TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“‘Wallahi wallahi wallahi tsautsayi yasa ta yimin kan kara sai nayi mata na itace, idan tana tutiya da ita din gwanace ni uwarta ce a wannan fannin, zatasan ni mansura cikakkiyar KARA DA KIYASHI ce daukan mara sani” abinda ta furta kenan qasan ranta, kafin daga bisani muryar dr mahmud ta mamayi kunnenta

“An samu ticket din? na ranar yaushe ne?, alright zanyi managing na jira ranar” sai ya sauke wayar daga kunnensa a hankali yana furta

“Alhamdulillah” yadda fuskarsa ke nuna annuri yaja hankalinta

“‘Wacce tafiya ce haka me muhimmanci zakayi?”

“Ni kadai tafiyar ta shafa,so ba wani abu bane na daban” ya fada yana kashe wayarsa. Binsa tayi da kallo,haka kawai taji jikinta bai bata ba,so amma koma inane zatabi diddigin tafiyar har ta san inda zashin. Hannuwanta ta sake tajuya tana ficewa don dauko masa plate din abincin data manta.

Tana saukowa daga stairs din hajiya qarama na shigowa falon,kallon kallo suka yiwa junansu, kafin hajiya garama ta buda baki da qyar tayi sallama. Kamar yadda tayi sallamar da gyar haka mansura ta amsa mata da gyar tare da dauke kanta, tazo zata wuce ta gabanta tamkar batasan da wanzuwarta a wajen ba. Matuga da gaske abun ya daure mata kai,don bata taba kawowa a duniya akwai lokacin da zaizo mansura tayi mata irin wannan abun ba

“Ina yaya yake?”

“Tunda kinsan kan gidan ai kinsan inda zaki sameshi” ta amsa mata da gatse, tunda ta sani aduk sanda tazo gurinsa itace ke shaida mata yazo din

“Idanma da gatse kika fada yanzun zaki ga cikar aikin irin na fauziyya” tana kaiwa nan ta kama stairs din tana hawa,hajiya mansura ta bita da kallon zallar mamaki baki bude.

Ya danyi mamaki da yaji ana knocking,ya miqe ya buda qofar, mamakinsa ya qaru da ganin fauziyya da safen

“Muje falo” yace da ita ha fito ya biyo bayanta. Nan falon saman suka zauna,yana qoqarin zama ta fashe masa da kuka

“Subhanallahi, lafiya me yake faruwa?” Hajiya Mansura da tayi gaggawar dawowa don taji abinda ke faruwa duk da tasan fauziyyan bata taba wata magana me muhimmanci tsakaninta da yayan nata a gabanta ba,ta saci kallon fauziyyan cikin sa’a suka hada idanu

“‘Maganace ta ahali yaya,zan samu sarari?” Kai ya jinjina vana karbar plate din daga hannun mansura yana cewa

“Mansura bamu guri”

“Tom” ta fada zuciyarta kamar zata fado daga qirjinta saboda tsananin takaici. Shekara da shekaru har yanzu babu abinda ya sauya a irin wannan abubuwan dake faruwa,a wannan shekarar kadai ta soma gain abinda fauziyya ta nema dr jarma bai bata ba
AURAWA TOUFEEQ HASEENA.

“Me ya faru?” Ya sake tambayarta,sai ta sake sakin hawaye

“Ba shakka yaaya toufeeq ya auro yarinyar da zata rabamu dashi” mamaki ya kamashi

“Kaman yaaya? wai säahar kike nufi?” Kai ta jinjina masa

“Itafa,tun daga lokacin da tazo gidan komai ya canza,shi kansa toufeeq ya sauya,a yanzun ban isa da shi ba,sai abinda tace,hatta da gaisuwa bankai ta shigo ta gaidani ba,saidai idan mun hadu a compound na gidan” Shuru yayi hannunsa saman bakinsa yana mamaki, vasan wanne aure akayi da manufar auren dake zukatansu dukka su biyun,to yaushe hankulansu suka hadu guri guda har suka fara mu’amalar da mutum me taurin kai da kafiya irin toufeeq sahar zata fara juyashi ya soma daukan maganata?

