyara zamansa cikin sofas din.
Gabansa ya qaraso ya tsugunna

“Daga yau na canza maka kitchen, zaka koma amfani da extra kitchen dake backyard”

“Okay sir, but inason gaya maka ma,if possible zanje gida gobe, momma na bata jin dadi” mutum ne shi mai bada uzuri ga ma’aikatansa,musamman idan ya shafi lalurar iyali ko ta iyaye

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected