TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
llahirin jikinta lullube yake da wata irin
suttura da aka yiwa dinki na mussamman da lafiyayyen yadin silki me tsananin tsada da daukar hankali,sannan akabi adon doguwar rigar silk din da wata rigar me zubin alkyabba ta baqin yadin velvet me adon zaren da aka tsomashi cikin ruwan gold. Tun daga nesan nesa da ita hancinka yana iya jiye maka kwantaccen qamshi me tafiya da tunani da takeyi,ba abinda ke fita daga jikinta sai wani irin haske da walwali ke kashe idanu. Babu abinda ake iya gani a jikinta,sakamakon yanayin shigartata daya rufe ko ina nata ruf,rufewar data bata damar yin kuka me yawan gaske ta qasan hular rigar da aka
Tullubeta da ita. Ba abinda ke mata yawo a tsakiyar kanta sai nasihar Dr girema,maama yaa muhyi yaa Saifullahi da yaa zaid,da kuma shaqigan ‘yan uwa sannan masoya irinsu anty farheen anty samreen.
Can cikin jikinta take jin wani yanayi me kashe zuciya, maganganun da sukayi mata sun shiga jikinta sun kashe duk wani karsashi da rashin damuwa da auren,sun dora mata nauyi me yawa, kalaman da suka furta a gareta,banda tana da aminci da afifa zata ce tabbas ta gaya musu manufarta a auren.
Ido ta lumshe tana jin wata
matsananciyar fargaba lokacin dajerin gwanon lafiyayyun motocin dasuka daukota suka fara cusa kai cikin gidan,a baya qaddara ta sanya ta shigo gidan a sunan nanny,a yanzu a karo na biyu qaddarar ta sake dawo da ita d sunan matar aure kuma matar me gidan,abinda ko kadan bata taba tunanin faruwarsa ba.
Wani irin yanayi taji yana bin sassan jikinta lokacin da hannunta ya game da na hajiya qarama da ta karbeta daga hannun yakura yayar Dr girema,zuciyarta ta motsu lokaci guda. Haka kawai takeiin matar kwata kwata bata kwanta mata ba ko kadan. Saidai har suka doshi sassan da ita kanta sãahar batasan wanne bane saboda kanta na lullube tana iya tsintar muryarta fes tana sake marabtar danginta
“Maji tace a wuce da ita sashenta ta huta,ita
‘yar gida ce a gurinta basai an bata wahala ba,kuma ko yaushe zasu kasance tare” sagon da baaba ramatu ta matso ta shaidawa hajiya garama kenan qasa qasa. Kai ta jinjina,a gasan ranta zuciyarta tana bata tabbas akwai dalilin da yasa shifa ta aikata hakan,amma koma meye har yanzu sauran akaloli suna hannunta,kuma ita zata ci daga da yin nasar kamar yadda tayi a baya.
Tunda ta tsoma gafarta a sashen jikinta da hancinta ta TABBATAR mata wani guri ne daya banbanta da kowanne sashe na gidan,guri ne me tsari da koda idanunta suna a lullube amma hakan bai hanata ganin lallausan carfet dan gasar turkey da qafafunta ke nutsewa a ciki ba. Qamshin da wajen ke fiddawa kawai ya isa ya saukarwa da zuciya tare da ruhi salaama,uwa uba dukka hayaniyar gidan sam sam babu ita a nan,bisa alama ma sun baro mutanen dake dauke da hayaniyar a can baya,sai wani irin shuru da sautin muryoyin da basu wuce biyar zuwa shida ba dake magana da sauti mara hayaniya.
Bata gushe ba tana biye da hajiya qarama dake ci gaba da cusa Kai zuwa hallway din da dakunan baccin sashen suke a jere,wanda aka sake narka kudi aka masa mugun gyara na fitar hayyaci,duk kuwa sa cewa babu abinda ya sameshi, amma a yanzun an masa gyaran da zai dace da rayuwar maaurata.
Zuciyarta dake qirjinta takejin kamar ana hurawa wuta saboda ruwan kudin da taga toufeeq din ya barnatarwa gurin,bayan ta samu dukkan bayanai da huijoji masu qarfi daje bayyana mata cewa ba auren soyayya yayi ba,auren sadaukarwa ne ga diyarsa fadeela,a qalla tafi shekara goma batasha maganin hawan jininta ba,amma a yau batajin zata iya kwana ba tare da tasha din ba.
Wasi wasi yaso cika zuciyarta taf,tunda suke mata aiki tsahon shekarun basu taba kawo mata labarin da ba haka yake ba,amma a yau ta shiga tantama,yadda taga komai ya canza,tayi imanin muddin babu son ron taoufeeq bata zaton akwai wanda ya isa ya sakashi yiwa bangaren irin wanna tsarin da kowa zaiyi burin kasancewarsa a ciki.
Bata fahimci cewa babu kowa a tare da ita ba sai bayan shudewar mintuna goma da sumaira ta shigo tana gaya mata yaa Saifullahi ya bada dokar kada wanda ya zauna. Hannun sumaira ta riqe da kyau,qwalla na sauko mata.
A irin wannan gigitaccen yanayin da take ciki inama acw afifanta tana kusa da ita? itace qwarin gwiwarta,saidai kuma inaaa,zagin soyayya ya sanya dukkan wani qarfi nasa ya nesantata da afifan,tana can itama domin fuskantar sabuwar rayuwa, rayuwar da säahar ke mata fatan ta zama me tsananin zaqi,ba me daci ba kamar yadda ta fuskanci tata.
Bude gofar da taji alamun anyi a
karo na biyu ya sanyata kasa kunne. A nutse take takowa zuwa cikin dakin, idanunta akan rufaffiyar fuskar sãahar,zuciya nata yi mata saqe saqen abubuwan da zata iya aiwatarwa a kanta,saidai duk abinda zuciyar ke gaya mata tana ganin bai dace da ya faru a wannan muhallin ba,a kuma dai dai wannan lokacin ba.
[14/09, 7:44 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI *
Book 02 Page 7
Har afifa ta gama wayar idanun saahar yana kan wayarta tana chart,ido tadan zuba mata zarginta yana sake tabbata,yadda sãahar me shakulaton bangaro tare da nuna halin ko inkula da dukka abinda ya shafi bikin ya sake tabbatar mata da zarginta,uwa uba ko sau daya ita dai idanunta basu taba nuna mata kiran toufeeq jarma ba
“Kina jina muna magana amma bakice
komai ba?” Dan duban afifan tayi,sai ta saki
murmushi
“To me kikeso nace?,salon nayi rash-in
kunya?,kuma ma ai kin gama komai,duk
abinda nake bugata ko zance ke kin isar
min,duk abinda ya samu ayi,wanda bai zama
lallai ba ko bai samu ba sai a haqura ko?” Kai
afifa ke girgizawa tana kallonta
“Amma dai ba haka kikayi ba a aurenki da
adamu” ajiye wayar tayi gefe wani murmushi
dake cakude da zallar nishadin da takeji
gasan ranta ya kubce mata ta zuro gafafunta
gasa cikin zummar shiga bandaki sannan ta
amsawa afifa
“Banda abinki hajiya afifatu,ai kullum dan
adam dada wayo da hankali yakeyi ko?,don
zanyi aure bawai ba hakan yana nufin na
mance da asalin su waye maza ba,ko kuma na manta radadi da daci da suka dasawa rayuwata ba”
“‘Anzo gurin” afifa ta fada tana zagayowa gabanta da sauri,ta jawo stool ta zauna akai tana fuskantar sãahar wadda ke mata duban mamaki
“Bestie bandaki zan shiga,yaa haka?”
“Inason nasan gaskiya ne bestie,yau ashe anzo wata gaba da zaki dinga boyemin wani abu a rayuwarki? meye ainihin gaskiyar magana akan aurenki da toufeeq jarma,duk yadda naso na basar nayi kaman ba komai na kasa bestie,ki gayamin gaskiya” murmushi tayi hankali kwance
“Ki barni naje nayi fitsarin mana”
“Na barki” ta fada tana dubanta. A nutse ta miqe ta wuce bandakin,ba jimawa ta dawo ta koma inda ta tashi ta zauna. Komai ta warware mata,abun sai ya sanya afifa murmushi me kama da dariya
“Allah ya sanya alkhairi,abu kuma yay kyau,hakanan hankalina ya kwanta da bayananki,amma ke dashi dukka ku shirya ranar karbar sakamako a tsakaninku”
“Sakamakon me?,kefa wani lokacin kin fiya jaye jaye”
“Lokaci zai bayyana komai”. Tasan halin afifan da iya saqa zance,sai kawai tabar zancanta,ta maida qafafunta saman gadon tayi kwanciyarta cikin nutsuwar data jima bata jita cikin ruhinta ba. Yayin da afifa ke duba kiran da ya shigo mata,sajjad ne,migewa tayi ta dauki scarf dinta ta fice a dakin, sãahar data fuskanci meke faruwa ta bita d kallo tana tabe baki