TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Matso maza diyata,cin abinci tare da juna yana gara dangon gauna soyayya da kuma fahimtar juna.
..tafaddal moha” ta garasa fada
tana sauke idanunta akan fuskar toufeeq,cikin zuciyarta tana juya halayyarsa da har yanzun bata barshi ba,a gefe guda kuma tana sake yarda da hirarsu da nadeeya ta daren jiya.
Tabbas akwai aiki a gabanta,wanda kuma zata aiwatar dashi. Sãahar nada kyakkyawar zuciyar da bazataso ahalinta su rasata ba,zatayi dukkan me yiwuwa ta tabbatar ta riqeta cikin iyalinta.

Bata taba kawowa zai sauko din kamar yadda maji ta buqata ba,sai gashi ya ajiye wayar tasa,ya kuma zamo daga saman sofa din da yake zaune,ya balle links din rigarsa yana tattare hannun rigar tasa sama. Bugun zuciyarta ne taji yana qaruwa saboda kusancin da suka samu sosai dashi,ya zamana yana tsakiyarsu ita da maji,qamshinsa me wani irin taushi,irin gamshin nan dake tashi a hankali ya fara karakaina a wajen,yana cakuduwa da nata
qamshin.

Dukka su biyun suka kai hannu lokaci guda a tare saman fararen plate din da baaba ramatu ta hado dasu don fara zubawa maji abinci,ya damqi saman hannunta a tausashe yana tsammanin plate din zai dauka. Karon farko kenan da hakan ta fara faruwa a tsakaninsu,a tare kowannensu ya dauke nashi hannun,wani irin abu yaji ya tsarga yarrr a jikinsa,tun daga hannun nasa ya aika sagon kowanne sashe na jikinsa. Yayin da saahar taji kamar wutar lantarki ce ta jata,cikin rashin saninsu kowannensu sai ya shiga yarfar da hannu,maji dake karantarsu a fakaice tace

“‘Zuba mana moha” sake maida hannunsa yay,,ya buda komai ya zubawa maji ya ajjiye a gabanta

“Wannan yayimin yawa,kuci kai da
matarka,samu plate ka zubamin kadan” ta fada idanunta akan wayarta kamar batasan ta fadi wani abu ba. Sam bai taba mata musu ba,don haka ya dauki wani plate din ya zuba matan ya ajjiye mata,ya sanya cokali biyu cikin plate din kamar yadda ta umarta,sai ta ajiye wayartata tana gyaran zaman glass din fuskarta,ta jawo nata plate din da cup din tea tana murmushi tace

“Toh…. bismillah ko?”

“Dangari” sãahar ta furta a ranta,maji ta gama daureta da dukka jijiyoyin jikinta,batasan ta inda zata fura buda baki tana cin abinci a gaban wannan dan rainin hankalin ba,tana jin ta bata wani babban aiki ne da batasan yadda zata alwatar da shi ba.

Idanunsa ya lumshe shima vana budesu duka lokaci guda,ya motsa bakinsa kamar zalyi magana,sai yaga idanun maji din a kansa,don haka ya cinye duk wani uzuri da yaso bata,ya gyara zamansa yana lanqwashe gafafunsa ya dauki spoon daya tare da fara motsa abincin,ya riga ya fahimci abinda majin keso,zai kuma amintar da ita. Yadda taga yayin itama hakan tayi,saidai a nata bangaren ko loma daya ta kasa kaiwa bakinta,abin yayi mata yawa tako ina,gefe daya ga maji da takejin nauyi matuqa,daya bangaren kuma ga uban ‘yan girman kan nan da takejin yadda ya sanya mata ido sosai. A nutse yake juya lomar abincin a bakinsa,duk da cewa bawai wani yunwa yakeji ba,amma saboda ya faranta ran maji din yake cin abincin. Yadda ta takura din shi hakan yayi masa,yana karantarta tsaf ta gasan idanunshi,wanda ba lallai bane ka karanci hakan kai tsaye.
[16/09, 7:18 pm] +234 703 451 7171: *HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_

Book 02Page 17

Amsa mata yayi yana tambayarta hidimar da aka qare jiya

“Alhamdulillah, duk da wata tana tafe in sha
Allah nan kusa,saura kwanaki shida kacal meenal ta dawo,karatu ya qare sai aure in sha Allah” tayi maganar tana murmushi,kai dr mahmud ya jinjina

“To Allah ya zaba abinda yafi alkhairi”

“Ameen ameen,tuwona mai na in sha Allah” da kyau sagon ya isa kunnuwan maji,sai ta saki wani qaramin murmushi tana sake juya kanta gefe. Fauziyya ta riga ta makara,tayi makarar da bazata sake yin sammako ba daga nan har illa ma sha Allah,ta rigata isa gaban Allah,ta rigata kuma shiga kotun Allah,ranar yanke hukunci kawai take jira.

Hamdala dr jarma yayi sannan ya fara da yiwa toufeeq nasiha hadi da tunasar dashi nauvin da ya rataya a wuyansa

“Amana ce ita muka karbo maka,sai kayi qoqarin sauke haqqin Allah a wuyanka,duk da cewa ba wai yau ka fara aure ba” shikam gaba daya wa’azin dr jarma mamayarsa kawai yakeyi,duka abubuwan da yake lissafa masa a yanzun kamar an buga masa gudumar mantuwa,sai yanzun da yake masa bita suke dawo masa a kai, gaskiya ya fada,babu yadda za’a yi suyi wasa da Allah,shi kuma aure koda wasa akeyi,koda wasa aka daurashi to ya dauru kenan. Sai yaji lema tana tsatstsafowa daga gaban goshin sa yasa tafin hannunsa ya gogeta. Kan sãahar ya koma,itama yayi mata abida duka zai gayawa nadeeya,sai da ya kammala sannan yace

“Komai na kamfanina ya gama dai daita kamar yadda nake zato sanadin tubalin ginin aikin daku kuka farashi,so saboda haka nayi hiring naku duk da ban tuntubi ra’ayinku ba,zaku je kuyi conclusion na aikin da ku kuka kafa harsashinsa na wata guda,ku tabbatar da gyaruwar komai din,saiku miga ragamar ga sabbin shugabannin da zan nada kuyi tafiyarku,zaka riqe matsayinka na CEO,ke kuma diyata zaki taimaka masa ne a matsayi
PA dinsa saboda ya samu saugi da saurin kammala komai kada na riqeku da yawa a company din,hutun sati biyu kacal gareku na hutun aure kafin ku fara aikin”

Kusan a tare suka kalleshi,sai ya
sakarwa kowannensu murmushi yana gyada kai alamun tabbatarwa. Maida kansu sukayi ba tare da kowa ya iya musa masa ba,saidai ba abinda qirjin sãahar keyi sai bada wani fat fat. Ya tana qogarin nesanta kanta dashi amma al’amura nason sake kawo kusanci a tsakaninsu?

Duk yadda hajiya qarama taso daurewa ta gaza,suyar maganar takeji har tsakiyar zuciyarta,tayi gyaran murya sannan tace

“Amma yaaya, kana ganin hakan ya dace kuwa?,ya zaa yi harka ta dukiyar iyali a dauko bare a sakata a ciki?, next week haseena zata dawo,sai nake ganin ita tafi dacewa da wannan matsayin” sosai zuciyar maji keson maidawa fauziyya martani amma ta dakata taji wace amsa mahmud zai bayar? ya canza ko har yanzu ita ke riqe da akalar steering na rayuwarsa kamar yadda yake faruwa a baya?

Dan qaramin murmushi ya saki sannan
yace

“Banda abinki fauziyya,ya zaa yi mutum ga matarsa ta sunnah kuma da ita aka fara aikin,tasan makamar aikin sosai sannan a ajjiyeshi a hadashi da wadda ba matarsa ba?” Mamaki ya kama haiiya caramar hadi da rudani, dama sãahar din ma’aikaciyar MT JARMA GLOBAL ce?,me ya kawota aiki cikin gidan?,anya anya ba turota akayi ba?,dukka wadan nan abubuwan dake faruwa ba shiri bane ba kuwa?.

“Yaaya,naga tuwona mai na mukeson ayi,hakan ai zai gara musu ma fahimtar juna yadda komai zaizo da sauqi ko?” Ba maji data karanci fauziyya shekaru masu yawa ba take kallonta fes a tafin hannunta ba,hatta dr jarma yayi mamakin yadda take iya furta wannan maganar a gaban saahar,amaryar da kwananta daya tal a gidan miji akewa zancan kawowa kishiya nan da wasu watanni KO satittika?. Toufeeq ne mutum na farko da ya fara miqewa,don ya gaji da jin soki burutsun hajiya qaraman. Ba tun yau ba ta sani shima ya sani,ba kowacce magana tata yake iya bawa muhimmanci ba tun dazun da taketa zubarta baima gama fahimtar inda ta dosa ba sai yanzu,ta barshi yaji da danyan hukuncin da abban ya yanke masa na komawa company har na wata daya,kuma wai shi da yarinyar da ta riga tabar company din a gaban kowa,a yanzun zasu koma shi da ita a mazaunin miji da mata?.
Iska kawai yake furzarwa a bakinsa,ya akayi komai yakeson ya dinga juyewa daga ainihin yadda qwaqwalwarsa ke wassafa masa zai tafi?, matsalar hajiya qarama da dukka maganganunta bai daukesu a bakin komai ba,don ita kanta haseena din da take magana a kanta bai dauketa wata cikakkiyar mace ba bare wani wasan kwaikwayon hajiyan ya tabbata,damuwarsa yanzun yadda yarinvar ke gara kusantoshi cikin lamuransa,ya gama da case din maji na tafiya honey moon ashe wani yana tafe. Qaramin tsaki yaja,sai ya sauya akalarsa zuwa dakin fadeela ya dubata,yana jin baccin da akace tana yi din yayi yawa,yasan ba kasafai ta fiya baccin safe ba.
Baice da kowa komai ba ya taka a hankali ya fice daga dakin,maji ta waiwaya ga sãahar da kunya ta hanata motsawa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected