TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Idan kinason zaman lafiya kiyi baccinki kawai” ya fada yana aza mata nauyin girjinsa idanunta kawai taja ta rufe gam, bata sake cewa komai ba, saidai tuni ta yanke hukuncin abinda zata aikata. Ba jimawa bacci yazo yayi gaba da ita, ya gyara mata kwanciya cikin jikinsa yakai lips dinsa yayi kissing goshinta,kamar zai cinyeta da idanunsa wani irin murmushi na fita akan fuskarsa

“Rigimammiya ta” ya fada softly yana jin zuciyarsa kamar wadda aka canzawa muhalli.

Afwan,yau na baku shi a rarrabe kuma page d’ai
d’ai,ayimin uzuri na wuni a asibiti ne. Amma gobe komai zai zama normal in sha Allah, Na gode da kasancewa tare dani.
[27/09, 8:42 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*

_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 34

Yamamci lis ta farka, ta samu baya dakin,sai abinci data tarar, toilet ta shiga tayi alwala ta dawo tayi sallar la’asar, kamar ba zata taba abincin ba amma wata irin azababbiyar yunwa takeji, rabonta da abinci tun toasted bread da taci da milk tea. Tana bude abincin tasan nadeeya cs ta girka,ta diba kadan taci ta maida ta rufe.

Taji dadin jikinta sosai, hakanan taji ta gaji da zaman dakin, tana zura slippers dinta aka turo gofar.

Toufeea jarma ne,cikin sassanyan yanayinsa,yana sanye da shirt da trouser dukkansu baqaqe,shigar data sake gara masa kwarjini qwarai, ta kuma fidda ainihin zallar kyansa,idanunsan nan masu kaifi a yau sun koma masu laushi, saidai cike suke da tasirin was abubuwa masu tarin yawa. Qarasa shigowa yayi cikin dakin qamshinsa yana mamaye ko ina,ta dauke kanta tana jin haushin yadda tabar qofar a bude har yaketa samun
damar shigo mata kai tsaye. Hannunsa goye a qirjinsa ya
garasa ya jingina da dressing table,da lallausar muryarsa
din nan yace

“How are you feeling?” Ta qasan idanunta ta gasa masa harara. kamar ba zata amsa masa ba sai kuma tayi magana ciki ciki kamar wadda aka viwa dole
“‘Da sauqi”

“Ma sha Allah Alhamdulillah” ya furta a nutse

“Su sajjad suna parlor suna jira” ya fada yana dubanta
still, don tunda ya shigo ko sau daya bai dauke idanunsa daga kanta ba. Da sauri ta daga kai suka hada ido,sai kuma ta basar, tana jin zumudin ganin afifa har cikin ranta, ta garasa sanya slippers dinta ta mige tana takawa.
Har ta gotashi taji an riqe hannunta a tausashe, da dan mamaki a fuskarta ta juyo suka hada ido ta watsar da kallon nata gefe

“Tsayani mana” y fadi yana sakar mata hannun. Dole ta dakata har ya cimmata suka jera,tare suka ratsa hallway din har suka isa falon. Idanun afifa akanta, murnarta itama ya gaza boyuwa. Rungume juna sukayi suka zube saman kujera tana gaida sajjad

Lokacin da yake ce maya ya jiki? Allah ya sawwaqe sai da taji kamar gasa ta tsage ta shige, tadan saci kallon toufeeq shima ita yake kalla. Ya fahimci kallon da take masa,sai ya tabe baki ya kuma watsa hannayensa alamun ba ruwansa baisan komai ba,a kunyace ta ja afifa suka shiga kitchen tana nemana abinda zata basu.

Karon farko data fara baqi kenan, afifa da ta lura tana ta wani bove dariya ita ta tayata suka shirya komai cikin tray, tana shirin dauka toufeeq din ya shigo. Har saman fuskarsa taga yaji dadi, yasa hannuwansa ya tallafe nata hannayen dake dauke da farantin yana mata wani irin kallo

“Jeki huta, thank you” banda tana gudun jiwa kanta ciwo da tuni ta zare hannunta daga qasan tray din, amma dole ta jira ya karba sannan ta zame nata hannuwan a hankali.

Koda ya fita ta laluba kitchen din ba afifa ba dalilinta, ta tako ta fito sai ta cimmata tsaye a tsakanin hallway dinsu

“Ke nake nema ai”

“Tuni na yiwa kaina qiyamullaili na fito….. Kai azaba,irin wanna kallo haka kamar babu gobe?, bestie kamar zaku cinye junanku?, kuyi haquri ku ragewa ‘ya’yanku fuskar da zasu kalla taku mana karku cinye kanku tun yanzu su su rasa abin kalla…

” Batasan ta dimawa afifa
dundu ba sai data gantsare tana fadin

“Wayyo hayatee,zata wujijiga maka baby” surrender sãahar tayi daga bakin qofar dakin tana riqe da handle tana duban afifa dafe da bakinta

“Bestie,ke yanzu har kina zancan daukar ciki?” Harara ta watsa mata

“Yo me za’a jira?, daga ni har mijina dukkanmu jarumai ne kuma munason junanmu, ribar auren soyayya kuwa ai haihuwa,ki zauna ke kam,nan da wata takwas zaki rakani labour room in sha Allah” dariya ta kubcewa sahar,abinda ta jima batayi ba, ta maida gofar ta garaso dakin tana neman gurin zama kusa da afifa

“Sannu da qogari bestie na yarda har yanzu da sauranki a hankali”

“Allah am serious, kedai ba kin zauna ba?, da alama ma sai yau aka bare gyadar” ido sahar ta fidda tana dubanta sosai

“Inji wanne munafukin?”

“Ba wani munafuki, ina ta kiran wayarki ne naji baki dauka ba,da na nemi nadeeya tacemin yau tun safe baki da lafiya, kina can kina bacci ke da oga,yanzun suka fito ita da fadeela, nasan halin bestie na da taurin kai da tsanar maza,nasan ba abinda zai kaiki bacci tare da MT JARMA haka siddan,saidai idan ya miki qarfa qarfa ne,idan kuwa hakane to ya burgeni wallahi, Allah yasa yayi miki ciki ma yau din ko jiyan, bansan actual ranar ba” ta fada tana ayaqyata dariya abinta, sai kuma ta sassauto ganin fuskar säahar din ba walwala, kamar ma hawaye ne cikin idonta. Kama hannun nata tayi

“Me kuma ya faru bestie?”

“Amanata vaci bestie,ni bance masa ina da bugatar auratayya ba,yasan auren meye mukayi amma sai ya yaudareni yaci amanata?” Saura kadan dariya ta sake qwacewa afifa,amma ta tabbatar idan tayi dariya gayyar zata watse ne

“Hana bestie, kamar bakiyi karatun addini ba?,haduwata da hayatee yasa na sake sanin waye taoufeeq sarai, may be ma fiye da ke tunda ke baki maida kanki ba,na miki imani da Allah jinki yayi kawai da kunne, amma dai baiyi niyyar aikata miki komai ba, kawai an samu akasi ne,wanda dama ba yadda za’a yi kina halalinsa ya zauna yana kallonki, saboda me?,bayan Allah ya bashi damar yayi komai ba komai?” Hannunta ta qwace daga na afifa, saboda ta karanci ba wani goyon baya zata bata ba,zata zartar da abunta ba tare data nemi shawara daga wajenta ba

“Kiyimin bayanin ciwon fadeela sosai,inason naji yadda yake fiye da bayanin da kika taba yimin, hankalina yana tashi, inason na kawo garshen ciwon a tare da ita,ina zargin matar nan zargi me qarfi,na tsaneta bestie haka kawai zuciyata ta wayi gari bata gaunarta sam sam” gyara zama afifa tayi

“Gaskiya ba’a yimin tarba me kyau ba,masu juna biyu ai sai da abun kwadayi,abani abu na saka a bakina sai naji dadin yi miki bayanin” harararta tayi tana migewa

“Zakiyi bayani ne da kyau,me bestie na takeso?”
Idanunta ta juya

“Me zan zaba ma?, kitchen din bestie din nawa kamar ba na matar aure ba,ba wasu ajiyayyun snacks ba komai,ko girki banga alama ba,ina dukka fikirarki ta girke girke?”

“Zaman nazo ma kenan” ta bata amsa tana harararta
sannan ta juya ta fice. Mintuna kadan ta dawo mata da
abinda ya samu ta ajiye mata bayan ta gama ta tattara hanakalinta ta fara yiwa säahar din bayani

“EPILEPSY Ciwo ne na kwakwalwa da ke iva shafar kowacce halitta me rai hatta dabbobi ma suna yin ta
Kin San ita kwakwalwa da nerves su ke controlling jikin
gaba daya suna anfani da electric signals ne wajen aika sakonni a sassan jikin Dan Adam.
Misali ko Abu ka kalla ko kaji sauti nerves din da ke cikin
idanun ka da kunne su zasu sarrafa wnn abun da ka gani
ko ka ji su Maida shi kwatankwacin electric current su
aika ma kwakwalwa ita Kuma ta tantace maka kaza ne ka gani ko ka ji”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected