TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“No worries* ya amsa masa a taqaice. Yana zaune har zuwa sanda Jacob ya dauko key na kitchen din,ya juya yana fita ta qofar gaba don yace kada ya bude ta qofar dake cikin main kitchen din.

Har ta tafasa ruwan tana jira ya huce sai taji batajin shansa, tayi taku biyu zata fita sai taja ta koma tana jan tsaki, kwata kwata bata qaunar sake giftasu bare taga kayan takaicin dake faruwa a falon. Tana mamakin yadda mace zata zub da kanta tayi tallan kanta a inda ba’a san daraja ko kimarta ba,me yasa suke rufe idanunsu.ne wai kaman basusan halinsa ba?. Sake jan tsaki tayi a karo na biyu,ta bude daya daga cikin locker’s na cabinet din inda aka jera duk wani kayan tea,ta fara hada milk tea, ko bata sha ba ta ajiyewa fadeela,ta tabbatar kwana biyu tayi missing girkinta.

Sai data gama hada komai tsaf sannan ta javo. daya daga cikin kyawawan kitchen stool din dake kitchen din wanda suke iri daya sak da jikin cabinet na kitchen din. ta zauna a kai. Hannunta a qirjinta tana duban tukunyar da ta fara tafasa,qamshin cardamom na ‘ana’ana da madara da flavour yana tashi kadan kadan yana cika kitchen din. Zuciyarta nason fadawa tunani amma tana turewa daga ranta, don batason yau kwata kwata ta kwana da wani ciwon kai bare a gobe ta rasa karsashin fita office a goben kamar yadda Dr jarma ya umarta

Tun kafin ya qarasa shiga qamshin yayi masa maraba,ya lumshe ido yana sanya kai a kitchen din, bakinsa dauke da sallama gasa qasa. Bata waiwayo ba ta amsa sallamar tana sake gyara yafen dankwalinta,kadan kadan yake dora idanunsa akan fuskarta,da gaske baiga alamun komai saman fuskartata ba. Ya garasa shigowa yana dauke kansa,ta qasan idonsa kuma vana satar kallon coffee pot dinta dake shirin fara tafasa wadda va tabbatar a nan gamshin da ya game sassan yake fita.

“‘Ina kwana” ta fada ciki ciki tana murza yatsunta wadanda ke da sauran shatin jan lallen biki a jiki

“‘Idan mutum vace bakisan daraiar ilkinki ba fitsarrun bakin nan naki yace zai qaryata right?” Ya fada yana kafeta da shanyayyun idanunsa. A bazata maganar tazo mata,sai ta daga fararen idanunta ta zubesu a fuskarsa wani abu me gyalli daga tsakiyarsu ya fusgeshi da qarfi ya maida nasa idanun ya lumshe, abinda dama yaketa son gani kenan, tsakiyar qwayar idanunta

“Ya kamata Jacob ya ganki a haka?” Yayi mata tambayar da wani yanayi da ya tunzurata

“Ya kamata Jacob ya zama yana shiga kitchen dinan?, Kai

ka damu dashi,ni dukkanku ban damu da wanzuwarku ba” shine abinda takeson gaya masa,amma sai wani sashe na zuciyarta ya kwabeta,uwa uba kuma a yau batason bashi damar da zai shanye mata tea ya barta da zafin lebe don haka sai ta kauda kanta kamar ba da ita yake ba. Hakan da tayi sai yaji abun ya zafafeshi

“Am talking to you” ya fada adan kausashe,har ta dago kamar zata kalleshi sai ta fasa, ta sauka daga kan stool din tana nufar tukunyarta sannan tace

“To” ta dauki garamin rariya ta fara tace ruwan madarar da ya tafasa yasha kayan qamshi. A nutse ta gama juyewa,ta ajiye kayan ta juya tana barin kitchen din.

Tukunyar data bari a wajen ya kalla,ya danja tsaki yana tambayar kansa tsoron yace ta dafa masa yakeji ko kuwa?. Kai ya girgiza

“No, bayason raini ne kawai” dole qanwar naqi ya jona coffee maker din yana hada kayan tare da addu’ar Allah yasa yayi dadi.

K’arfe sha biyu da rabi na rana suna zaune a falon, ranar farko kuma karon farko da ta taba zama a falon bawai wucewa ba,hakan ya faru ne saboda nacin da fadeelan ta dinga yi mata

“Please anty N mu zauna kawai a nan,nan din yafi dadi, kuma sai nafi sanin abby ya dawo,daxun yayimin alqawarin kawomin cookies” kumatunta ta kama taja tana murmushi

“Bakin kwadayi,shi yasa kike qara kumatu” hirar da suke ne ta tsaya cak, fara’ar fuskarta kuma tayi gaura duka lokaci guda. A nutse ta tashi daga durquson da tayi tana duban fuskar IG celebrity MEENAL YA’AQOUB AJI,wadda ta shahara da dora mabanbanta hotuna da fuskokin MT JARMA da Instagram basa gajiya da recommending mata ita tamkar ta buqaci haka daga garesu. Ta bangaren MEENAL itama sanda take takowa nata idanun suna kan fuskar säahar din, wani irin abu me girma yana zarta mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafarta. Jikinta dukka ya fara fidda gumi tana jin wani rudani yana shigarta. Addu’a takeyi qasan ranta. Ya Allah ya sanya ba wannan bace matar yaa moha, Allah ya taqaita wahalarta ya sanya ba ita bace,muddin hakan ta kasance tasan babu ta inda zatakai labari wajen hada kyanta da take taqama dashi dana sãahar din.

Duba daya tal ta yiwa meenal din ta dauke idanunta daga kanta,saboda cikin qasa da minti daya sautin muryarta ya tabbatar mata itace haseenar hajiya qarama. Yadda ta debeta ta watsar itama ya bata amsar cewa ita dince, itace matar da tasha gaban burinta takeson kawowa cikar burinta barazana,wannan tunanin ya sanya ta sake tsuke fuska itama

“Ukhtie….abby dinki yana ciki?” Ta tambaya don gudun karya tsarinsa, kamar yadda a dazun ya gargadeta kan bayason irin wannan zuwan

“Ya fita” fadeelan ta amsa mata a taqaice don ba wani sabo ko shaquwa bane me yawa a tsakaninsu,don meenal din na hannun mahaifinta tun tana da shekara goma sha biyar, kawai lokaci lokaci ne take zuwa musu hutu,tunda kuma ta shiga university ma bata sake zuwa ba sai yanzu data kammala

“Okay” meenal din ta fada, cikin satar kallon sahar ta samu waje ta zauna, ta kuma dora qafa daya saman daya ta fidda tsadajiyar wayarta ta fara dannawa.
Tamkar batasan Allah yayi ruwanta a gurin ba sukaci gaba da hirarsu da fadeela, nadeeya duka yau din bata nan, don haka sai su biyu. Har zuwa lokacin sallar azahar yayi ta janye fadeela suka wuce dakinta suka bada farali, sannan suka fice daga sashen don komawa sashensu,saboda yau tana da sha’awar yi musu abincin dare abinda tunda ta dawo gidan batayi ba.

Bayan sãahar din meenal tabi da kallo, tana da izza fiye da tata tana kuma da miskilanci da jin kai da yafi nata yawa yanzun ta ina zata fara quntata mata? ta wanne bangaren ya kamata ta fara ajiyewa rayuwarta bacin rai?, sai kawai ta gyara kwanciyarta cikin qayatattun kujerun falon tayi kwanciyarta hankali kwance,ta dauki. waya ta turawa hajiya qarama tex don kada tayita bulayin nemanta cikin gidan.
[21/09, 2:02 pm] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

“TABARMAR KASHI’

Book 02 Page 23

*****Tsaye take cikin kitchen din tana qoqarin rufe lunch bag din fadeela dake dauke da tarkacen kavan beak dinta na makaranta. Sanye take da wata lafiyayyar tattausar abaya sagar dubai, da aka sagata da zare da kuma yadi me tsananin kyau da tsada. Maroon color ce wadda aka yiwa ado da bagi da kuma zaiba a jiki. Daga ciki kuma wani lallausan cotton lace ne maras nauyi wanda aka yiwa dinkin riga me dogon hannu da straight skirt. Daurin kanta ya zauna das sakamakon yadda ta yiwa gashin kanta gammo daga baya ta kuma daura dankwalinta ya zauna mata dass da samfurin daurin dankwalin nan da ake kira zahra buhari. Wani irin tattausan gamshi take fitarwa,wanda ya zame mata al’ada ya kuma kama suturunta da kyau. Turaren wuta na kaya me asalin tsada wanda take samu takanas daga masu abun wato garin mahaifinta BORNO. Wani irin sassanyan kyau tayi a safiyar kyau me ratsa idanu da shiga zuciya,ba tun yau ba shigar laffaya na daya daga cikin shigar dake matuqar qara mata kyau da matuqar da kwarjini, takan koma kamar balarabiya tare da fita a ainihin yarenta na SHUWA-ARAB.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected