TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
* Shuka a idon makwarwa_☺️☺️
Kira daya maji ta dauka,sai a sannan kuma yaji wani nauyi yana kamashi sanda amintacciyar muryarta Re furta sallama a gareshi, idanunta na tara ruwan hawaye,yau itace Muhammad da kansa ya daga waya ya kirata bisa radin kansa?,wacce irin farar rana ce yau a gareta?.
“Muhammad” ta kirayi full name dinsa cikin karyewar murya,duk wani qunci da take ciki a dan kwanakin saboda abinda mahaifinsa ke shirin aiwatarwa a kanta sai taji yana kwaranyewa
“Kiyi haquri maji,qila na tasheki a barci ko?”
“Bacci Muhammad?, ina daku a wani muhalli da ban aminta da amincinsa ba ina ni ina bacci?,shekara ashirin da wani abu rabona da bacci a irin wannan lokacin, kada ka kashe Muhammad, gayamin dalilin kiran” sosai yaji zuciyarsa tayi wani mugun karyewa,duk yadda yaso ya rige hawayen da suka taso masa abun yaqi yiwuwa,UWA wata halitta ce da kaf duniya babu inda zaka samu rahamar da tayi dai dai da wadda ke cikin zuciyarta akan d’anta,shin sau nawa ya hana idanunsa bacci kamar haka ya yiwa maji din addu’a koda na sati guda ne? ya sani duk salla ya sanya goshinsa a qasa sai ya musu addu’ar
“Rabbirhamhuma kama rabbayani saghira” saidai yasan ko kaso daya cikin dari na wadda ita ke musu baiyi ba
“Ki yafemin majl,am sorry for all the…..” Sargewa
muryarsa tayi,sai kuma maji din ta tari numfashinsa
“Muhammad kai da ‘yaruwarka baku taba yimin laifi ba,kuma ba zaku taba yimin ba,idanma kunyi na yafe muku har wanda zaizo a gaba” furucin da ya sake kashe masa jikinsa kenan,ya cikata da godiya sai kuma ya kasa cewa komai
“Baka neman matarka Muhammad?” Ta tambayeshi kai tsaye,saboda tasan basuyi waya ba, hakanan ta tambayi nadeeya ko ya karbi number a wajenta tace a’ah
“Ya zanyi maji? ji nake kaman ni kadai ne a gidan” Yayi subutar bakin fada,bai kuma farga ba sai da murmushi me sauti ya qwace mata
“Zan tura maka number dinta,ka kira matarka,
Muhammad ka riqe matarka fiye da rigon da zaka yiwa duk wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka” kai yake jinjinawa
“Ka tayani addu’a,wani al’amari ne ke son sake waiwayowa cikin rayuwata ya kuma tunkareni, Allah yayimin zabi mafi alkhairi koda zuciya ta bataso” maji ta fadi a sanyaye. Hankalinsa yaji ya tashi a lokacin farko da ya fara jin haka
“Me yake faruwa maji?” Murmushi tayi
“Ba wani abu bane, karka daga hankalinka, addu’a kawai na bugata daga gareka”
“Amma dai kina lafiya ko? ‚ba wani abu dake damunki?”
Idonta ta rufe hawayen da take tattali suka sauka,lallai babu wani abu tabbatacce sai ikon Allah,yau itace toufeeg din da aka nesanta tsakaninsu ta kowacce fuska ke tattalin farincikinta da tambayarta lafiyarta?
“Lafiya galau nake Muhammad ta kowacce fuska,ka kira matarka, Allah yayi maka albarka” daga haka ta yanke kiran saboda kukan da taji yanason kubce mata. Bata daga cikin mutane marasa yafiya,to amma kuwa anya zata iya yafewa fauziyya?.
Ba jimawa number wayar ta shigo wayarsa
“Germany?” Ya fada a hankali bayan ya gama qarewa
number kallo ya kuma fahimci code din wanne country
ne maqale a jikin phone number din.
“Me sukeyi a Germany? ‚basa tare kenan da maji” ya
gayawa kansa sanda wayar ta soma shiga tana ringing.
Idanunta da sukayi nauyi saboda kuka da bacci
ta daga,a kasalance takai hannunta ta jawo wayartata,batare data duba ba ta daga,saboda jikinta ya bata afifa ceko maama,tafi zaton afifan ma don haka tace
“Bestie” cikin wani irin sanyi sanyin da ya sanyashi jin
saukar muryarta cikin kowanne sashe na jikinsa,ya
lumshe idonsa sannan ya sakar mata sallama cikin taushi.
Tashin farko ta nemi baccin da yake idanunta ta
rasa, saita maida jikinta ta jingina da jikin gadon dake
kusa da ita tana amsa sallamar zuciyarta na wani irin
harbawa
“Matata nake nema,tana kusa?” Ya fada a nutse. Rasa amsar bashi tayi don haka tace
“Bata nan” garamin murmushi ya saki
“Matar toufeeq fa?” Salon yadda yayi maganar ya sake daburtata tare da kashe mata jiki gaba daya
“‘Idan sago ne ka bayar sai a bata” jikinsa ya amsa gaba daya,sai ya gyara zamansa tsakiyar gadon sosai yana sakin mata murmushin da sautinsa ya sauka har kanta,ya kuma tayar mata da kowacce tsiga ta jikinta
“Sago ne me nauyi,wanda babu kunne da zai iya dauka,hakanan babu harshen da zai iya isar dashi,saboda kebataccen sirri ne da ya shafi mijin da kuma jarumar matarsa…..Please tell her, her taste,scent and feel of her skin next to mine…..its all i want every single night,but ta barni cikin kewa da matsanancin so, ki gaya mata am falling and falling and falling for her entirety,ki sake gaya mata i want to feel her skin and i want breath her in i want her in the worst way,| want kisses every corner of her body to express all love which ¡ have in my heart,a million feelings all for one person” gam ta rintse idanunta, tana jin wani abu me nauyi yana saka saman zuciyarta,wani irin yanayi da bata taba tsintar kanta a cikinsa ba,wani irin saqo da ya isa kowanne sashe na gangar jikinta dama zuciyarta,wasu kalamai masu matugar nauyi da zafi da bata taba sauraren kamarsu wajen zaqi da qawata zukata ba. Duk da kasnacewar adam a baya gwani wajen iya tsara kalamai, amma a yanzun sai takejin wadan nan kalaman da kuma kalaman adam,tamkar an dauko ginin gargajiya na ainihi an sakashi tsakiyar fadar white house ta amurka
“SAHR” ta tsinci kalmomin sunanta a bakinsa da wani irin amo me narkar da zuciya kamar yadda ya saba kiranta
“Am too late to be your first. But right now am preparing my self to be your last” kasa jurewa daukan nauyin kalamansa tayi,tsarin yadda yake furta kalaman kadai sun banbanta da muryarsa da yake magana da ita ko da yaushe,wani irin shauqi da soyayya me tsananin tasiri ta sanya ya rasa kowanne kuzari a jikinsa,yana jiran yaji koda kalma daya daga bakinta, amma maimakon hakan sai katse kiran yaju tayi. Zare wayar yayi a kunnensa yana dan sakin qaramin murmushi, kafin ta katse wayar ya iya tsinkayar yadda taja numfashi da sauri cikin sheshsheqa. Wayar ya sulale ya ajjiye a gefansa,ya miqe yana sake jin wani irin shauqi tare da tsananin tausayinta yana fusgarsa. Diary din ya rungume a qirjinsa yana jin tamkar ita ya runguma,ya zura slippers dinsa ya sauka a gadon a hankali ya fice daga dakin.
A nutse ya murda qofar dakin nata, idanunsa da hancinsa suna sake tabbatarwa lallai nan din muhallinta ne, ko ina a tsaftace a kuma gyare da sassanyan qamshinta me wani irin sanyin da bai taba jin irinsa ba.
Kai tsaye ya wuce gadonta,ya haye abinda tare da jan duvet dinta ya kawoshi saman fuskarsa,yakuma dauki pillow dinta guda daya ya rungumeshi saman fuskarsa yana sansanar sassanyan qamshin hair mist dinta. Har cikin kwanyarsa ya zuqi qamshin da kyau sannan ya saki pillow din ya dawo qirjinsa. Sake bude dairy din yayi duk da ya gama karanceshi, idanunsa suka sauka saman page na goma layi na farko
“FAKE MEDICATION” ya karanta zuciyarsa na harbawa,yanayin fuskarsa ya canza ya rufe littafin a hankali tunaninsa yana komawa baya
“Ko shine dalilin da yasa taqi yarda da kulawar kowa akan fadeela? ko wannan ne dalilin da yasa ta dauki nauyin siya mata magani tare da bata maganin da kanta ba tare data bugaci kowa ya kusanceta ba?. Meye ya sanyata wannan tunanin? ,wannan matakan tsaron masu garfi haka