TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Wait mana” ya furta yana dubanta, kamar ta zura da gudu haka taja ta tsaya sannan ta waiwayo da nufin ta samu gurin zama. Kadan ya rage bata fadi ba saboda tsabar rudewa,murdadden jikin nan nasa dake dauke da curarrun muscle ya bayyana muraran, gargasar dake lullube da jikinsa da damatsensa da suke fadin yadda mamallakinsu ke yawan daga qarfe, ba komai a jikinsa sai wani gajeran towel da ko cinyarsa bai gama rufewa ba don tabbas idan yace zaya zauna ne to kana iya hangen jikinsa sosai.

“Come and serve me masallaci zaki shiga ne haka na ganki da hijabi?” Ya fada cikin gatse, don ba haka yaso ganinta ba,yaso ya morewa kallonta ne sosai. Bata tankasa ba ta dawo gaban tray din

“Stop madam,ki cire wanann hijab din kada kiyimin gazanta” magana ce fal bakinta takeson maida masa, amma kuma tana tsoron kada allura ya tono garma,abisa dole ta hadiye ta zare hijabin yadda ya bugata ta fara saving nasa pancake

“Furar is enough” ya fada yana duba wayarsa da ya samu da tarin miscalls

Gida biyu hankalinsa ya rabu,rabi yana kan wayarsa rabi kuma tana ta fusgar hankalin nasa,so samu ace yanzun tana jikinsa yana shan duminta bai taba tunanin akwai ranar da wata mace zata dinga wasa da hankalinsa haka ba.

A nutse ta mige ta isa gareshi, dai dai sanda ya daga kiran dava shigo wayar tasa, miqa masa cup din tayi,ya miga hannu da zummar karba, kawai sai ya hade hannuwansu guri daya ya kuma jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinvarsa tare da manneta da qirjinsa ya riqeta tsam. Ko motsi hanata yayi,cikin tattausar muryarsa din nan da yau tayi kusanci sosai da kunnenta taii ya ambaci sunan maji yana kuma gaidata.

A galla ya kusa minti talatin suna magana da majin,ita kuma tana zaune zaman cinyarsa,wata muguwar kunya na dawainiya da ita,duk sanda ta motsa zai zake maidata jikinsa va manneta gam, har ya kammala wayar sukayi sallama,ya aje wayar gefansa sannan ya tattara hankalinsa a kanta. Tallafo hannayensu dake riqe da cup din yayi ya matso dashi saitin bakinsa,sannan ya kamo daya hannun nata ya aza saman cokalin dake cikin furar, murvarsa gasa gasa cakude da alamun damuwa yace

“Oya…feed me please” ya furta kamar wanda ke tsoron wani ya jishi. Shi ya taimakawa hannun nata ta hanyar rigeshi, yana tayashi debowa tare kaiwa bakinsa. Wani irin shiru ya ratsa tsakaninsu,ba wanda ke cewa komai a tsakaninsu,sai jikkunansu dake hade,dumin fatar cinyarsa da towel din bai gama rufewa ba tana ratsa

saahar tare da haifar mata da wani irin vanayi a cikin jikinta. Shima baice komai ba har suka gama,sai ya sanya daya hannun ya sake dafe tafukan hannayenta yana kallon cikin idanunta tare da sauke wata ajiyar zuciya me nauyin gaske

“Na gode, Allah yayi miki albarka” har ciki tsakiyar ranta tali dadin addu’ar, batasan cewa shi ya fita jin dadin samun wannan kulawar ba, duk da sai daya tilastata kusan ya samar da ita

“Ameen” ta furta can gasan ranta amma kuma labbanta sun motsa

“Amma….kin saka an dakeni kuma an hanani kuka?” Ya fada yana langabe kai cikin wata shagwababbiyar murya data sanyata daga kai ba shiri, idanunsu kuwa suka hade guri daya,sai ya dage mata gira abinda ya sanyata saurin mai da kanta qasa

“Yes maji tace zakuyi tafiya tana neman alfarmata na barki ki tafi, batason kuma doguwar tambaya ita tasan inda zakin keda angel” ya qarasa fadi cikin yanayi na nazari.

“‘Nima ina sake neman alfarma tare da rogon kauda duk wata tambaya daga ranka shakka ko kokwanto, khairan in sha Allah” har cikin bargonsa sautinta ya ratsashi, karon farko data masa magana da irin wannan salon, hashi kuma kusancin dake tsakaninsu ya bashi damar jin tone dinta tarrr

“Oh my god,repeat please,sake fadi” fuska ta tsuke,ta kuma shammaceshi ta mige da zafin nama,saidai ya rigata ta hanyar cafko hannunta

“Waye yace ki tashi?, haka kawai kin ciremin towel,oya mayarmin da abuna” sulalewa kawai tayi a wajen ta tsugunna tana curewa guri guda,ko kallonsa a haka ba zata iya sake yi ba bare ta gyara masa munafukin towel din daya dauro. Magiya ta hau masa

“Tashi kije” ya fada yana danne dariyar dake qasan ransa,da gaske yarinyar ta horu yadda ya kamata,inda dane da tuni yasha tsiwa da musu sau babu adadi. Koda ta fita waiwayawa tayi ta ballawa dakin harara tana jan awafa sannan tayi gaba

_niko nace a banza,ihu bayan hari kenan,idan yarinya ta isa tayi a gabansa mana
[04/10, 8:52 am] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *

Book 02Page 46

_assalamu alaikum,barkanmu da dare,jiya an samu typing error,zakuga na sana matsiyaciya a maimakon matsoraciya,ina fatan kun fahimci kuskuren dake gurin,na gode_

Tun daga ranar data fuskanci ina ya sanya gaba take rufe dakinta da wuri su kwanta ita da fadeela,idan yazo ya gani saidai ya koma ranshi babu dadiyaso ya sake wasata da kyau ya kuma more kafin lokacin tafiyar kamar yadda maji ta gaya masa. Amma a kwanaki itace take shirya musu breakfast tayi musu abincin da zasuci idan sun dawo,ta kuma hada lafiyayyen dinner. Sai a lokacin ya vadda da zancan hausawa da sukance a rashin uwa akanyi uwar daki, tabbas a rashin samun girkinta yake yaba abincin Jacob, bai taba tunanin akwai wani da yakai
Jacob iya girki ba sai gashi ya samu wadda ta fishi nesa ba kusa ba.

Hankali kwance säahar keyin shirin tafiyarta,shiru da meenal da hajiyan sukayi da al’ amuransu jikin säahar ya bata tabbas ba a banza ba,saidai ita kanta cikin satin baccinta ragagge ne, don addu’ar neman nasara tuquru takeyl.

Qarfe biyu na dare yana zaune cikin dakin nasa yana sarrafa CCTV camera din dake cikin dakin nata,duk da ta haramta kwanansu tare amma hakan bai haramta masa ganinta ba ta hanyar CCTV camera din, abinda ya zame masa kamar ibada,a kullum idan ya dawo daga aíki ya kammala komai sai ya zauna yayi bitar wuninta na ranar a cikin dakin,saidai daukar kadan yake samu,duk da cewa yawanci zazzafar dauka ce dake yawan dagula lissafinsa,don a nan ne yake samun damar ganinta sosai, abubuwan da bata iya barinsa ya kalla yadda ya kamata a nan yake samun dama.

Kwanakin data dauka tana sallar daren duka yana sane da su,ko a yanzun da tafiyarsu ta kama jibi ne yana bibiye da komai,amma har yanzu baici karo da inda tayi maganar tafiyar ko wani abu daya danganceshi ba.

Ajiyar zuciya ya sauke,ya tabbatar gobe zai tafka mata tsiya ne,bazai iya bari tayi tafiya me nisa haka ba ba tare da sunyi kyakkyawar gaisuwa ba,sai ya maida daukar ya rufe ya koma duba history na jiya da daukan da camera din ta yiwa sashen hajiya qarama. Bude video din yayi yana sake nazari,hajiya mansura ce ita da hajiya qaraman,kowacce fuskarsa cikin bacin rai,kuma magana suke da juna cikin fushi, saidai har yanzu ya kasa tantance me suke gayawa junansu saboda sunyi nisa da ma’ajiyar camera din tsaron. Ya jima yana duban fuskokinsu su biyun,yadda suke a haka a hakan ake nuna masa su cikin mafarkinsa,ya dade sosai yana sake bibiyar wasu motsinta na baya dake ajjiye sannan ya kashe yana sauke ajiyar zuciya

“Akwai gagarumin abu a qasa” ya furta a hankali, gaba daya zuciyarsa da gangar jikinsa suna bashi akwai babban al’ amarin dake tunkaroshi, saidar ya rasa meya wannan?.

*********Washegari tun bayan sallar isha’i da sukaci abincin dare ya kafa ya tsare a falon, wanda kusan wannan ba al’adarsa bace yafi zama a balcony dinsa study room ko cikin dakinsa,kasancewar shi din mutum ne maras son hayaniya ko a shiga al’ amarinsa. Fadeela na lafe a jikinsa tana ta masa hira,yayin da nashi idanun kekan säahar duk wani shiga da fita da taketa yi tana sake kammala musu kayansu na tafiyar da zasuyi a gobe saman idanunsa ne. Tun a yanzun ya dinga jin wata kewa tana ratsashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected