TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Lomomi kadan ya rage ya ajjiye plate din saman freezer wadda tafi kusa dasu
“Baiyi dadi ba” ya fada yana yarfar da hannunsa,ya juya ya dauki ruwa ya balle murfin yana sha yana karantar fuskarta. Tayi algawarin daina biye masa, don haka sai ta rabashi kawai ta fita a kitchen din.
Murmushi ya saki, yadda yaga ta iya jurewa batayi magana ba,duk da ba haka yaso ba, don bakinta yazo ya sake sha, don hakan ba garamin dadi yakeyi masa ba.
Bai ganta a falo ba,cikin dakewarsa wanda ba zakace shine ya gama neman rigima yanzu ba a Kitchen ba yace da nadeeya
“Daga yanzu zuwa ko ysuhe, duk lokacin da hajiya ta fita unguwa ko wani guri ki sanarmin, immediately, but ina bugatar sirri,kin gane?” Kai ta gyada sannan tayi masa a dawo lafiya,cikin ranta tana mamakin dalilinsa na bata wannan aikin.
Kamar zata kifa lokacin da take sauke masa ruwa da drinks sanda yake zaune a gaban Dr jarma. Tun bayan da yayi aure wanna shine ganinta dashi na biyu,saboda gaba daya ta daina zuwa gidansu. Ko bayan data fita bayan hannunta ta sanya tana share hawaye, ta gaji da zaman jiran nan, ta qagu alqawarin da mommynta tayi mata na cewa nan da wani dan lokaci zai kawo kansa wannan algawarin ya cika,haqiqa akwai mutane da yawa da sai ta dauki fansa a kansu,hajiya qarama data zama mutum ta farko wadda ta yaudareta game da lamarin toufeeg tana cikinsu,koma tace itace mutum ta farko.
Tun zamansa gaban Dr jarma ya fahimci kamar cikin farinciki Dr jarma din yake, bai taba komai cikin abinda aka kawo masa ba kamar ko yaushe ya gyara zama,kansa a qasa bakinsa cike da addu’ ar Allah ya dorashi kan Dr din
“Abba alfarma nazo nema” ya fada yana dan shafa sumarsa dake sheqi.
Zamansa ya gyara yana dubansa
“Wacece alfarma kenan Muhammadu?”
“Abba,don Allah inaso SAHR tayi zamanta a gida,duk aikin da kake tunanin zata tayani, i can do it gaba daya ni kadai,idanma akwai buqatarta, zan ajjiye mata komai a study room dina ta ding aikin daga gida” dan shuru Dr jarma yayi na wasu sakanni, daga yanayin maganar toufeeq kadai ya shanshano wani abu, can gasan ransa dariya tana son kamashi amma ya danneta,sai yadan bata rai kadan
“Yanzunma kanason ka koreta ne da baqin halinka yadda
ka saba ko kuwa?” Da sauri ya girgiza kai
“No, Allah abba ba haka bane”
“To yaya ne?” Yayi masa tambayar yana tsirashi da ido
tare da son qureshi,don yanason samun tabbacin abinda yake zargi. Sumar sa kawai yayita shafawa,ya kasa cewa Dr jarma komai, baisan ya zai furta masa ba,ta yaya zaiyi masa bayani? abban baisan akwai kunya tsakaninsu ba?
“Muhammadu, ka gayan gaskiya”
“Abba…. I don’t know how to explain, kawai dai…..
Banason yadda maza suke kallonta,nayi duk iya bakin
gogarina akan hakan ta daina faruwa, har hijabai na dinka mata, amma wallahi abba a banza,abun is annoying me”
Dariyar da Dr jarma yaketa boyewa ta kufce masa, yayi qas da kansa yana kallon yadda toufeeq din da magana doguwa ke masa wahala amma yadda ya karkace yanata rattabo masa bayani wanda simple question ne da a amsa daya ya gama da ita. Ta wani gefen sai zuciyarsa ta karye yana tuna shekarun baya rayuwa tsakaninsa da SHIFA MAJI,yayi gogarin dai daita fuskarsa ya daga kal yana kallon toufeeq sanda yake fadin
“Don Allah abba a barta, kada kace a’ah” kafadarsa ya dafa yana murmushi
“Daina rogona muhammadu,mutum da matarsa?, ko a
baya ma ai ni bance dole ba, ta fuskar alfarma nazo, kuma naga kayi accepting, ko a lokacin inda kace ba zatayi yi ba ba komai, matarka ce qarqashin dukkan mulkinka da ikonka take,sai abinda kace zatayi,tunda bakaso na janye ta zauna ta kulamin da muhammaduna” sai a lokacin kuma kunya ta saukar masa,yayi qasa da kansa yana qoqarin tuna da meye da meye ne ya gayawa dr jarma din.
“Na gaya maka zanyi tafiya ko? gobe zan wuce Algeria”
ya fadi yana duban toufeeq
“Algeria abba?”
“Eh, zanje na gyaro wata barna, fatana Allah yasa kada gyaran ya daukeni lokaci mai tsaho, don banajin ko da zanyi shekara zan iya dawowa ba tare da na samu yadda nakeso ba” maganar ta dan Sanya toufeeg a duhu,amma duk da haka yayi masa addu’a da fatan alkhairi sosai, suka fada hirarsu irin ta d’a da uba.
[28/09, 9:21 am] +234 903 576 5837: “HUGUMA*
• TABARMAR KASHI*
Book 02 Page 36
A nutse da wani irin sanyi ya maida dubansa gareta,wani sashe daban take duba bashi ba. Har gasan ransa yaji bazai iya tafiya ya barta cikin office din ba, kamar bai gaji da kallonta ba
“Madam” ya kirayeta da wani irin amon sauti me laushi da sanyi. Tsigar jikinta tadan zuba saboda canzawar sautinsa a yau din, amma sai ta fuske kamar bata jishi ba.
Ya matsu ya Kalli qwayoyin idanunta,yanason yabar mata wani saqo me nauyi da narka zuciya,kamar yadda ya sani, sauran mata ma suka sani, idanunsa nada wani irin mugun tasiri da maganadisu me qarfi dake narka zuciyar mata da yawa,ya kuma tafi da tunaninsu. Uwa uba yana matuqar qaunar idanunta, tun a shekaran jiya daya qure musu dukkan kallo harda wanda ya wuce qa’ida ma idan akwai,kallon cikin idanunta na tuna masa yanayin da suka shiga gaba daya shi da ita a wancan ranar,yadda komai ya canza cikin lokaci qanqani. A ranar ya fara tabbatar da kyawun qwayar idanun nata.
Hannunta ya saki kawai sai ya rigo qugunta, sai gata
tsaye a gabansa suna fuskantar juna. Kanta kawai ta
sunkuyar ta hanashi kallon fuskarta bare akai ga idanunnata, abinda ya hanata kowanne yunquri na qwatar kan ta shine Karantar da tayi saima tana wajen
“Da mutane fa a gurin nan” ta fada qasa qasa wai don
kada saima din taji, saidai abinda bata sani ba,yadda tayi
cooling voice dinta ya sanya yaji tsigar jikinsa gaba daya
ta tashi,yadan ja wani numfashi hade da sheshsheqa
“| know, just i want to look into your eyes……please” jin
abinda ya fada ya sanyata maida idanun nata ta kulle
gam, tana nufin ba zata bashi wannan damar ba,har cikin zuciyarta abinda tayi niyya kenan, indai idanunta yakeson kalla zai bushe a wajen saima ce kawai ta zalunceta data ci gaba da zama a gurin, tana pretending kamar bata ganinsu,ita kuma tayi imanin dukka hankalinta yana kansu,banda ita da tuni ta tureshi daga riqetan da yayi.
Zanen fuskarta ya shiga kallo daki daki, tun daga
kyakkyawan eye brows dinta,miqaqqen hancinta mar
tsaho da tudu, shape din idanunta da kuma eye lashes
dinta masu tsaho ya dire zuwa kyawawan lips dinta da
suke yawna fuzgarsa,duk yadda yaso ya daure ya kasa
“Your lips look so lonely, would they like to meet mine?” Babu shiri ta bude fararen idanun nata tarr bisa fuskarsa da suka cika da tsoron kada ya aikata din. Qaramin murmushi ya subuce masa. Fuskarta ya kama ya hade fuskokinsu guri guda, abinda ya Sanya saima ba shiri cikin rawar hannu ta kwashe takardun da bata gama tabbatar da ingancinsu ba ta bude qofa ta fice
“Am dying to have my lips on yours one chance please!”
Duka garfinta ts tattaro ta turashi tana yin baya,numfashi take maidawa hadi da sanya hannunta daya tana gyara zaman hijabinta
“Why all these ne wai?, why?” Ta tambayeshi cikin zafin rai, zuciyarta na gaya mata shi kuma jikinta kadai yakeso, sha’awar ta kawai yakeyi, bashi da aiki sai burin son taba jikinta?.
Da baya da baya yaja ya jingina jikinsa da bango yana rufe idanunsa, tuni kowacce jijiya ta jikinsa ta amsa