TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Sister nadeeya baqo mukayi ne?” Sai da tayi gaba sannan ta amsa mata
“Yaa toufeeq zan kaiwa, bayajin dadi ne” ajiye komai tayi ta biyo bayanta da sauri, kwanaki kusan bakwai kenan tanason ganinsa amma kuma tana hagura saboda zazzafan warning din da ya aje mata kan shiga sashensa haka siddan ba tare da dalili me qarfi ba,a yau din kuwa ta samu dalili me qarfin.
Idanunsa da har yau basu gama dawowa dai dai ba va zubawa meenal,wani kwarjini nasa tare da zazzafan gaunarsa na sake hudata
“‘Tsaya a nan” ya fada cikin tsawa, maganar tasa data sanyata jan burki ta tsaya din tana dubansa gabanta yana faduwa
“Daga yau sai yau, daga kuma rana irin ta yau, koda wasa, koda ganganci idan na sake gain gafarki a sassan nan sai na ballaki balluwar da bazaki moru ba kin gama tashi a aiki kenan har abada, bacemin a gun idiot!” Ga fada da tsawa me garfi wadda hatta nadeeya sai da hantar cikinta ya kada. Har takai qofa ta jiyo muryarsa yana cewa
“Ki hada dukka kayanki ki koma bangaren babarki, daga yau kar na sake ganinki a wannan sashen” kamar zata kifa haka ya garasa ficewa tana sakin kuka me sauti, bata ko damu da ma’aikatan gidan dake binta da kallo ba,har ta isa sashen hajiya qaraman ta sameta a parlor ta fadi a jikinta.
A rude ta dagota tana tambayarta
“Ke lafiya? me ya sameki haka?” Cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata
“Banason qarya da sakarci, yanzun nan na shiga dubashi na sameshi yana bacci,sannan bugu da gari ma babu ta yadda za’a yi toufeeq ya gaya miki haka” masifa da fada sosai ta rufe hajiya garama dashi
“Haka kike gani ko? zan miki qarya ne?, komai nace yayi sai kinyi shakka, bayan a gaban idanunki yakeyin wasu abubuwan?, ina dukka tutiyarki da alfaharinki? ina abubuwan da kike alfahari da su? duk ni a wajena a banza suke tunda toufeeq kawai kin kasa mallakamin shi to wallahi wallahi nan da watanni biyu masu zuwa indai baki mallakamin muradin zuciya ta, kema ba zakiga abinda ranki yakeso ba” tsananin bacin rai ya sanya hajiya garama ware hannunta ta mari haseena, karo na farko da hakan ta faru tsayin rayuwarta
“Baki da hankali ni kike gayawa haka?” Dafe da kuncinta take duban hajiyan
“Ni kika mara momy?” Yadda tayi tambayar a tsaye tamkar hajiyarce diya ta mari mahaifiyarta haseena. kallon da take binta da shi ya sanyaya jikinta,sai a sannan ta tuna, mahaifinta sai da yayi mata bayani kafin va barta ta taho
“Ba’a bata mata rai,saboda tana da wani hali me kama da cutar tsananin fushi” da sauri ta kamo hannunta ta rige tana fadin
“Kiyi haquri, nayi miki alqawarin mallakar toufeeq a wata guda kacal, qasa da abinda kika buqata”
“Ashe zan take faranti kenan kowa ya rasa” muryar hajiya Muneera ta baqunci kunnensu, abinda ya sanya suka maida hankalinsu bakin qofa. Kaifin idanunsu bai hanata ci gaba da qarasowa falon ba, itama su take kalla
“Ashe da gaske ke din ‘yar kunama ce fauziyya?,ni zaki yaudara kiyi wasa da tunani na? ki lasawa diyata zuma a baki yanzun kuma ki maye mata gurbinta da madaci?, tunda haka abun ya zama nafsi nafsi, kowa divan cikinsa ya sani to ki kwana da sanin muddin labiba bata samu toufeea ba haseena ma ta rasashi har abada” tana sauke furucin haseena na sauke mata lafiyayyen mari a fuska. Tsananin mamakin dava zarta zafin marin da shi hajiya Muneera ke kallon haseena baki bude
“Shashasha. ke har kin isa ki hanani samun muradin raina? ba mutum ba, ko mutuwa banajin tayi wannan isar”
“Kinyimin dai dai,ai da kin barta ma baki maretan ba” sai hajiya qarama ta matso gaban hajiya Muneera din tana mata wani kallo
“Bazance karki taka faranti ba,ki taka,amma ki takashi kina da sanin cewa idan zai bare zai bare ne harda aurenki da YAYA NA, zakiga mummunan sakamakon da baki taba tunanin aukuwarsa ba,karki manta inada qarfin sawa a auro a kuma saki a duk sanda naso hakan” Sai a sannan ta sauke hannuwanta daga kuncinta inda haseena ta mareta
“Bavan kuma va bare da aure na alagarki da yayanki shine abu na garshe da zai garasa zirarewa daga farantin,wannan marin da ‘yarki tayimin ki rubuta ki ajiye,sai ya zame muku nadama da ba zaku iya kauce mata ba, fauziyya kada ki manta,ni dake kar tasan kar ne‚wanda ya fasa a tsakanina dake baya ya raina Allah”
“Da kyau!” Hajiya garama ta fada sai haiiya mansuran ta tsugunna ta dauki jakarta data fadi a gurin,ta kuma juya tana fita daga sashen cikin matsanancin baqinciki vau ace yarinya kamar haseena da aka haifa a gabanta?,yarinyar da ko autarta ya girmeta ita zata daga hannu ta sauke a fuskarta?.
Gaba daya hankalinsa bai kwanta ba har sai daya tabbatar ya sanya a nema masa visan Germany. Duka duka so yayi ace ya samu cikin sati guda kacal,amma aka shaida masa bazaiyiwu ba,short stay ma zata iya daukan sati biyu kafin ta samu
“It’s too long ya rabbi* ya furta qasa qasa yana karanta bayaman da aka turo masan. Hakanan don babu yadda zaiyi yayi accepting a hakan ya sanyama ranshi salama da dangana, amma ji yakeyi ranar kamar ba zata zo ba, kamar ba zasu hadu ba.
A ranar bayan Dr anwar ya cire masa garin ruwan yayi booking na daki a bristol palace, suit din da ya saba kamawa ya kama na tsahon sati biyun, sabodia baya jin zai iya ci gaba da zama gida daya tare da hajiya garaman. Ya riga ya saita camera din da wayarsa, koda yana can zai iya ganin dukkan abinda yaso. Nadeeya batasan abinda yake faruwa ba kawai taji toufeeg din yace ta shirya kayanta kaman na 2weeks zasu bar gidan su sha iska, hakanan ya tura baba ramatu gurin abokiyar zaman mahaiffyar sajjad, gidan ya rage daga hajiya garama sai masu aiki.
*******Cikin nasara fadeela ta kammala kwanakin da suka diba mata kafin aikin, duka gwaje gwaje sun kammala,hakama shirin aikin nata,aka sanya mata rana da kuma lokaci.
Zuwan ba zata sajjad da afifa sukayi mata ana ya gobe za’a yi aikin,batasan cewa tana da rauni ba sai da taga bestie dinta,ashe dai tana bugatar wani a kusa,ta rige hannun afifa da kvau hawave nason sauko mata
“C’mon bestie meye haka? u are strong woman,kinyi abinda ba kowa ne zai iya ba, kici gaba da addu’a,it will be successful surgery in sha Allah”.
A ranar babu wani wadataccen bacci da tayi,kamar ko yaushe ta kwana tana sallah tare da addu’a me tarin yawa.
***K’arfe takwas na safe afifa ta shigo musu da lafiyayyen breakfast da sajjad yayi musu order. A tsaye gaban madubi ta samu säahar cikin black laffaya me adon silver a jiki. Agogon hannunta silver color take daurawa, komai nata cikin sanyi take yinsa,saidai tayi wani irin mugun sassanyan kyau,kayan sun haskata sosai tare da gara mata wani irin kwarjini, Wayarta ta jawo ta sake duba sagon toufeeq na daren jiya,wasu irin sagonni yake aike mata masu taushi da narkar da zuciya cikin kwanakin saboda koda ya kirata bata dagawa,haka kawai takeii a ranta kamar tayi masa wani babban laifi da bazai gogu ba,ta dinga jin kamar ta shaida masa abinda sukeyi a Germany. Idanun afifa a kanta har ta garaso, dai dai sanda fa ajjiye wayar ta maida dubanta kan afifa
“Afifa, am afraid” a nutse ta tako ta dafa kafadarta tana murmushi
“Karki saare bestie,khairan in sha Allah” sai ta miqa hannu ta dauko cup na tea data hada mata da plate dindake dauke da tarkacen chips dasu ketchup