TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
*_Washegari*
Tun da safen taji cikinta yayi wayam kamar bata taba sanya masa abinci ba,sai data leqo taji bataji motsinsa ba,don tun sallar asuba da ya fita ta maida key ta rufe,ta bude ta lallaba ta shige kitchen din.
A gurguje ta dafa tea,ta soya qwai tayi toasting bread guda uku. Daga gaban kitchen cabinet din ta tsaya tana ci a gurguje,so take ta gama ta koma daki kafin ya risketa.
Tana tsaka da ci tattausan gamshinsa yayi mata sallama,bata waiwaya ba don ta saddaqar shine, ta cusa bread din a bakinta tayi tsaye kawai tana jin takunsa. A nutse ya kamo qugunta ya manna da jikinsa,ya dora kansa a kafadarta ya sanya hannunsa ya jiyo da fuskarta ya zamana suna facing juna.
Miskilin murmushin nan nasa dake da wuyar gani ya
saki
“Halan marowaciya ce ke ko?” Ya furta yana lullumshe mata ido, kamar wanda ke jin bacci. Bai jira tace komai ba ya kai bakinsa a nutse saman nata bakin. Bread din ya gutsira a tausashe, numfashinsa ya gauraye da nata,ya janye idanun a nutse yana tauna bread din, sai ya kama hannunta dake riqe da cup na tea din yakai bakinsa ya kurba a hankali. Kai ya jinjina,komai ta dafa yana da wani irin taste na daban da baya jinsa a ko ina. Ko daya hadiye dake gutsire sauran na bakinta yayi,sannu sannu sai gashi ya cinye mata bread din tas da tea din,ya saketa a nutse yana murmushi
“Thanks for this beautiful breakfast,i love you” yayi maganar yana tafiya da baya da baya idanunsa a kanta kamar bazai janye ba. Har yakai qofa sannan ya juya da hanzari ya qarasa ficewa yana jin shauqi na ratsashi.
A gurguje ta juya itama tana wucewa daki, ko ina cikin kanta na maimaita amsa kuwwar muryarsa cikin taushin nan nata da kalmarsa ta qarshe ta
“| LOVE YOU”
“He loves me?” Ta tambayi kanta tana tsaiwa gaban madubi tana duban fuskarta. Ta yaya zai fada sonta indai har da gaske ne? bayan dab take da kammala aikinta ta koma inda tafi wayo?, qwaqwalwarta ta daure tsam, daidai lokacin da kira ya shigo wayarta. Da sauri ta dauka tana komawa gefen gado, maji ce,kamar tasan kuwa a yau take shawarar kiranta,ta tabbatar itace hanya mafi sauqi da zata bi tayi tafiyarta a sirrance cikin kwanciyar hankali. Cikin kunya da nauyi ta daga kiran.
Kamilar muryar maji din ta ziyarci kunnenta da kyakkyawar sallama
“Ibnaty…..kaif einty”
“Barka da warhaka maji” sãahar din ta fada tana murmushi cikin kunya matuqa,kunyar da sai a yanzu takejinta ta gasken,irin kunyar dake wanzuwa tsakanin suruka da surukarta
“Barka kadai d’iyata,munyi waya da nadeeya tace kina sashenki,ina fatan komai lafiya,kuma komai yana tafiya cikin kiyayewar ubangiji ba tare da matsala ba?”
“Komai lafiya alhamdulillah”
“Nima ina gab da dawowa,wata matsala ce takeson faruwa fil usbu’il maadi(cikin satin da ya wuce) wala kin in sha Allah sa’arji’u ilaikum fi hazash shahr(saidai in sha
Allah zan dawo gareku cikin wannan watan)”
“Allah ya amince maji munyi kewarki, nahnu mushtaquna ilaiki(munyi kewarki)” murmushi ta saki cike da jin dadi
“Wa’ana aidan yabnaty (nima haka d’iyata)”
“Maji” ta kirata a sanyaye
“Na’am diyata,me yake faruwa?” Ta fada kai tsaye saboda yanayin kiran da taji tayi mata
“Akwai maganar da nakeso mui,nayi wani danyan hukunci ba tare da neman shawararki ba”
“Karkiji komai diyata,nayi imanin ba zaki taba cutar da kowa nawa ba,saboda addu’ata a kanki take,kuma Allah ya zabar mana ke,na tabbatar in sha Allah ke da duk abinda zakizo mana dashi alkhairi ne,gayamin kanki tsaye, menene?”
[29/09, 11:47 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 40
“Na shirya tafiya da fadeela don yi mata aiki ta rabu da lalurar da take fama da ita a sirrance ba tare da ko mahaifinta va sani ba bare mutanen da muke rayuwa
tare dasu ba”
“Allahu akhbar ” maji ta maimaita har sau uku
“Kamar tare dake muke wanann tunanin? wannan shine abinda na shirya aiwatarwa na farko bayan na dawo Nigeria,na baki goyon baya alf bil alf(dari bisa dari)”
“Amma maji, banason kowa ya sani saboda ina tsoron kada a sanya abun yaqi yiwuwa” kamilin murmushi maji ta saki
“Fauziyya hajiya qarama,ko ba ita kike tsoron kada ta sanya moha ya hana ba?,ina da labarin yadda tayi ruwa tayi tsaki ta hana duk wata maganar da za’a tayar akan a yiwa fadeela aiki,na bar zancen ne akan cewa ni daya zan iya aiwatar da aikin, koda ita din bataso,saboda nasan duk inda takai ga girman kaidinta,bata isa ta sanya moha ya hanani ba.……..har yanzu bakisan me fauziyya ta yiwa rayuwata ba,zauna da kyau diyata yau na gaya miki labarin da masu shekaru irin naki dake rayuwa tare dani basu sani ba” a sanyaye sãahar ta gyara zamanta saman gadon sosai, tun kafin taji komai daga bakin maji jikinta ya sanyaya,ba abinda take haskowa sai fuskar hajiya qarama a sannan.
* TUNA BAYA 1988 *
Mummunar faduwa gabanta yayi,wani irin hargitsatsen kallo daya watsa mata shi ya sanyata cikin rudani, batasan me tayi masa banda kulle qofa da tafiya da key din,kallon daya watsa mata yafi qarfin wannan laifin, kallo ne na zallar qasqanci da kuma tsana,tasan dai ranar yau lafiya galau suka rabu,ya fita cike da murna zai karbo upper dinsa aiki ya samu,suna ta murna dukkansu tare da saka ran fita daga tsanani zuwa sauqi, sai dukka gwiwarta tayi sanyi da irin nau’in kallon da yake jefa mata.
Kafin ta qaraso ainihin tsakar gidan sai wulgawar fauziyya ta gani, wadda kanta ke daure da bandeji da yayi tsatstsafar jini gaba daya daga samansa,ta nufeshi a gigice ta cukuikuyeshi tana neman mafaka a bayansa,bakinta na wani irin rawa na zallar toro da firgici take cewa
“Na shiga uku akh, gata nan ta dawo,don Allah ka boyeni,kada ka bari ta qaraso,wallahi zata qarasa illatani kamar yadda taci alwashi” tayi maganar tana wani irin haki da tawar jiki, kamar wadda tayi gudun kwana da wuni.
Baki kawai ta saki galala tana kallon fauziyya,qwaqwalwarta gaba daya ta rikice,me take nufi ne? saita maida dubanta ga bandejin kanta tana mamakin me ya sameta daga fitarta
“Bata isa tayi miki komai ba,a yau qarshen al ‘amarinta yazo, muguntarta a kanki kuma ta qare!” Muryarsa mai zurfi dake fita da amon fushi ta fusgi hankalinta, saita maida dubanta kansu gaba daya, kwanyarta na sake rikicewa da salon maganganunsu da ba ganewa takeyi ba.
Ci gaba tayi da kallonsa, saidai ya zaro biron dake.
gaban aljihunsa ya kuma dauko takarda a daya aljihun nasa,ya bude kan biron cikin fusata. Cikin mamaki me yawa taga fauziyya ta kama biron ta riqe gam
“Me zakayi yaaya, ka rufamin asiri don Allah, kada kace zaka saketa saboda ni” ta fada hawaye na wanke mata fuska. “Ki saki fauziyya,duk mutumin da bayason jininka kaima baya qaunarka,ban ga amfanin zama da ita ba, baya ga tarin dimbin gori da maganganun data fada a kanmu” kuka sosai fauziyya keyi,ta kuma riqe abun rubutun taqi sakar masa tana bashi haquri, abinda yayi masifar daure tunanin SHIFA, me yasa fauziyyan dake burin afkuwar haka ita ke bada haqurin kada a saketa?.
“Kinci darajarta,ki dubi abun kunya wanda kike quntatawa shine yayi silar kubutar dake daga afkuwar wani mummunan abu a kanki” mamaki ya sake kasheta,kanta ya daure tamau, tama kasa cewa komai baki sake take kallonsa har ya miqe ya nufi hanyar soron gidan,har yanzu zallar bacin ran dake saman fuskarsa bata gushe ba. Har yakai bakin qofar sai kuma ya dawo,ya tsaya gaban fauziyya dake zube tana kuka