“Yanzun me va faru?” Hawaye sosai ta matso

“Waini yarinyar zata kalla tace daga yau tanamin kashedin babu ni na fadeela, ta soke bata duk wata kulawa da nake bata,ta shiga ta fita ta canza komai har na makarantarta,abinci bata magani,hatta da daukan yarinyar yanzu babu wanda yake da wannan ikon idan ba ita ba,hatta kaita makaranta yanzun ta maidashi wuyanta”. Ga mamakinta murmushi ne ya subuce akan fuskarsa yana dan girgiza qafarsa,cikin ransa aminci da gaunar sãahar tana ratsashi

“Banda abinki da rigima irin taki, kefa yanzun kin girma,da meye kikeson kiji? da shekarunki koda kasuwancinki koda kula da fadeela? ina cewa ke sauqinki ne ma,aiki aka rage miki da nauyi ko?” Sosai ta girgiza,amma kuma ba zata saare ba sai taga abinda ya turewa buzu nadi

“Haba yaaya,haba yaaya, ubanta ma nina raineshi bare diyar? ta yaya kawai don an aurota zamu sake mata kula da diyarmu haka sakaka? yadda yanzu duniya ta zama babu gaskiya,sai a hada kai da mutum a cucuka”

“‘ah dakata fauziyya,duk ba za’a samu wannan daga sãahar ba ina kyautata mata zato, banda abinki meson naka ai shima naka ne,ki bar musu diyarsu don Allah, ki cire ranki daga wannan qanqanin abun,duka ba damuwa bane”

“Yanzu ba zata tsawatar ba kenan yaaya?” Murmushi ya saki yana girgiza kai

“A’ah ni bazan shiga wanna maganar ba, diyarsu ce, inda ace kina qorafi ne akan nadeeya to itace ‘yarki sai kuma inda qarfinta ya qare” Boom taji wani abu cikin kanta,karo na farko data fuskanci haka daga
gurinsa, bai taba ganin hawayenta ba ba tare daya zartar da abinda take muradi ba. A yanzun shurun da tayi ma
kamar bai fuskanci bacin ranta ba,janta ya shiga yi da
hira yana yi mata tayin abinci

“Alhamdulillah na qoshi, zan wuce gida na baro meenal
ita kadai,kasan kuma baquwa ce har yanzu”

“‘Gaskiya ne ya kamata tazo tayi kwana biyu su saba da mamarta da yar’uwarta”

“Zatazo” ta amsa masa a taqaice,saboda ta qagauta ta

fita daga cikin gidan ko zata samu damar yin
kyakkyawan tunani akan yarinyar,sai takejin kamar wata masifa ce ke tunkarota.

System ya tura mata da tarin wasu ayyuka da zata
tattara masa bayanan guri guda. A nutse take aikin
tamkar ma bata office din, lokaci lokaci tana ji a jikinta
tamkar yana kallonta ne,amma kuma duk sanda ta daga kan nata don ta tantance sai taga idanunsa yana saman system.

Mintuna goma sha biyar kacal suka rage lokacin
break ya cika,har a lokacin bata motsa ko ina ba tana zaune tana gogarin tattara aikin da ya bata hatta da wayarta ma a kashe take, don batason tayi wani abun ma da magana zata shiga tsakaninsu.

A karo na barkatai ya sake satar kallonta, shi kansa
bazai iya tuna wani abu a rayuwarsa da ya yiwa adadin satar Kallon da yayi mata ba ba tare da shi kansa vasan satar kallon yake ba. Dai dai lokacin data zura hannuwanta ta cikin lafayar ta kuma bayan wuyanta tana gogarin tattare gashin data nannade, santsinsa ya sanya ya ware da kansa yake kuma damunta a wuya. Hakan ya baiwa laffayar damar zamewa, lallausan gashin nata dake da wani irin bagi da daukar idanu ya ware a kafadarta ta hagu. Tana qoqarin mayar da mayafin kira ya shigo ta wayar office din. Ta daga kai zata kalleshi suka hada ido, basarwa yayi cikin shan gamshi va kuma hade rai sosai, don bayason ta fahimci tun ba yanzun ba idanunsa ke kanta

“Kin manta aikinki ne?” Ya fada a dake,har ta dan juya
idanunta zata sauke masa harara sai tayi saurin gyara
kallonta,tayi rolling qwayar idanun tamkar me yin fari.
Wani irin ayalli idanun nata suka bada,a dole ya rusunar da kallon nasa daga kanta. Migewa tayi a nutse ta isar ga wayar ta daga,ta kara a kunnenta tare da yin sallama da nutsatsiyar muryarta me sanyi da taushi. Cak ya tsaya daga singing din da yakeyi sautin yana shigar masa kunne

“Idan kuma namiji ne fa?” Yaji tambayar ta fado a ransa,sai ya rige biron a hannunsa yana juyashi tare da son tsinkayo muryar waye a wayar.

“Ma sha Allah, ina fatan Khadija Muhammad girema ce?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected