TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

-the worst feeling in the worid is knowing you’ve been used and lied to by someone you trusted, and the saddest thing about betrayal is that it never comes from your enemies_

Ya maimaita kalaman sun kusa sau biyar yana jin wani abu yena taba zuciyarsa yana jin kamar saboda shi akayi duke weden nan maganganun, akwai wani abu clin reyuwarta bayan wanda ya bincika ya saniyes… ya san da hakan duk da a wancan lokacin yace bashi da bugater ya sani din, amma a yanzun sai yaji yana da she’awar haken. Maida littafin yayi ya rufe, a maimakon ye maidashi wajensa sai ya fice dashi daga dakin gaba daya

Guri yayi masa a davinsa sannan ya juya ya fito, tunda bai ganta a sassansa ba ya tabbatar tana sahensu nadeeya. Zai iya cewa a kwanakin shida su biyu rak yaga gilmawarta a sashen kwata kwata,duk da cewa shima din ba wai zama yake a gidan ba, yanata qoqarin ganin ya fara hada kan ayyukan da zaiyi a company din dr, so yake yana cika wata guda yabar qasar dawowarsa kuma sai baaba ta gani, abu daya zai masa cikas,ya tabbatar Dr shine mutum na farko da zai fara masa maganar yana da iyali a yanzu, amma yasan yadda zai tafi da komai,yanason ya danyi nesa kadan ya samu zafin da kansa ya dauka ya sassauta.

Sanda taji anyi knocking migewa tavi ta zauna sosai duk da yadda kanta yake ciwo kamar zai cire ta dauka baaba ramatu ce, da muryarta da tayi sanyi qwarai tace

“Shigo” ya murda gofar ya turata ya sanya qafarsa. Ta lumsassun idanunta da kanta data jinginar a fuskar gadon taga shigowarsa, bata tsamamci ganinsa ba,ta miga hannunta a da hanzari ta jawo dankwalinta ta budeshi tana rufe gashinta. Kansa ya dauke kaman bai gani ba,ya qarasa shigowa ya jawo stool zuwa gaban gadon ya zauna sosai yana dubanta. Kwarjini taji yayi mata kamar yadda yake mata wasu lokuta,kanta ta juyar wani bangaren gasan rabta tana mamakin abinda ya shigo dashi. A nutse ya kafeta da kallonsa, mayun idanun nan nasa suka dinga ratsa jikinta suna bata alamun akwai kakkaifan idanu a kanta,batasan me yasa ba,duk sanda zai kalleta sama da second biyu sai taji kallon har cikin jininta,abinda kaf rayuwarta bata taba ji ba akan wani. Yadda baice komai ba haka itama,bataga amfanin zuwan da yayi ya sakata a gaba yake mata kallon daukan alhaki ba,wannan ya sanya ta yaye duvet din ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon

“Koma ki zauna” ya fada still idanun suna kanta. Kamar ba zata koma din ba kamar yadda yace,sai kuma ta tuna

da gargadinsa, batason wani abu da zai kawo haduwar jikinsu waje daya ya sake faruwa,don haka ta dakata daga gogarin saukar da takeyi fuskarta na kallon gabanta,baya iya hangen fuskarta da kyau,sai gefen fuskarta dake dauke da kwantaccen gashi ta gefen kunnuwanta. Kansa yadan gyada kadan ya fuskanci gwanar taurin kai ce

“Kina da masaniyar matsayin hajiya a gurina?” Ya tambayeta adan kausashe, tun kafin ya gara komai a kai ta fahimci inda maganar tasa ta sanya gaba

“Ko na sani ko ban sani ba ba wanna bane ya kawo ni gidan nan ba,nazo ne don kula da fadeela, kuma na dauki alqawarin bata dukkan kariya da dukka iyawata,bazan taba barin wani abu ya cutar da ita ba alhali ina da ikon dakatar da shi, saboda haka na dakatar da ita daga bata magani don aiki nane”. Fuskarsa ta dan sauya yana mamakin qarfin halinta

“Kika dakatar da wa?‚are you in your sense?” Zuwa lokacin kasancewarsa a gurin kawai matsi ne da takura a wajenta don haka ciwon kan nata zuwa lokacin kamar an ninka mata shi, har ya fara sauka zuwa idanunta kamar yadda yake mata a yawancin lokuta idan yazo da tsanani. Waiwayawa tayi ta dubeshi kai tsaye

“Yes, na fada na dakatar da ita, bama ita kadai ba kowa a gidan nan, ciki harda kai mahaifinta”. Karon farko kuma lokaci na farko da garfin halinta tare da qarfin gwiwarta ya burgeshi yaso kuma bashi dariya har ya murmusa da wani kalar miskilancin murmushi wanda gefen bakinsa ne kawai ya motsa, saidai hakan ba qaramin qara masa kyau yayi ba. Gefe daya kuma yana karantar yanayinta da ya canza, tabbas akwai abinda yake damunta,yasan kuma ba zata taba fada ba,sannan muddin ya barta ta kwana a haka kota galabaita yayi imani daya daga cikin haqgoqinta kenan da ya gaza saukewa ne.

Ci gaba tayi da sauka daga gadon, tana ganin ta gama bashi amsa,no need ta tsaya wani dogon magana,gefe daya zuciyarta na sake cika da mamakin hajiya qarama,tare da jin cewa ta shiryawa tunkararta da dukka wani nau’in abu da zatazo dashi.

Sai daga gama sauka kaf yana kallonta ba tare da ya sake cewa komai ba yana sake nazartar garfin hali da kafiva irin nata. Sunkuya tayi da zummar gyara takalminta ta saka,sarawar da kanta yayi ya sanyata tallafeshi tana furta

“Wash” ba tare data tuna ma yana wajen ba. Sai a sannan ya mige a nutse, ya tako a hankali zuwa inda take,qamshinsa ya tabbatar mata da garin kusancinsa da inda take
[19/09, 5:33 pm] +234 903 576 5837: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*
Book 02
Page 20

Bude idanunta tayi a hankali ba tare da ta daga kanta ba,saboda tsaiwarsa a gabanta dava gefe ya bata damar ganin doguwar fara qal din qafarsa. Sake yunqurawa tayi da nufin tashi

“You can’t do it,lemme help you” ya fada yana miqa mata hannunsa. Kau da kai tayi,ta yaya zata bashi hannunta?,gobe yayi mata sharri yace ta taba masa hannu?. Wannan abun ya sanya ta qarfafawa kanta gwiwa,ta yunqura a karo na biyu ta miqe gaba daya,saidai ko taku biyu bata yi ba duhu ya mamaye idanunta,wani irin jiri ya debeta yayi baya da ita zai zubar a wajen. He is ready akan kome zai faru already,saboda yanayinta ya gama nuna masa babu lallai ta iya barin dakin kamar yadda taso,tsabar dai taurin kaine da kafiya irin nata,don haka cikin zafin nama ya tallafota,yayi mata kyakkyawan masauki saman qirjinsa. Duk da yanayin da take ciki amma hakan bai hana hancinta zuqar ni’imtaccen qamshin dake fita tun daga ainihin skin da gargasar qirjinsa,vest zuwa rigar jikinsa ba. Wani irin abu taji wanda ya tilastata damqe gaban rigarsa da hannunta,ya lumshe idanunsa kadan yana sauke ajiyar zuciya saboda yadda dumin jikinta ya fara ratsa rigar jikinsa zuwa fatarsa yana ratsa jikinsa sosai

“stubborn girl” ya furta qasa qasa da wata irin murya me taushi. So take ta tureshi daga jikinta amma ta kasa saboda jirin da takeji,yasa hannunsa ya tallafeta sosai,sannan ya fara takawa da ita sannu a hankali suna fita a dakin.

Hankalinta a tashe yake,bata son kasancewarta cikin jikinsa,tana jinta ne kamar a kan qaya,batason wani ya gansu a haka,to amma yadda takejin garin yana juya mata tasan tayi qarya tace zata iya takawa da kanta. A hankali suke takawa,bugun zuciyarsa na sauyawa da wani irin bugu na daban,qamshin turarenta na shige masa hanci,kamar yadda qamshin hair mist dinta ke ratsa dan kwalinta yana fitowa zuwa qofofin hancinsa. Duk taku daya da zatayi sai tudun qirjinta ya gogeshi,idanunsa yake rufewa yana jin abun yana tabashi har tsakiyar kansa,hakan ya sanya jikinsa ya fara weakening,ya dinga kokawa da kansa ya sake aro jarumta ya yafa,sai ya dinga Allah Allah su isa ya zareta daga jikinsa. Dab da zasu shiga sassan nasa yaja ya tsaya saboda muryar Joseph da yake jiyowa,ya tuna ya barsh ne yana goge goge. A nutse ya juya gefan damansa yana kallonta,rigar atamfa ce a jikinta,duk da dinkin boubou ne amma hakan bai hana tudun qirjinta fita ba sosai,da alama tana daga cikin matan da suke da baiwar cikarsa da kuma tsaiwarsa,ganin sun tsaya sai ta danso janyewa baya kadan,ya dauka zata fadi ne,da hanzari ya zanya dukka hannayensa ya tallafota don kada ta fadi inda kai tsaye yayi mata masauki a karo na biyu cikin qirjinsa ya maida hannuwansa ya rufeta gam a tsakiyar faffadan qirjin nasa,jikkunansu suka mannu guri guda dumin jikinsu kuma ya sake gauraya yana ratsa jikinsu da kyau. A tare suka sauke ajiyar zuciya wadda ta fito duka lokaci daya,sãahar ta lumshe idanunta zuciyarta na quna ta yadda yau din ya samu damar hada jikinsa da nata,jikin da yake iqirarij batasan darajarsa ba. Tattara dukka hannuwanta tayi ta tureshi daga gareta,abun yazo masa a bazata don haka ta zamu nasarar raba kanta da shi,idanunta da suke adan jirkice ta dubeshi dasu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected