TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“You stole my heart” ya fada can qasan
maqoshinsa,labbansa kadai sune suka motsa. Itadimma lallabawa tayi ta zauna zaman kujerun dake gurin, tsahon wasu mintuna shuru ba wanda yace da kowa komai,yayi ta maza yana qoqarin binne komai a ransa ya mige ya tsaya saman qafafunsa ya fara takawa
“Let’s go” ya fada a taqaice, sai ya kasa ci gaba da tafiya sanda ya isa bakin qofa,ya tsaya har ta qaraso. Lalubar hannunta ya sakeyi ya hade da nasa,ta ja zata fincike yace
“‘Kina cirewa ban yafe ba” laqwas taji zuciya ds gangar jikinta tavi, bata da wani sauran zabi sai ci gaba da binsa da tayi.
Kamar ya koma haka yaji lokacin da suka isa hall din, bai dauka zaman meeting din da mutane da yawa ba haka idanu sukayi caa a kansa shi da ita dukka suka mige suna masa barka da zuwa. Da ka ya amsa yana jin nutsuwarsa na raguwa. A nutse y jawo hannunta ya jawo kujerar da aka tanada saboda zaman CEO ya matso da ita gabanta,ya zaunar da ita a kai sannan ya koma bava ya tsaya yana dafe da kujerar, tamkar yaron gidan da uban gidan nasa.
A schedule na meeting din one hour ne meeting ne, amma cikin mintuna talatin ya sallamesu. Yadda suka shigo yanzunma haka suka koma office din yana riqe da hannunta,wannan shi ne ya zama muhimmin topic na tattaunawa a cikin company din a ranar.
Tunda suka dawo duk bavan minti dava zuwa biyu sai ya daga kai ya kalleta. A duk sanda ya kalletan kuwa sai wani abu mai qarfi ya fusgeshi tattare da ita. Wasu lokutan har sai ya tsaida abinda yakeyi ya zuba mata idanu yana kallonta cikin wani irin nutsuwa da wank lamari me matugar qarfi kaifi da kuma zurfi cikin zuciyarsa.
Bata fahimci komai ba, kawai ta fuskanci yau din yana ta sanyata zurga zurgar dauko wancan ajjiye wannan.
Yayi amfani gwarai da wannan damar wajen samun damar morewa kallonta ta yadda ranshi yakeso.
A karo na barkatai ya sanyata dauko masa wani book cikin tsararriyar book shelf dake gefen table dinsa,saidai akwai tazara tsakaninsa da ita. Sanda ta miqe don isa gurin sai ya daga kansa gami da ajiye biron dake hannunsa,a hankali yake sake qarewa tafiyarta kallo, komai nata unique ne, bai taba cin karo da mutum me uniqueness irin nata ba.
Ta maida hankalinta sosai tana duba masa littafin da
ya aiketa ta dauko din,ba kuma wai don zaiyi karatu bane,a’ah,kawai yanason yaga wannan kyakkyawan takun nata. Yadda take tura baki da bata rai saboda bataga book din ba ya sanyashi sakin murmushi yana jin wata gajiya da kasala suna bin sassan jikinsa,wanda shi kansa yasan ma’anar hakan a tattare dashi. Ya miqe a nutse yana sanya hannayensa a aljihun wandonsa, har ya isa gareta bata sani ba. Daga bayanta ta tsaya, dab da ita,tazarar data rage a tsakaninsu duka baifi taku daya rak ba.
Muryarsa ya sassauta sosai ya kuma rage tsahonsa yana son daidaita kanshi da ita ya dawo da kansa saitin kafadarta,cikin laushin murya tamkar wanda yake a buge yace
“Am so tired,can you give me a hug pleasssssse” cak ta dakata daga abinda takeyi tsigar jikinta tana tashi,yadda yayi maganar saitin kunnenta ta shigeta sosai,sam sam bata tsammaci tsaiwarsa a wajen ba,saita qame a tsayen, bata juyo ba bata kuma ci gaba da neman littafin ba. Ragowar taku dayan da ya rage shi ya qarasa, cikin sanyi da tashi ya zura hannuwansa ta saman cikinta.va kuma jawota a mugun slow ya manneta da jikinsa. Kamar wadda aka yiwa allura ta zabura tana juyowa da sauri da nufin kufcewa,saidai kuma babu damar kuncewar saboda yayi mata zobe gaba da hannunsa. Kai tsaye idanunsu suka jone guri daya,ya lumshe nasa idanun tare da budesu lokaci daya yana sakin wani lafiyayyen siririn murmushi da ya sanyata kasa jurewa kallonsa saboda wani tsalle da zuciyarta tayi ta kuma ce mata
“He was elegant” kanta takeson kawarwa amma ya hanata wannan damar,ya kama fuskarta ya riqe da kyau yana mata wani duba dake dauke da tarin ma’anoni masu wuyar fassarawa,wanda yakejin tamkar bakinsa bazai iya fadinsu ba
“Hold me please hold me so close, that your breath become my oxygen” ya fadi numfashinsa na fita da sauri da sauri saboda yadda ya kwadaitu da labbanta. Bai iya controlling kansa ba kuwa sai daya dangane da bakin nata kaman dazun,ya shiga sauke mata hot kisses ya hanata katabus da dukka wani yungurinta na qwatar kanta. Har tsahon wani lokaci kafin ta samu nasarar tureshi, taja baya tana kallon idanunsa da nata idanun da hawaye ya cikasu taf yana gab da gangarowa. Bai wani damu da kalar kallon da take masa ba, yafi damuwa da yadda bata qaunar ya rabi jikinta,wanda a yanzun yakejin cikin zuciyarsa bazai iya wani dogon zamani ba tare da ya rabeta ba,ji yake kamar wani magnetic ne a tsakaninsu. Murmushi ya sauke mata da idanunsa da suka sakeyin wani irin laushi
“Your eyes driving me insane madan ki daina kallona haka” ya furta yana gyara zaman sumar kansa da yatsunsa
“Only you can give me that feeling” ya furta a nutse idanunsa har yanzu cikin nata idanun da bata iya gani sosai saboda qwallar cikinsu.
Ba tare da kowannensu ya sakeyin komai ba sukaji an tura qofar office din, sautin takalma masu tsinin dunduniya ya soma tashi kafin daga bisani muryarta ta bayyana cikin sallama.
Har cikin jinin jikinsa sai da yaji wani abu ya tsarga,lokaci daya gabanin yakai ga juyowa dukka wata walwala da nishadi da ya samu a yanzu suka fara narkewa. Säahar ke fuskantar qofa,don haka da ita idanunsu ya fara jonewa.
Fara tas din mata, wanda har haskenta yaso zarce haske na dabi’a,tana da wani irin kyau shimfidadde akan fuskarta,saidai kuma a gangar jiki, irin matan nan ne da basu da hips kwata kwata,duk kuwa da cewa ita din ba wai siririya bace amma rashin hips din nata bayyananne ne ga duk wanda yasan tsarin halitta a gurin mace. A shape gown ce a jikinta ta wata shadda ‘var mali komai na jikinta cike yake da ado da gawa
“Sãahar, nanny N ko?, i see” ta furta tana jifan sahar da wani irin kallo, zallar kyawun da bata tsammaci samunta a tattare da ita ba yana bugar son bugar da ita,tako ina tana hangen wasu qualities kai tsaye daga gareta ta cikin hijab dinta kai tsaye, kyan suffa ciki da waje wanda cikin qasa da minti biyu wani azababben kishinta daya ninka wanda take ji a kanta kafin ta ganta ido da ido va lullubeta.
Farat daya kwanyar säahar tayi mata recalling muryar, take kuma ta fahimci wacece, idanunta ta maida kan toufeeq wanda tashi daya kamanninsa suka canza da wani irin bacin rai da zallar tsana
“Barka da warhaka uban ‘yata” ta fada tana rangaji tare da jifansa da wani irin shu’umin kallo da tasan yanaso ada
“Kar ka damu yanxu am single, naje na dawo kuma dukka don saboda kai” zare idanunta sãahar tayi daga kansu,tanaji a ranta bata da bugatar sauraren kowa a cikinsu,bata son jin komai daga bakinsu, don ba matsalarta bane, kowa yaji da matsalarsa, kuma kowa ya rige damuwarsa don haka ta fara takowa da nufin ta isa ga gurbinta na dazu ta dauki takalminta da hand bag dinta.
Cikin jikinsa yaji tahowarta, zuciyarsa kuma ta gama gaya masa abinda zatayin, ficewa zatayi ta barshi da ameesha,fuskar da ya jima da shafe babinta cikin rayuwarsa. Rabuwa yayi da ita har ta garaso dab dashi, bata taba tsammanin yana ganinta ba,sai kawai ji tayi ya tattarata cikin jikinsa yayi mata wata kyakkyawar runguma. Mamaki ya hanata motsawa, sai kuma yadda kunnuwanta suka jiye mata adadin qarfin bugun zuciyarsa da ya qaru matuqa, ala dole tayi luf tana jin bugun sosai cikin kunnuwanta,abinda zai shaida maka lallai yana cikin fushi