TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Muje yaya” ganin ya tsaya bai shiga ba bai fita ba.
“Sannu da zuwa” maji ta furta a sanyaye, baice mata komai ba sai hannu da ya miqa mata
“Bani key din motata” idanu suka hada da fauziyya,saita saki murmushi,batace komai ba ta miqe tsam,ta shiga dakinta ta fito dashi ta miqa masa. Juyawa yayi ya miqawa fauziyya
“Ki riqe a hannunki ki dinga hawa,duk lokacin da ni nake da buqata na dinga amsa daga hannun naki,jeki” sanyaya gwiwar fauziyya din tayi, ba haka taso ba,so tayi yayi mata irin cin mutuncin da ya saba yi mata a gabanta,ya wulaqantata ya fifita darajarta akan tata. Juya key din tayi a hannunta sannan ta juya ta fice shi kuma yazo zai wuce cikin dakin nasa ba tare da ya sake bi takan maji ba.
Kasa motsawa tayi tana zaune a gurin har ya gama abinda zaiyi ya fito,ya buqaci abinci ta zuba masa,yayi kiran shalelen tasa tazo suci abinci yadda suka saba tace ai ta fita dana mota. Maji na zaune tana nazarin rayuwa,me gobensu zata haifar ita da mahmud da irin wannan makauniyar rayuwar dake wakana a tsakaninsu. A daren bayan sun gama shirin kwanciya ta sameshi cikin kwantar da kai take tambayarsa abinda vake damunsa tare da shawarar yayi gogari ya daidata gidansa
“‘Ni ba abinda yake damuna, hankalina yana tashi idan fauziyya bata cikin walwala, raina yan baci idan nata ran ya baci saboda ba abinda nake tunawa sai amanarta da mahaifiyata ta barmin” yadda yake maganar kadai ya sake tabbatarwa da maji lallai abub yayi girma ya wuce duk inda ake zato,daga wannan lokacin ta sanya idanu kan fauziyya fiye da baya,babu jimawa kuma ta fahimci irin aikin asirin da takeyi akan yayan nata kuma miji ga maji din.
Randa ta karanci hakan ta samu fauziyyan na zuba wasu abubuwa cikin abincin Mahmud din maji tayi ram da hannunta tana kallonta
“Kin ganowa kanki ranar barinki gidan nan sakarmin hannuna” ta fada kanta tsaye bacin rai ya hana maji magana, wacce iriyar baqar masifa ce haka?,duka duka shekarunsu dava da fauziyya har yanzu babu wanda ya rufa shekara arba’in, gaba daya ba zasu wuce talatin da bivar ba amma ta zama wata bagar masifa?.
“Kinyi asara wallahi,sannan bana danasanin barina gidan nan saboda nayi imani duk sanda hakan ta faru cikin qaddarata yake,ke baki isa ki zanamin gaddarata ba”.
Tun daga wannan ranar fauziyyan ta dauki damara,saboda ta sani maji din nada wani irin kariva da take hana asiri cimmata nan da nan, kuma tasan hakan baya rasa nasaba da yawan addu’a da azumin nafila da bata rabo dashi.
* MAMAYA *
Tun daga wancan lokacin da ta kama fauziyyan take kaf kaf da abincinsu su duka cikin gidan, don tayi imani ba abinda fauziyyan ba zata iya aikatawa ba.
Ranar da ta zama baqar rana a gareta, ranar data shiga tarihin rayuwarta,ranar da ba zata taba mancewa da ita ba,ranar kuma data zama mafarin zanen dukkan qaddarorin da suka wanzu a rayuwarta dana iyalinta.
A wani yammaci liqis wanda kadan ya rage magariba ta kunno kai,ta gama abincin dare cikin galabaita saboda yadda qamshin girkin yake damunta yana hautsina mata kayan ciki, yanayi ne dakan faru da ita a duk lokacin da take da qaramin ciki,ko a yanxun tana tsammanin cikinne saidai haka kawai ta kasa gwadawa bare ta tabbatar, saboda yanayin da take ciki wanda zaiyi wuya ta samu nutsuwa ta kwana uku cikin gidan fauziyya bata sakata a masifa ba,abinda yake dakushe kaifin abun wanda a yanzu sukanyi sati daya har zuwa biyu lafiya lafiya shine addu’ar data tashi tsaye tana yi, ba dare ba rana. Tana kammala abincin ta fita a kitchen din tana fatan samun wata iskar da babu qamshin abincin a ciki kota samu ta dawo dai dai,ta kama hannun nadeeya ta saka toufeeq a gaba suka wuce, zuciyarta na tuna mata da kalaman da fauziyya ta gaya mata kwanaki uku da suka wuce,wadanda suka sanya maji din dauketa da mari, abinda bata taba yi mata ba kenan.
“Badai yara ba? sai na rabaki dasu rabuwa ta har abada,saina tabbatar miki da cewa ni fauziyya ni kika haifawa su”. Ta jira abinda zai biyo baya akan marin da tayi mata amma har yanzu bataga alaman Mahmud ma yasan da abun ba,hakan bawai ya bata kwanciyar hankali bane, a’ah, ta sani tabbas akwai abinda zai biyo baya.
“Abba ya dawo maji,muna masa sannu da zuwa bai amsa ba” toufeeq ya fadi mata,saita kalleshi da mamaki,don bataji shigowarta ba bai kuma nemeta ba,qilan yau an birkitashi ne kamar yadda ake masa duk sanda akaga dama. Batabi takan zancan toufeeq ba,sai ta zauna tana jira ta koma dai dai sannan ta iskeshi.
Motsin da ta danji a kitchen ya sanyata yunqurawa babu shiri saboda tunawa da tayi ta baro abincinsu ta cewa da toufeeq “Ina zuwa ku zauna”. Tun kafin ta garasa ta hangi fauziyya a ciki gabanta ya fadi ta kirayi sunan Allah tana qarasawa da gaggawa. Shigarta yayi dai dai da ware wani abu baqi cikin kwalba da fauziyya tayi tana shirin antayawa a cooler din abincin Mahmud. Caraf tayi da hannun fauziyya tana kallonta
“Me kike shirin aikatawa maqiyar Allah da manzansa” maimakon ta amsa mata yadda suka saba sai kawai taga ta saki kwalbar,maji tadan ja baya tana duban kwalbar data fadi qasa ta fashe,wani irin wari wari yana fita daga ciki, shi ba warin fiya fiya ba shi ba na maganin bera ba, kafin ta gama wannan nazarin fauziyyan ta zame hannunta ta kama hannun majin ta rige tsam kamar me shirin hanata tabawa,sai kuma taji ta kwazara ihu tana kiran sunansa
“Yaaya!, innalillahi wa inna ilaihi raji’un yaaya kazo ka gani* tunanin maji ne ya juye, ta kasa fahimtar abinda fauziyyan ke shirin alkatawa. Cikin qasa da second talatin ya iso qofar kitchen din, hannunsa riqe da wasu takardu,wani irin lafiyayyen fushi na kwance kan fuskarsa
“Yaaya,kaga abinda na kamata tana shirin zuba maka,yaaya dama kasheka takeson yi,bata qaunarka” fauziyya dake wani irin rawar jiki ta fada hawaye na wanke mata fuska.
Wani tashin hankali ne va bayvana baro baro saman fuskarsa ya zubawa maji ido, majin da lokaci guda tunaninta ya juye, tsananin kidima da rudewa da jin yadda fauziyya ta juyar da abin kanta lokaci guda ya gigitata
“Shifa?,kece shifa da kanki?, bazan musa zancan fauziyya ba,saboda gashi na gani da idanuna” sai ya watsa mata takardun hannunsa saman fuskarta
“Sati uku cur na fuskanci ana dauke takardun kadarorina,sama da qasa na dinga nemansu daya bayan daya ina rasawa,sai gasu guda shidan cif a dakinki, ashe kin shirya kasheni ne ki mallaki abinda na tara ko?” Wani irin kukan baginciki ne ya balle mata
“Wallahi wallahi bani na daukar maka ba bansan dasu ba” ta fada tana jin ranta yana daci,sharrin kisa da sata duka lokaci guda?.
“Idan bake bace nine kenan nakaisu dakin
naki?,bayanke ki gayamin wanda yake shiga dakina”
“Babu” ta amsa masa kai tsaye,saboda tasan babu din shine amsar
“Gwara da baki wahalar da shari’a ba,kije na sawwaqe miki na gaji da yadda gidana yaqi zama lafiya sanadiyyarki,na sakeki saki daya”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, allahumma aiirni fi musibati, wa’akhlifni khairan minha” ta furta da madaukakin sauti dake gauraye da sautin kuka, idanunta suna sauka akan fuskokin nadeeya da toufeeq wadanda suke tsaye daga bakin qofa suna kallonta, daga shi har nadeeya din idanunsu cike yake da hawaye,sai taga uban yaja hannuwansu ya fice dasu ya barsu daga ita sai fauziyya.