TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Ba zuwa office yau” ya fadi yana fita a nutse yana barin hallway din.

Hakan itama yayi mata,saboda ita kanta yau ranta a bace yake. Yau din ya raina mata hankali ya kuma bata mata lokaci yadda ya kamata,inda ace sunje office din to bata jin zata yi komai saboda haushinsa da ya cika mata zuciya. Baqinciki ya sanyata yin zaune a bakin gadonta kawai ta kasa fidda rigar ma daga jikinta, tana jin qarar tashin motocinsu,sai kawai ta koma saman gado ta nade abinta ta kwanta tana jan qwafa, kallonsa a kanta yaqi bacewa daga idanunta,babu wani namiji baya ga adam data taba tsaiwa va kalleta har haka saishi, duk da kowacce shiga jikinta yane yake da mayafi, amma har gangar jikinta tana jin kallonsa shi din me zurfine, don ya banbanta da yadda takejin idanun sauran mutane idan suna kallon nata.

Wayarta kawai ta jawo ta bude data tahau online, ta samu afifa kuwa a lokacin

“‘Bestie yau ba office?” Tsaki ta tura mata, sannan ta fara bata labarin rainin wayon da yau din toufeeq din yayi mata. Abinda ya bata mamaki dariyar da afifa ta dinga aiko mata da ita

“Banason wulaqanci bestie, idan ba zaki tayani ba ki barni da bacin ran da ya dasa min” sai a yanzun afifa ke sake yarda cewa akwai fa autanci da gaske, da taga gayyar na shirin watsewa sai tace

“Ba shiga sabgar da ba tashi yayi ba, banda abinki bestie duk duniya kallon miji da mata na haqiqa sukeyi muku,kinason ki tona muku asiri ne?, kinga dole yayi komai don ya tabbatar da ingancin aurenku a zuciyar kowa”

“Shi ya sani,bazan sake bari ya rainan wayo irin na yau ba”

“‘Nima ina bayanki” afifa ta fada tana boye dariyarta.
Gyara kwanciyarta tayi

“Bestie na fara wani tunani cikin raina,inason kiyimin cikakken bayanin yadda za’a magance epilepsy magani na har abada”

“You mean surgery?”

“idan har ta kama da hakan hakan za’a yi” gyara zama afifa tayi

“Idan nau’in epilepsy dinta yana cikin nau’ikan wanda za’a iya yiwa surgery din zaki iya taking risky na hakan? bayan family dinta ma dake tare da ita basuyi mata ba?” Ido tadan rufe tana tunanin maganar afifa, sannan ta bude tana maida mata amsa

“I can take the risk afifa indai za’a dace…..anjima zamu tattauna akan ciwon if you are available”

“Ba damuwa” ta amsa mata itama, tasan tsaiwa da rashin tsoro da va jima da dasuwa a zuciyar sãahar, indai tace zatayin to zatayi babu fashi.

Ta jima zaune a daki abinta, har akayi sallar azahar, ta bada farali tana zaune tana duba lokaci.
Batabar gurin ba sai data daidaici lokacin dawowar fadeel daga school ya kusa,sai ta miqe ta ninke abun sallarta, ta sauya kayanta zuwa wata gown sassauqa, don kitchen takeson wucewa kafin su qaraso. Ita ko nadeeya yanzun sun daina cin abincin kowa sai nata. Gown din tayi mata kyau sosai,ta maidata kamar wata baby musamman da gashin kamta ke fake a tsakiyar kanta cikin wani pink ribbon. Gown din me siririn hannu ce, kuma bata gama saukowa ba sai ta dora hijab da ya sauka har gasan gafafunta,ta zura wasu takalma masu laushi ta fito a sashen nata.

Dab da zata isa ga sassansu fadeela hajia garama ta fito. Kamar ko yaushe cikin shigar fariya da alfarma, mayafinta a kafada don ita din ba ma’abociyar yafa mayafi bace. Wani kallo tabi sahar din dashi sannan ta saki murmushi tayi gaba

“A’uzu bi khalimatillahit taammati minsharri ma khalaqa,Allahummakhfinihim bima shi’ita” ta samu kanta da furtawa saboda wani faduwar gaba da saukar mata sanadin murmushin murmushin da ta gani akan fuskarta.

Baaba ramatu ta samu da zuwaira suna hira a falon,ko ina a tsaftace kamar ko yaushe,suka gaisa cikin girmamawa sannan ta wuce kitchen bayan tace da zuwaira da ta mige zata bita suyi zamansu,abu me sauqi zata hada.

Veggies couscous ta shirya tare da egg
souce, tasan fadeela da son kayan zaqi,ba kuma kasafai take barinta vanzu tayi ciye ciyen kayan kwalin nan na banza da wofi ba,sai ta bude freezer ta fidda kankana ayaba yoghurt ta hado da madara ta zuba sugar tayi mata blending water melon smoothie data cikawa madara sosai. Tana juyeshi a wasu madaidaitan drinking glasses masu bamboo lids bayan ta zare glass straw din da suke dashi nadeeya ta shigo.

“Aunty N,yauma akwai special abu da alama, qamshi tun daga compound” tayi maganar tana legen smoothie din da take juyewa

“Abincin faddee ne” dan fuska nadeeya ta bata

“Amma ana wasa tare ci banban, nidai wannan smoothie din za’a tallafeni dashi,yau nasha rana, inajin ajiye aikin nan zanyi” ta fada tana narke fuska. Murmushi säahar ta saki ta maida murfin ta rufe ta zura mata straw din ta miga mata. Zuqa daya tayi ta lumshe ido

“Anty N,bazan iya shan wannan abun a tsaye ba bari na garasa daki”

“A fito lafiya ” ta fada tana murmushin santin da taga
nadeeya din tanayi.

Cikin fridge ta maidashi inda sanyi bazaiyi masa
yawa sosai ba,saboda ta saka ice cube qurin blending din so da sanyinsa. Muryarta taji tana qwala mata kira

“Tom an dawo kenan” ta fadi a ranta tana murmushi, a hankali taii sautin nata yana matsowa kitchen din,sanda ta lita dab da gofa saita waiwayo tana murmushi hadi da dan harara a idanunta na yadda ta tafi school bata nemeta ba yau din.

Maimakon fadeela sai idanunta suka hadu da nashi,gabanta ya fadi,ta dauki hannunta tana nadeshi a girjinta saboda yanayin rigar da take sanye dashi, already ta cire hijabinta tun shigowarta kitchen din, saboda tasan babu wanda yake shigowa, daga ita sai baaba ramatu sai zuwaira. Sam bata kawo zai shigo ba,saboda bata taba ganinsa cikin kitchen din ba sam.

Duk yadda yaso yiwa idonsa shamaki a kanta amma hakan ya faskara,sambala sambalan singalalin hannunta dake da lallausar fata me santsi yabi da kallo, a hankali ya zarce da kallon qirjinta data lullube da kyau da singalalin hannun nata,saidai duk da hakan hannun nata bai wadatar ba,saboda cikarsu da tsaiwarsu ya sanya suka fito ta saman rigar fam dasu.

Kadan kadan zuciyarta ke bugawa tana duban fuskar fadeela tare da qoqarin waskewa da nuna bata damu da shigowar tasa ba. A kasalance ya dauke idanunsa yana cewa da fadeela

“Sauka angel ki qarasa” saboda dama ha daukota ne a bayansa da kansa yau din. Kafada ta maqale

“Abby ki qarasa ladanka please,ka shigar dani ka kaini
gurin anty N” ta fada tana maqale kafada

“Ya salam” ya furta a ransa,wannan rigimammiyar ruwa takeson ballo masa. Magiya ta dage da yi, hakan ya sanya ya fara takowa da ita cikin kitchen din yana gogarin hana idanunsa kawai wanann gurin da ya zame masa kamar wata jarrabawa akan yarinyar.

“‘Matso abby ka gani” fadeela ta fada tana miqewa daga bayan nasa,nufinta ta taka bayansa sannan ta maqalewuyan säahar

“What?, sauko angel” ya fada yana dan daga kansa yana dubanta. Sake marairaice fuska tayi

“Please mana abby, munyi algawari fa kace yau bazan taka qafafuna a qasa ba” kai ya girgiza yana tuna sunyi hakan, amma shi bedroom dinta yace zai sauketa.
Idanunsa ya lumshe ya gara taku biyu gaba yadda yarinyar keso,saahar na tsaye tana murmushi idanunta akan fadeela, saidai can qasan zuciyarta wani mugun gudu takeyi kamar wadda tayi gasar tsere, taku biyunsa su suka hade dukka wani tazara dake tsakaninsu,wadan nan abubuwan da suke tone masa idanu,suka zame masa idanunsa barazana suka samu kyakkyawan masauki saman girjinsa. Yadda yaji saukarsu saman likinsa haka tail vadda girinsa ya tokare nata. Dukkansu jikkunansu suka karbi wani sago me nauyi da bala’in ratsa zukata,yayin da säahar jikinta ya dauki rawar da saura kadan fadeela tasha gasa, banda toufeeq yayi zafin namar taro yarinyar,ya saka dukka hannuwansa ya sauketa a gasa yana duban fuskarta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected