TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Tashi kibi mijinki kinji, Allah ya yiwa aurenku albarka,ya tsone idon asara da hassada qyashi mugunta d mugun abu”. Cikin ranta sai data yiwa maji addu’a sosai data bata damar barin wajen. Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke tana lumshe idanunta,tanason ta zauna tayi bitar abubuwan da suka farun amma kanta ya dauki zafi,ba yanzu take da bugatar hakan ba, saita waiwaya sassan dakin fadeela tana duban qofar dakin,qaramin murmushi ta saki,tunda tazo gidan bataga fadeelan ba,tayi kuma kewarta sosai,don ba kadan ba tana jin yarinyar qwaral a zuciyarta,sai ta soma takawa zuwa dakin itama ba tare da tasan yana ciki ba.
Da gaske baccinta take lakadan hankali kwance,da alama tayi nisa sosai kuma tana jin dadin hakan,a tausashe ya zauna daga gefanta ya sanya hannu ya kama hannuwan ta yana kalla,kusan komai nasa ta daukeshi banda kamannin fuska da wani lokacin take yanayinsa,wani lokacin kuma yanayi take da maji. Sake damqe hannun nata yayi a tausashe yana sauke numfashi me zurfi daga hunhunsa,ko meye yake faruwa yanzun da shi ta sanadinta ne,lalurarta jarrabawa ce a gurinsa daya tabbatar akwai abinda Allah ke nufi a gareshi,kuma koma meye yana fatan ya zame masa kaffara da nasarar rayuwa.
Cikin jikinsa yaji alamun an bude gofar,da yake dakin ba wadatar haske nadeeya ta kashe mata kowanne fitila sansa zasu fita sal ya sanya bata hangeshi a gurin ba sam.
Ta gefen idanu yake dubanta sanda take takowa cikin dakin,sassanyan turarenta yana kwararowa tare da cika dakin. Sanda ta ganshi already ta iso tsakiyar dakin,taja ta tsaya dai dai sanda ta mige a nutse,saita juya da nufin fita a dakin,don ba zata iya zama dashi daki guda ba.
Batasan ta ina ya iso ba,batasan yaushe yayi dogon takun da ya rigata isa bakin qofa ba,ta dai ganshi yana maida key din jikin gofar yana kullewa. Batason ta nuna tsoro ko firgita,sai tayi kamar bata ga abinda yakeyi din ba,taci gaba da takawa zuwa bakin qofar,ta
Kama key din zata bude,wanne tudu wanne gangare sai ji tayi an mata wata wawiyar fusga an ajiyeta tsakiyar dakin. Yadda ta tsorata yasa gudun numfashinta ya qaru sosai,ta fidda idanunta waie tana kallonsa sosai sanda yake tsaye a gabanta hannuwansa cikin alihun wandonsa,ya zuba mata narkakkun idanunsa dake cike fal da bacin rai. Qara taku yayi gaba ya fara hade Gap din dake a tsakaninsu,sai ta fara ja da baya tana dubansa cikin zallar mamaki
“Meye haka?,ka bani hanya na wuce” ta fadi ganin ta qure bangon babu kuma sauran inda zata sake goce masa. Kamar da kurma take magana,bai fasa nufota ba yana dubanta da tsimammun idanunsa,miskilar fuskar nan tasa a mugun hade cikin rashin walwala. Idanunta ta mayar ta runtse sanda ya qaraso dab da ita taku daya kacal zaiyi ya hade da ita. Cak ya tsaya yana kallon yadda fuskarta ta soma yin ja,soft lips dinta suke shacking kamar tanason furta wani abu daga dan mitsitsin bakinta na rashin kunya amma tsoron da taji ta kasa fadin komai. Sannu a hankali idanunsa suka sauka kan qirjinta da yake a cike sosai a kuma tsaye,bugun zuciyarta na nuna alamun ya qaru ta yadda qirjin nata yake sama da gasa da sauri,ya lumshe idanunsa saboda yadda dumin numfashinta dake gauraye da qamshin jikinta ke sauka a wuyansa,wani abu yaji kaman ya fusgeshi,sai yayi taku uku baya a hankali yana jin jikinsa yana saki. Irin wannan yanayin ya taba ganinsa sau kusan hudu cikin mafarkinsa,sak kamar irin haka,irin wannan dukiyar fulanin da yasha kai hannu zai taba amma mafarkin ya katse a dai dai wannan lokacin,ko a yanzun sai daya murza hannuwansa dake cikin aljihunsa da kyau,yaja numfashi sosai yana son daidaita kansa,cikin husky voice dinnan tasa dake da wani irin kwarjini yace
“Open your eyes” a hankali ta fara bude idanun nata har ta kammala budesu gaba daya
“Ke wacce irin mara kunya ce?,ban gaya miki banason tsaki ba,kinyimin tsaki kin harareni me navi miki? ni sa’anki ne? ko don na aureki shine garamar qwaqwalwarki take gaya miki yanzun dai dai muke kamar yadda take gaya miki a baya?” Ya jefa mata tambayar yana tsareta da kallon nan nasa me ladabtar da kowa ba tare da yayi magana ba. Kalaman da ya gaya mata sai suka tunzurata,ta danne tsoratar da tayi din ta sake galla masa harara
“Waye yace ka dinga shiga gonata?,ba haka mukayi da kai ba,munyi da kai kowa zaiyi rayuwarsa ne ba yare da ya shiga rayuwar dan uwansa ba..
tunda nazo kagan na.
bata ida garasawa ba saboda wata muguwar ba zata da yayi mata,dumu dumu ta tsinci harshensa cikin tsakiyar bakinta wanda shine ya toshe sauran maganganun da tayi niyyar gaggaya masa. Wani irin zuqa yakewa bakin nata yana hadawa sa lips dinta cikin wani irin salo da zata iya cewa ta mugunta ce kawai.
Cikin sakanni gaba daya kwanyarta ta birkice da tsananin tsoro gami da firgicin abinda yake faruwa din. Kaf rayuwarta babu mutumin data taba hada baki dashi irin haka baki cikin baki,gefe guda kuma yadda labbanta suka dauki radadi ta gama saddaqarwa sun tsage ne kawai. Duk yadda take tunanin zata iya tureshi ta kasa,sai kawai hawayen da suka tarar mata suka budewa kansu da kansu hanya suka fara sauka,danshinsu ya gangaro zuwa kumatunta ya fara taba skin na fuskarsa.
A hankali yaja da baya qafafunsa na wani irin sanyi da laushi,ya kalleta lokacin da take dugewa a waien tana cusa kanta tsakanin gafafunta tana sakin kuka a hankali don kada ta tashi fadeela dake baccinta batasan ma wainar da ake toyawa ba, yatsuntsa biyu saman lips din nata da ko da bata kallesu ba tasan sun tasa sosai
“Idan wancan karon na takeki wannan karon bakin tsiwar zan cinye gaba daya,kuma bani zan hadiye ba karnuka zan sa a kaiwa,as from today karki sake cewa zaki sakamin wata doka taki,nine gaba dake so nine me sanya kowacce doka nayi niyya,ko zaman dadiro nake da mace bata isa ta kafamin doka ba bare sadakina na biya,ki aje a ranki bazan taba neman komai daga gurinki ba idan ma shi kikewa,don nafi qarfinsa,ko yanzun bakina da kika lasa saikin biya hakan” daga wannan ya juya a hankali ya fita a dakin.
[18/09, 7:21 pm] Mimah Yusuf: “HUGUMA*
* TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 18
Hawaye sosai takeyi tana shafa labban nata da suke mata zugi, anya ba baki afifa tayi mata ba? ‚idan ba haka ba me yasa yake mata kwarjini har haka?
“Martabar aure” amsar da zucivarta ta sake nanata mata kenan kamar yadda afifa ta gaya mata. Motsin fadee ne ya sanyata saurin share fuskarta da daidaita kanta. Ai tana hada idanu da sãahar din ta wantsalo gaba daya daga saman gadon ta qanqameta tana kiran
“Anty N,good morning” rungumeta itama tayi sosai cikin jikinta,a hankali takejin wani farinciki, bacin ran dake lullube a zuciyarta ya dinga zagwanyewa. Sun jima a haka sannan ta dagata tana kallonta
“Chubby fadeela ina wanka?” Kai ta langabe a shagwabe
“Sai kinzo ke zakiyimin” dariya tadan saki
“Kin fara girma fa,muje na gani” sai ta riqe hannunta suka wuce toilet din.
Sanda suka fito tana tsane mata jikinta aka tura gofar aka shigo. Baaba ramatu ce suna hada ido da sãahar ta tambayeta
“Ya akayi baaba” dab da ita ta iso, ta dan waiwaya ta kalli bakin gofa ta tabbatar a rufe take sannan ta warware bakin zaninta, wata leda ta ciro tayi saurin migawa sahar,sai sãahar din tasa hannu ta karba tana jinjina kai