TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Hmmm,soyayya manya,mun jima da dawowa daga rakiyarta,mu da ita ko a lahira mun raba jaha” ta fada qasa qasa kamar me qunquni tana gyara kwanciyarta,sai kuma ta tuna zata yiwa maama gyaran wardrobe,don haka ta miqe ta sauko,ta kama gashinta me santsi ta daureshi waie daya,ta dora hula a kanta ta zura slippers ta fice.
********Ya jima a zaune yana juya wayar hannunsa,dukkansu mamaki suke bashi qwarai, nadeeya maji ga kuma mai gayya mai aiki fadeela. Yadda suke nuna tsantsar zakwadi da kuma farinciki akan wannan auren abun daure masa kai yakeyi. A yau sun jima suna waya da majiirin wayar da basu taba yin me tsaho irinta ba,duk da cewa kamar dai ko yaushe itace tayi kiransa bashi ne yayi kiranta ba. Dole bayan ya gama mamakin lamarin ya ajiye wayar gefe,dai dai lokacin sajjad ya shigo gurin bakinsa dauke da sallama.
Guri ya samu ya zauna yana kallonsa yana kwance cikin lounge chair
“‘nata jira naji daga gareka” kyawawan zagayyun idanunsa kawai ya daga ya kalli sajjad din
“Game da me fa?” Takaici ya kama sajjad din,kamar bazaiyi magana ba amma ya cije
“Ba aure zakayi bane malam?”
“Aure zanyi sai mene?”
“Bakasan kana da buqatar yin wasu abubuwa ba,mace fa zaka ajjiye cikin gidanka,a ina zata zauna?,ka hada mata lefe?,dinkunan biki da sauransu”
kamar bazaice komai ba,sai ya miqe ya zauna sosal sannan ya zura qafafunsa qasa yadda zaiji dadin zaman,idanunsa akan sajjad din
“Ce maka akayi wani aure ne duk da za’a tsaya masa wannan hidimar? kawai a daura ta shigo taci gaba da aikinta,ni kuma na bata gurin zama da ciyarwa da suttura that’s all,duk wadan nan abubuwan da kake jerowa sai ku masu auren farko,tun wani zamani da ya shude muka rufe wanan batun” sai ya miga hannu ya janyo plate din apple da Jacob ya ajiye masa.
Ido sajjad ya zuba masa,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya saki qaramin murmushi sannan ya miqe
“Zaka gane kurenka,indai macece ba’a cika musu baki,i pitty you duk lokacin da ka fada tarkonta,saboda haka kabi a hankali,shawarace kyauta na baka” baice masa komai ba sai qaramin miskilin murmushin da ya subuce akan fuskarsa,wannan maganar ta sajjad bata da banbancin da tatsuniya a gurinsa. Banda fadeela,babu abinda zai sanya ya biya sadakinta ta amsa sunan matarsa a bakunan al’umma bare azo gurin da sajjad din ke magana a yanzu.
*********Karo na biyu ya sake gwada kiran qanwar tasa,wannan karon ta shiga sabanin lokutan bava da kiran yake yankewa.
Spoon din hannunta ta ajiiye lokacin da kiran ke shigowa,wani hamshagin murmushi ta saki,yadda yayan nata yake bata kulawa tun daga wancan zamanin zuwa yanzu yana y mata dadi matuga,kuma har yau bata canza zani ba sanadiyyar jajircewarta
“Assalamualaikum barka da warhaka yaaya” hajiya qarama ta fada bayan ta saka wayar a kunnenta
“Yauwa barkanki dai FAUZIYYA” Cikin kulawa suke gaisawa da juna,ya tattambayeta yanayin kayan da taje siyowa a qasar. Tsahon mintuna goma suna tattaunawa sannan ya fara maganar da itace maqasudin kiran
“Kwanaki kusan bakwai ina kiranki na kasa samunki har ina tunanin akwai matsala ne”
“Babu yaaya wani lokaci ajiye wayar nake a nan hotel idan banason yawan kiran”
“To yayi kyau, Allah ya taimaka,amma inajin ai dole ki yanki ticket na dawowa sati me zuwa ko satin sama ma,don yaronki ya tashi aure,Allah ya amsa addu’armu” Wani irin mummunar faduwar gaba me hade da wani tashin hankali ne suka rufto mata,tamkar wadda ake juyewa duwatsu saman kan nata
“Yaron….na? wanne kuma?” Ta fada tana qoqarin boye gigicewar da tayi. Dan murmushi dr jarma ya saki
“Kina da wani d’an ne bayan toufeeq?,inda
‘yarki nace saiki tambaya nadeeya ko
HASEENA?” Sarawa kanta yayi da matsiyacin qarfi,wani zazzafan gumi ya karyo ilahirin jikinta ta kowanne sashe,taji kamar an saka allura da zare ana daure kanta,cikinta ya juya take bayan gida ya matsota
“Yaya?,ka manta haseena naketa ajjiyewa toufeeq? tunda anyi na farko ba’a dace ba?,ita kanta yarinyar bata taba kula kowa ba saboda ta sanya ranta akan TOUFEEQ din,ko yanzu haka sati uku ne kacal ya rage ta gama karatunta ta baro hannun babanta ta dawo nan nigeria don su daidaita kansu ita dashi”
“Banda abinki mijin mace hudu ne faidan yaga yana da ra’ayi uku ne sauran da zai cike ma,sannan ita kanta yarinyar bata da matsala,na santa farin sani,itace wadda ta taba rige president na kamfani na,kuma kema kin santa,wadda ke kula da fadeela kafin tahowarki”
“Kanbun uba!” Ta fada gasan ranta har bakinta yana motsawa
“Nanny fa yaya!” Ta fadi cikin daukaka sauti
“Ba nanny bace fauziyya,kawai tayi sha’awar aikinne,amma badon ta rasa komai ko kuma bata da gata ba,infact ‘yar Dr mamman girema ce,wanda kikaso a baya,kikace matarsa ce ta hanashi sauraro da kulaki” wani bala’in kawai bayanan yayan nata suka qara mata,Dr mamman da baya ganin kowacce mace a gabansa sai matarsa?‚buzuwar nijer,wadda koda wasa mamman din bai taba kallon wata mace ya taya da zummar zai aureta ba saboda yadda ya samu kula biyayya da dukkan wani jin dadin rayuwa da d’a namiji yake bugata da muradin samu daga wajen diya mace? ‚matar data wahalar da ita ta kuma kafa tarihi ta zama mace ta farko da tayi mata shamaki da abinda takeso? bayan tafiyarta toufeeq ya koma gidan,yarinyar tayi amfani da wannan damar kenan ta ja hankalinsa? har sai daya kamu da soyayyarta me zafin da ya kasa sukuni cikin sati uku kacal ya nema aurenta?,to itakam fauziyya tana me? wanne irin sakewa tayi haka?. Kamar dr jarma shima yanason canzawa,ta yaya yake maganar idan toufeeq din yana so?,bata saba jin wannan kalamin daga bakinsa ba a duk sanda ta bugaci wani abu daga garesa, komai tsananinsa kuwa
“Ya kikayi shuru?” Ya jefa mata tambayar. Cikin duniyanci da wayancewa tace
“‘Ina lissafin randa zan dawo ne,da abinda ya kamata na taho dashi na hidimar biki,sanann wannan karon abun yayimin banbarakwai ne,ba kamar aurensa na baya ba da akayi komai dani,wanann lokacin labari kawai naji” dan murmushi dr jarma yayi
“Kinsan kowanne aure da yadda yake
Zuwa,amma dai batun haseena karki damu,indai sun daidaita kansu shikenan,zanfi kowa farinciki da wannan,tuwo na,mai na”
rintse ido tayi tana jin zafin abinda yake fadaidan sun daidaita kansu kuma?,ba ruwansa kenan bazai shiga ba bare ya tilasta yiwuwar abun?. Har yanzu batasan me yasa ta kasa bude wata qofa guda daya tal ba,duk da tarin nasarorin da taci take kuma kan ci,amma har yanzu qofar bada umarni ga toufeeq bata kammala buduwa. A duk abinda ta umarta da yayi,musamman abinda ya shafi janibin rayuwarsa akwai yiwuwar yayi ko kada yayi,bata manta lokacin da ta umarceshi da kada ya dawo da Ameesha,sai ganinsa tayi da matarsa a wancan lokacin,ribar kawai da taci shine watsewar lamarin da yayi babu jimawa dutse a hannun riga. Da tana da wannan cikakkiyar damar,to da a yau zata umarceshi da ya dakatar da komal,ya ajjiye batun auren ya saurari zuwan yaruwarsa nan da sati uku masu zuwa.
Gefe guda babu abinda ya sake dagula mata lissafi irin haseena,batasan yadda zata tunkareta da zancan ba,bata iya jurewa tashin hankali,bata da juriya sam ko iya cinye abu,ta tabbatar babban bala’i da tashin hankali ne zai biyo baya. Dole tayi iyakar bakin gogarinta na ganin ta toshe dukka wata kafa da zata zamu labarin wannan auren,kafin sannan ta shirya fada mata tare da yi mata bayanin komai yadda zata fuskanta. Bacin ran haseena dai dai yake da nata bacin ran,ita daya qwal ta mallaka a duniya,tafi qaunarta sama da komai a rayuwarta,kai koda kuwa dukiyarta da take mutuwar so,take tattali da fadin tashin tarawa tsahon shekaru,ai dukka tana yine saboda ita haseena din.