TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Da zaki taimaki kanki da kin nemo mayafin arziqi kin suturta jikinki,duk da naga alama bakisan darajar jikin naki ba” ya qarashe maganar yana sake dauke dubansa daga kanta.

Maganar tayi mugun sokarta,saita samu kanta da sauke dubanta ga jikinta,tunda dai tasan boubou ce a jikinta da take sakakkiyar da sai an saka mata irinta uku ma a ciki ko biyu bata matsesu ba.

“Subhanallah ” ta fada can gasa muryarta da dukka ilahirin jikinta suna rawa,cikin hanzari ta saki hannayenta,wannan ne ya bawa rigar damar komawa ta sake kamar yadda take.
Qafafunta taji kamar suna neman kayar da ita,Allah yasa tana kusa da kujerun da aka aje a wajen domin hutawa,da hanzari ta nema daya ta zauna a kai,duk da yadda zuciyarta ta cika da burin takawa ta fice a gurin,to amma yadda qafafun sukayi sanyi tasan ba zasu bata hadin kai ba.

Waiwayo ya sakeyi karo na uku,saiya tako sosai ya garaso gabanta,iska ta fara debo qamshinsa dake da wani irin scent na musamman tana watsawa tsakiyar hancinta har zuwa kwanyarta. Ya rage tazarar dake tsakaninsu sosai,ya duqa yana dubanta da kyau

“Bari na baki amsarki da farko,ba lafiya bace tasa nake nemanki ba,saboda kalen dangi kin daukarwa mutane yarinya kin riqe kamar ke kika haifeta,ki fiddomin yarinyata,sanann.
..daga naira daya har
zuwa cikar burinki na kudin da kikeson mallaka ki gayamin,zan biyaki ki koma kici gaba da aikatau dinki,badon son raina ba,sal don saboda cika umarnin Dr jarma” maida idanunta tayi ta runtse da kyau,ya zageta iya yadda ransa yakeso,bayan bata aikata masa komai ba,idan ta barshi bata mayar masa ba lallai yaci nasara a kanta,to amma yayi mata wani irin kwarjini a yau wanda bai taba yi mata irinsa ba,sai ta miqe cikin dabara tana dubansa kai tsaye

“Sannu garuna,jinin mansa Musa, you are too proud mr jarma na sake maimaitawa,daga million daya har million dari idan zaka bani bazan koma aiki babazan koma ba nace bazan koma ba ana dole? yarinya kuma ka fini sanin yadda tazo gidan nan,so no need na tsaya maka bayani..
…sannan wannan jikin
da kake magana a kai, inason gaya maka idan ka saba bin matan turawa da sauran yarika na qasashe daban daban inda kake zuwa da sunan kasuwanci….to wannan ilkin da idanunka da baka yiwa shamaki suka sauka a kai,ka gaya musu yafi qarfinka har abada,har gaba da abada din,saidai kallon daga nesa” ta garasa fada tanason hana kanta sakin kukan da yake danqare a zuciyarta. Juyawa tayi zata tafi,saidai kafin tayi wani motsi yasha gabanta.
Zuciyarta ta tsinke da ganin yadda yayi dab da ita,iskar bakinsa da hancinsa dake cakude da wani kalar qamshi tana sauka akan fuskarta kai tsaye saboda qarancin kusancin dake a tsakaninsu,fararen idanun nan nasa sun kada zuwa launin ruwan goro goro

“Dan iska ne ni tatacce wanda yake bin mata daga qabilu da qasashe daban daban,amma kinsan wani abu?…….dukka virgin nake ballewa sabbi dal a leda,bana amfani da second hand ko zawarawa” a hautsine ta daga kanta tana dubansa,juriyarta tana katsewa, qyallin hawaye na ragaita cikin fararen idanunta. Bakinta ya bame bam,ta rasa wacce amsa zata bashi,cikin hakan muryar sajjad da fadeela ta soma dososu hakan kuma bai sanya shi ya matsa ba,sai itace ta zame ta zauna a gurin tana qoqarin boye ruwan hawaventa kada yaga zubarsa.

Tana jin alamun sun iso gurin,bata Ko iya waiwaya wa ta hada ido dasu ba ta mige ta fice a gurin gudu gudu sauri sauri,sajjad ya bita da kallo,sanann ya dawo da dubansa kan toufeeq dake rungume da fadeela cikin kallon tuhuma

“Me kayi mata haka?”

“Let’s go” kawai ya fada yana dauke da fadeela a kafadarsa wadda keta masa surutu. Sai da taga sun shiga mota suna shirin fita a gidan sai kuma ta marairaice

“‘Ina zamu abby?”

“Gida,gidan ba dadi fadeela, hutun ya isa haka ko?” Kai ta gyada a hankali, itama tayi missing nasa,to amma tanason zama da sãahar fiye da komai

“Amma ba tare da anty N zamu tafi ba? naga ko sallama bamuvi ba”

“Zata taho daga baya” ya amsa mata a taqaice,don a yanayin da yake ciki baya bugatar dogon zance. Maganganun data gaya masa sunfi komai tsaya masa a rai,shi zata kalla ta yiwa qazafin neman mata?,shi Muhammad toufeeq?, wanda ko yatsar mace da gangan bai taba rigewa ba,bai taba sanin kowacce mace ba a duniya sai matarsa ta sunnah,ita dinma duk duka lokutane gayyadaddu da zai iya lissafasu. Idanunsa dake masa zugi ya mayar ya kulle yana sauraron radadin kalamanta a tsakiyar zuciyar tasa.

Karon farko a rayuwarta da kalmar
BAZAWARA ta taba gona mata rai,tayi kuka tayi kuka sosai,kukan kuma ya hade mata da wa’adinta da takeci a gidan. Shigowar afifa biyu tana neman inda fadeela ta shiga,amma saahar din tayi banza kamae bata ji ba,tana qudundune a bargo,ta tabbatar idan tayi magana afifa zata fahimci kuka takeyi,wannan ciwon kuma na yau batason rabashi da kowa,a barta ita kadai tayi jinyar kanta da kanta,itadai ta sani a yadda yazo din nan,bazai bar gidan ba sai ya dauki diyarsa.

A shigowa ta uku kuwa taii afifa na fadi yanzu maama ta gaya mata abban fadeelan ya
Aiko a bawa maama haquri ya wuce da afifa zata qarasa hutunta a gida,idan dr ya dawo a gaya masa. Tsaki taja qasan ranta

“Badai shi ba,saidai sajjad,shi zai bada sagon” ta gayawa kanta. Maganganunsa sun mata munin da takejin ba zata iya yafe masa ba,duk da ta gaya masa masu zafin gaske,amma shi va jawo koma meye ta fada,don menene zai aibata mata jikinta? maganar ta zafafeta da yawa,don ko sanda ta miqe don yin sallar magariba sai data tsaya gaban mirror ta sake qarewa kanta kallo,ta kuma sake maimaita yanayin tsaiwar da tayin a dazun da har tasa ya fadi hakan

“Allah ya sakamin” ta fada qasa qasa tana wucewa bandaki.

Kwanakin haka ta dinga kwana tana tashi da zafi da ciwon kalamansa,wadanda ta rubutasu tas suka zauna cikin kwanyarta.
Maama da dr girema sun dauka kawai kewar fadeela ce,afifa ta gama karantar akwai wani abu,saidai har lokacin sãahar din bata fito ta gaya mata me ya hadasu ba,saboda tana in haushin yawan yin wayar data tsiro dashi a kwanakin da wani da batasan waye ba. Bata nutsu ba bare suyi ma magana don haka ta zuba mata ido tana jiran sanda zata nutsu ta fidda komai daga ranta.

********kwanaki uku da dauko fadeela,da safe yana shirin fita ya kaita gurin dr raheema tayi mata checkup,daga can ya biya da ita daya daga cikin guraren wasa na yara wai don ta warware sosal ta koma kamar da,yanason ta manta da sãahar da abinda ya danganceta.

Ta wani bangaren kuma tunanin daya kwana dashi a daren jiya ne har yanxu bai sakeshi ba. Yaya akayi maji tasa yarinyar nan har irin haka,harma take yabonta da kuma shawartarsa ya dawo sa ita? wai wanne irin abune da ita da har take iya mamayar zuciyar kowa daya danganceshi?,mutane masu kima da daraja a rayuwarsa? kamar amfani da tsafi?

“Astagfirullah” ya fada yana gama saka links din hannunsa,dai dai lokacin da akayi masa knocking.

Muryan Joshua ne,amintaccen yaron dake masa shara yake kula da tsaftar lungu da saqo na sassan bedrooms dinsa. Daga bakin qofar ya gaidashi ya sanar masa cewa BOSS ne ya shigo. Ajjiye abinda yakeyi a gaggauce ya buda qofar ya fito yana mamakin zuwan Dr iarma din a daidai wannan lokacin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected