TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Bari to na taimakeki na rage miki wasu amsoshin tambayoyin…..nasan kin shiga kogin tunanin meye dalili na na hana yaaya ya sakeki ko? ‚nayi hakanne saboda banason tafiyarki yanzu,nafison saikin gasu yadda ya kamata, idanunki kuma sun gane miki girman matsayina a wajensa da kuma qarfin izzata,ta yadda zaki rayu kina bada labari a duk inda kika zauna”
[02/10, 2:56 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 42
“Nifa bakiyimin komai ba kibar ma maganar don Allah, banason bacin ran fauziyya gaskiya,a kan ranta ya baci komai ma zan iya aikatawa,yar uwata ce bani da kamarta,farincikinta shine nawa, zama lafiya da ita shine zama lafiya da ni” shuru tayi tana juya maganar a ranta,tabbas akwai qamshin gaskiya akan abinda zuciyarta keta raya mata. Tun faruwar wannan mu’ amalar tsakaninta dashi sai aka dan samu sassauci kadan,ya daina fushin da ya dauka gadan gadan da ita,yaci gaba da bata kufin cefane shima, amma kuma har yanzu abubuwa da yawa bata canza zani ba, fauziyya taci gaba da juya akalar gidan tamkar yadda mahaifiya ke juya akalar gidan danta. Hatta da abinci a yanzun suna cin duk abinda fauziyya ta zabi a girka ne. A haka aka yiwa mahmud albashin farko,sun kuma hada masa da wani kudi da suke bawa sabon ma’aikacinsu,don haka a sannan ya shirya tashinsu daga gidan, zuwa babban gidan da Kamfani ya bashi.
Batasan hawa ba batasan sauka ba,sai siyayya da taga suna ta fita ita dashi. Ko sau daya bata nuna tasan abinda yake gudana ba,idan ma fauziyyan tayi ne saboda ta quntata mata ko ta bata haushi, saidai qasan ranta bacin rai ne danqar irin wanda fauziyya ke burin ganin ta cusa mata,ko a fuska a lokacin wani irin ramewa majin tayi,saboda dukka wani kwanciyar hankali da • nutsuwar gidan miji ta rasata, dukkan hankalin mahmud ya karkata ga buqatunta da faranta mata,kai idan kaga yadda abun yake zaka dauka kishiya ce fauziyya a wajenta,kishiyar ma irin wadda tayi dukkan me yiwuwa wajen raba tsakanin miji da abokiyar zamanta.
Da wani dare mahmud ya aika toufeeq ya kirayi shifa din, a lokacin tana zaune saman abun sallah,don yanzu babu abinda yake bata nutsuwar ruhi da sanyin zuciya sai sallah da azkar. Ta iso ta riskesu a falo sunata sabgoginsu,fauziyyan ta wani murje a lokacin saboda tarin supplement da take dirkawa kanta na qarin qiba da kuma qara haske,wanda har sun wuce qa’ida,hips da boobs dukka sun fito sosai.
Guri ta samu ta zauna a nutse tace
“Gani” dubanta mahmud yayi,a idanunsa yaga ramewa da kuma canzawar da tayi, qasan zuciyarsa yana jin wani iri babu dadi, saidai baki ya gaza furta komai, hakanan wani abu yana tasowa yana danne dan qaramin tausayin da yakejin yana masa tasiri.
“Nidai bansan me yake damunki ba, gaba daya kin tsangwami kanki?,lokacin da ya kamata ki tsaya mu fuskanci rayuwa, Allah amshi addu’ar da kiketa yi mana” wani kallo tayi masa sai ta kauda kanta,batason tace komai saboda bata son fauziyya ko kadan taga alamun karaya a tattare da ita,ta tabbatar abinda taketa son gani kenan,saboda yadda ta matsa qaimi kawai ya isa bayar da amsa ga maji
“Nan da kwanaki uku zamu koma sabon gida,a baya na miki alqawarin sabbin kayan furniture da komai da komai,to yanzu yanayi ya sanya ba zasu samu ba,saboda nauyi da ya gara yimin yawa,an siya bawai ba’a siya ba, amma kayan furniture za’a sakawa fauziyya tunda itace garama, kuma ba mai zama bace, idan ta samu miji aurar da ita zanyi,kayan kitchen kuma na ajjiye mata su kada auren ya taso bani da komai a lokacin, idan Allah ya hore miki nan gaba sai a canza miki wasu,zan saka azo a kwashe wadan nan ayi musu gyara” qas tayi da kanta,har cikin zuciyarta takejin wani irin bacin rai,bawai na furniture din da yace za’a yiwa kwaskwarima ba,a’ah……na yadda kullum kwanan duniya yake qara qasqantar da martabarta a idanun fauziyya yake kuma sake wulagantata. Ta tabbatar idanun fauziyya a kanta suke taga action dinta,don haka ta daga fuskarta da murmushi
“Banda abinka ai basai ka tsaya yimin bayani ba, Allah ya hore ya bada yadda za’a yi‚ba komai” har ransa yaji dadi duk da cikin jikinsa yakejin bai kyauta ba, sai ya jawo wata leda
“Gashi ganwarki tace ki fara dauka”
“A’ah ta dauka ba wani abu;idan ta gama zaba moha ya kawomin” ta fada tana miqewa
“Laaa maji ai ba wani abun bane,komai iri daya aka siyo, bambancin kala ne kawai” fauziyya ta fadi,wadda bata son maiin ta wuce ba tare data sake ganin wannan ba. Sabbin atamfofi ya siya musu masu tsada da zasu dinka na tarewa a sabon gida,waiwayawa maji tayi ta kalleta
“Bani da zabin kala fauziyya,ko kin manta likkafani da kala qwaya daya yazo?, kuma shine tufafinki kuma tufafina na qarshe?” Turus tayi tana bin maji da kallo,tasan cewa magana ce ta gaya mata a fakaice,sai bata sake cewa komai ba har ta wuce zuwa dakinta.
Saman abun sallarta ta koma ta zauna tana nazarin abun zuciyarta na soyewa,ta gaji da zubda hawayenta,zuwa yanzu zuciyarta ta fara soyewa,sai taci gaba da ambaton sunan Allah sannu a hankali har ta samu sassauci.
Cikin wannan yanayin suka koma sabon
gidan,wanda duk yaga dakin fauziyyan zai dauka shine dakin maji,ya zuba mata komai sabo,hakanan kayan yara ma suna gurinta da komai nasu
“‘Itace uwarsu ai ita zata kula dasu” abinda Mahmud ya fada kenan. Maji ta jishi kawai, amma ta barwa ranta koda zata sallamawa fauziyya komai banda yaranta da ita daya ta raini cikinsu ta kuma haife abinta. Tsayayyar macace da ita kanta fauziyyan tasan cewa nasararta dukka akan yayanta take,amma majin ta shallake hankalinta,duk yadda taso a maida mata maji kamar mahmud don taci duniyarta da tsinke ta gaza samun hakan. Hakanan yaran, kusan tunda suka koma gidan majin ta sake janye yaranta jikinta da kyau,ta kuma sakasu cikin dukkan wasu addu’o’i na tsari na sha da shafawa.
Kwatsam Allah ya fiddawa fauziyya miji,a ranar har kukan farinciki maji tayi cikin daki, saboda tana ganin Allah ya kawo mata qarshen baqinciki da damuwarta. Da farko fauziyya taso taqi auren YA’AQOUB AJI, saboda yana da mata,sannan arziqinsa baikai yadda ta tsarawa mijin da takeson aura b,amma daga bisani yaci galaba a kanta bayan itama yaci galabar fidda matarsa daga gidan tun kafin takai ga shiga gidan.
Mahaukatan kudi mahmud ya kashe wa auren fauziyya,duk abinda ta nuna tace tana so shi zai saya mata,a lokacin hatta hidimar yara data gida data makarantarsu sai data tabu,ya tsaida wasu abubuwan da yawa saboda ya cika muradin fauziyya yayi mata aure kece raini. Sam maji bata damu ba,saboda tasan aski ya riga yazo gaban goshi,akayi biki aka tattarata aka migata gidanta.
A washegari sai da maji tayi azumin godiya ga
Allah,a ranar gidanta ya fara zamar mata gidanta,hatta da iskar gidan sai da ta jita daban da wadda ta saba shaqa. Cikin lokaci kadan abubuwa suka fara komawa saiti,saidai hausawa sukance ba’a taba bari a kwashe duka,haka yake,don duk da da tayi nasarar daidaita al’amura masu tarin yawa,amma har yanzu fauziyya na baki da zuciyar mahmud,a qalla a rana sai yayi zancanta ya kusa sau goma,kira kuwa sai da maji ta gaji tayi masa magana
“Kai yayanta ne kuma namiji, bai kamata ace kana vawan kiranta haka ba saboda tsira da mutuncinka, ina laifi a rana sau daya?” Shine aka samu sassauci ta fannin kira, amma banda haka babu abinda ya canza zani.