TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Waye ya shigo?”

“Boss ne” ta amsa mata cikin girma mawa,maida wayar tayi ta ajiye ta fasa kiran toufeeq din,don tayi amanna nan din Dr jarman zai fara shigowa,kuma dole toufeeq din ya biyoshi.

Duk bayan minti daya sai ta kalli agogo amma bataji shigowar yayan nata ba kamar yadda ya saba yi a duk sanda ya kawo ziyara gidan,duk da cewa abune mawuyaci ka ganshi a gidan. Zuwa lokacin haqurinta ya gaza,ta kasa jurewa,sal ta miqe tsaye tana gyara daurin dankwalinta hadi da qwalawa me aikinta kira tace ta rigo mata wayarta ta biyota da ita.

Tabbas Dr jarma ne ya shigo,don ga galla gallan motocinsa da vake amfani dasu nan guda hudun a fake a parking lot na gidan.

Abun ya sake daure mata kaita maida dubanta ga sassansu fadeela. Gabanta ne taji yadan fadi,saboda jikinta ya gama bata yana can,don son tabbatarwa saita nufi sashen kawai kai tsaye.

A parlor din farko ta samu baaba ramatu tana qarasa kintsa dan abinda bai gama gyaruwa ba a sashen, kasancewar yadda tsafta ta ratsa kowa cikin gidan harta da ma’aikata maza da mata,basa barin koda tsinke a waje bare qura

“Yaaya ya shigo?” Ta tambayi baaba ramatu kai tsaye

“Eh suna ciki”

“Shi da wa?” Ta tambayeta fuskarta adan
yamutse

“Toufeeq amarya da alhaji sai hajiya maji”

“Danqari” ta furta har yana furucin nata yana fitowa fili. Daga kai baaba ramatu tayi ta kalleta,suka hada ido,sai hajiya qaraman ta basar kamar ba ita tayi maganar ba,ta sanya kai ga hanyar da zata kaita qaramin falon sassan gidan wanda daga can sai hallway na bedrooms dinsu. Kai baaba ramatu ta girgiza

“Allah ya kyauta” ta furta qasa qasa taci gaba da aikinta, zuciyarta cike fal da mamakin dabi’un fauziyyan da har yau suka gaza sauyawa.
Ganin idanun TOUFEEQ da sãahar dake a mazaunin suruka yanzu a gurinta shine kadai abinda ya sanya ta gaidashi da harshen larabci a taqaice,kamar yadda suka saba shekarun baya da suka shude. Wannan abunne yayi masa mugun fami hadi da tuna masa wani lokaci can baya. Majin ta mige zata fice tana
cewa “‘dan kun gama Khadija ki sameni a falo mu qarasa ko?”

“Da kinyi haquri kin koma kin zauna akwai maganar da zamuyi” Dr jarma din ya fada a tausashe,wanda shi kansa baisan da haka yayi maganar ba. Cak hajiya qarama ta tsaya tana jin qirjinta yana bugun uku uku,sautin da yayanta yayi magana da maji din a yanzu,wani tsohon sauti ne da yake mata amfani dashi a shekarun baya idan yana son lallashinta.
Wai meye yake faruwa ne?,sannan wacce magana ce da yau yayan nata ya hada iyalinsa,harda bare aurowar jiya amma ita babu ita aciki? koma meye za’a tattauna din ba zata iya Jurewa a tattauna ba tare da ita ba. Sai data dorawa fuskarta fara’ar dole sannan ta buda qofar dakin hade da yin sallama. Maii itace ta farko da idanunsu suka fara haduwa waje daya. Dauke kai maji din tayi kamar yadda ta yiwa dr jarma din da a yanxun ma ya samu nasarar dawo da ita ya zaunar duk saboda idanun mutum biyun dai,toufeeq da SÄAHAR
Sam bata ko gaunar jin muryar fauziyya a rayuwarta bare ganin gilmawarta,itace silar da har yanzu take zaune ba tare da wata gagarumar katangar dake qara cikasa daraja da kimar diya mace ba wato AURE,ko tuna abubuwan da fauziyya tayi mata a rayuwa batason yi,amma duk da haka tana godiya ga
Allah da ya bata wasu damarmakin,duk da wasu sun subuce mata,amma still har yanzu tana rige da lambar mutum ta farko data zamewa fauzivya qadangaren bakin tulu,tsare tsarenta suketa tafiyar wahainiya,wasunsu ma su gurgunce ba tare da sun cimma gaci ba

“Ashe duk kuna nan,abun na ahali ne,ko mu koma?” Ta fada da sigar tambaya.

“A’ah,qaraso mana,you are the part of duk tattaunawar da za’a yi din” dr jarma ha fada yana fidda gyara zamansa,har yanzu idonsa na kan maji din wadda ta baiwa banza ajiyarsu shida ‘yaruwar tasa.

Guri ta samu ta zauna a tsakaninsu,a sanann majin ji tayi kamar ta miqe ta fice a wajen,to amma kuma yin hakan kamar bada qofa ne ga fauziyya,so far kuma ita din tana jin a shirye take akan sake maido yaranta ilkinta,wanann na daya daga cikin boyayyun dalilan da yasa batabi ayarin family dinta da sukazo biki sun koma tare ba.

Kamar yadda suka saba toufeeq ya gaidata,tayi gogarin gagaro murmushi

“‘Lafiya lau ango,idonka kenan?” Gaisuwar da sãahar ta migo ita ta katse tuhumar da take masa ta sigar tambaya a fakaice. Wani irin shu’umin kallo tayi mata,tadan kada qafarta kadan

“Amarsu,lafiya ya kwanan baqunta?,koda yake
ma ai ‘yar gida ce na manta” ta furta tana sakin wani murmushi me dauke da ma’anoni da dama,gasan ranta kuma zuciyarta ke
sake cika da alwashi da algawura iri iri akan sãahar din,sai ta biya baqincikin da ta sanya ta kwana dashi a jiya sanadiyyar maida mata maaganganun da tayi. Maida dubanta tayi ga
yayan nata Dr jarma tana gaidashi.
[16/09, 7:18 pm] +234 703 451 7171: *HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 15

Kayan jikinta ta zare kaf ta shiga wanka,tanata qoqarin controlling kanta da fushin da yakeson taso mata a kansa,batason taje wajen maji fuskarta da wani yanayi maras dadi. Cikin miti hamsin ta kammala Shiryawa cikin wata qawatacciyar lallausar atamfar exclusive super me matugar kyau da tsari, dinkin tea boubou akayi mata wanda ya zauna mata a jiki qwarai da gaske, ya kuma fidda sigar kyau da dirin da Allah yayi mata,siririyar sarqar dake wuyanta ta gara fidda tsaho da hasken wuyanta. Medium chantilly vail ta yafa wanda ya dace qwarai da shigarta,ta wadata iikinta da turarukanta masu sanyin qamshi. Har tayi taku biyu gaba qafafunta sanye da wasu plate shoes na kamfanin saint Laurent sai ta dawo ta tsaya gaban mudubin tayi folding hannayenta a qirji,kenan yanzun tare dashi zasu jera zuwa cikin gidan?. Qaramin tsaki taja tana juya abun cikin ranta,ita sam ko hanya batason hadawa dashi,duka yadda ma ta lissafa abubuwan yadda zasu kasance sunata zuwar mata da sabanin hakan,totally ma bata taba kawowa zatayi koda rabin kwana bane a sassansa bare kwana guda cur,saidai ta riga ta tsarama kanta yadda komai zai tafi,bata yarda da wannar tsarin ba.

Duk da tare suke da jibril suna tattaunawa akan ayyukan da ya fara a Australia ya barosu ya taho nan,amma hankalinsa yana kan agogon hannunsa,lokaci lokaci sai ya daga ya duba,ransa yana sake baci. Ya tsani jira, kuma yana tsammanin ya sanar mata zasu shiga maji na son ganinta. Sam baiso ma main ta umarci ganinsu a tare ba,to amma yadda ya fuskanci maji na cikin murna matuga da auren nasa,bayason sam abinda zai tauye wannan farincikin nata.

Mintunan da ya diba mata suna cika ya miqe hannayensa zube a aljihun wandonsa yana yiwa jibril bayanin abinda zai tattara masa ya kuma tura masa duka bayanan ta email,sannan kai tsaye ya fice daga falon zuwa farfajiyar gidan yana takawa majestically kamar yadda ya saba.

Dab da zai isa ainihin sassan gidan nadeeya ta fito dauke da wasu trays. Har zata gota taji husky voice din nan nasa na kiranta. Da sauri kuma cikin murmushi ta sauya akalarta zuwa gareshi,idanunta a kan miskilar fuskar nan da kullum take a dinke tsaf,banda ita,kaf duniya batajin akwai wadda ke iya tunkararsa haka,sau da dama ita dinma yana mata kwarjini,wannan dalilin ne ya sanya ko yaya tayi masa wani laifi take shiga uku,iya idanunsa kadai sun isa sakaka a tara

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected