TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Hasbiyallahu la’ilaha huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim” ya fada yana nutsa yatsunsa cikin sumar kansa me santsi da laushi, sunan hajiya qarama kawai ke yawo cikin kwanyarsa,wani irin gumi ya yanko masa, ya sauko a hankali daga saman gadon, cikin jikinsa kawai yaji yana bugatar bibiyar footprint na CCTV cameran da bai samu bibiya ba a yau.
Saman qawataccen madaidaicin study table
dinsa ya zauna,ya fara bibiyar motsin komai na dukka guraren da ya sakawa CCTV camera din. Cikin mintunan da suke na qarshe,wadanda suka nuna masa awanni biyu da suka shude kenan yana gab da kammala kalla ya koma parlor din hajiya qaraman, inda yayi ajiyar CCTV camera din ba tare da saninta ba.
Fitowarta daga dakinta afujajan yaja
hankalinsa,yayi zooming na video din take komai ya bayyana,sak irin robar da me aikinta ta yar,tablet din da a ido suke kama da irin na fadeela,gama irgasu da ficewarta,sai yayi hanzari ya koma sashen CCTV din dake sashen su nadeeya din.
Yaga wucewarta falo ya duba ta dakin sãahar ba alamar motsinta,gabansa yana faduwa tare da ambatar
“‘La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” ya shiga bangaren dakin fadeela,cikin tsananin tashin hankali jikinsa nason rikicewa,saboda tuni zuciyarsa ta gama hasaso masa komai.
Ko ina na jikinsa ya dauki kyarma,ya saka tafin hannunsa guda daya yana lullube fuskarsa sanda hajiya garaman ta gama musayar qwayoyin tare da bin aikin nata da wadan nan kalaman. Gumi ne ya jiqashi sharkaf bakinsa yana rawa kamar wanda iskar qanqara ke kadawa
“Hajiya why?,why hajiya why!” Ya fada da mugun qarfi yana dukan table din har sai daya amsa kamar zai balle gida biyu
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” yayita maimaitawa,hawaye suna sauka daga idanunsa zuwa fuskarsa. Duk da yana iya tuna wasu abubuwa kadan kadan da suka faru zamanin quruciyarsa, amma bai taba tunanin hajiyan zata iya aikatawa fadeela irin wannan mummunar ta’asar ba
“Me tayi miki?! me tayi miki?!, ni zaki yiwa haka!, ni zaki illata ba ita ba,she’s innocent, batasan me duniyar ke ciki ba har yanzu!” Ya furta da qarfi kamar mahaukaci,ya kasa controlling kansa gaba daya,wani irin tashin hankali da matsanancin fushi yakeji sosai yana cin zuciyarsa
“Ya Allah, ya hayyu ya qayyumu,la takilni ila nafsy darfata ainin,aslih li sha’any kullahu ya Allah, astagfirullah wa’atubu ilaihi” harshensa ya samu ya kama wadan nan addu’o’in, yayita maimaita su babu adadi. A hankali nutsuwa ta fara saukar masa,saidai kuma hade take da wani irin mugun ciwon kai mara misali,bai shiryawa kwanciya ba sam amma tilas sai da gangar jikinsa takai ga gadonsa, idanunsa a runtse yana kiran sunan Allah kowanne sakan,yanason tuna wanne zunubi fadeelan ta aikata mata?, meye takeson cimmawa?, tabbas säahar ta hango abubuwa masu tarin yawa,abubuwan da yaci ace ya zauna sun tattauna komai zafin kanta da dojewarta, amma zuwa yanzun anzo gurin da bazai iya jurewa dawowarta ba.
Sosai ta dinga bitar kalamansa cikin kwanyarta.
Juyi kawai takeyi cikin duvet tana jinta so lonely,gadon yayi mata wani irin fadi,ba fadeela,wata zuciyar tace
BABU KUMA ABBYNTA ko?. Kamar zata qaryata amma sai ta kasa qaryatawar, saidai kuma tana mamakin ta saba da shine da har zataji kewarsa? bata da amsa face maida idanunta da tayi ta lumshe kawai.
Zafafa biyar
[05/10, 11:55 am] Mimah Yusuf: “HUGUMA*
_TABARMAR KASHI_*
Book 02Page 49
Washegari har qarfe sha biyu na rana bai fito ba,yana kwance yana jinyar jiki da zuciyarsa gaba daya.
He’s ready to meet them ko ina ma suka tafi ba tare daya gayawa maji ba,don bayason ta hanashi ko ta rogesa don yasan bazai iya ba,wannan ya sakashi ba shiri ya nemi Dr anwar,ya iskeshi cikin yanayin matsanancin zazzafan zazzabi,wanda dole ya sanya aka daura masa drip a parlor dinsa.
Ranar sukayi da Jacob zai dawo, amma baikai ga isowa ba, sannan Dr anwar yace lallai yaci wani abu,dole ta sanya ya turama nadeeya gajeran tex,sai gata ta iso parlor din a gigice
“Yaa moha,dama baka da lafiya?,jiya ba lafiya ka kwanta ba? me ya sameka?”
“Relax, relax” ya fada cikin coolness da jigatacciyar muryarsa da abubuwa da yawa suka tarar mata, idanunsa akan fuskar nadeeya wani irin tausayinsu yana ratsashi,waye yasan yawan adadin cutarwar da ta yi musu ne ma?. Ita dinma kallon toufeeq din takeyi,tana mamakin wanne irin ciwo ne haka farat daya da ya sanya fuskarsa ta faada?.
“Ki samo min tea da wani abu lite zanci kafin ruwan ya aare”
“Okay yaaya” ta fadi tana juyawa da hanzari ta fita a sashen,ya rakata da ido har ya gama fita sannan ya maida idanun nasa ya kulle.
Shawaginta na biyu kenan cikin gidan, saidai sam sam bataga wulgawarta ba,hakanan bataga motsin fadeela ba koda wasa,duk kuwa da cewa yau din weekend ne,baka rasa zirga zirgar yarinyar a farfajiyar gidan wunin ranar gaba daya,musamman idan basu fita ba, sannan shi kansa toufeeq an shaida mata yana cikin gidan,amma tun daga wayewar gari zuwa yanzun ace bai nemeta ba?,duk da ta dade da lura abubuwa nata canzawa, tun daga ranar da yarinyar ta amsa sunan matarsa kawo yau,to amma kuma lokaci ta bawa kowa,jira take ta gama yiwa kowa shirinsa na daban.
Ko ubansa jarma da yayi tafiya ba tare da ya shaida mata inda yaje ba,da kuma adadin kwanakin da zaiyi kamar yadda ya saba shaida mata, tana sane da wannan, kuma ba zata taba bari hakan taci gaba da faruwa ba
Nadeeya na fitowa sukayi clashing da hajiya garama
“Ke,ke lafiya?” Hajiyan ta kira nadeeya da sauri,dan datakawa tayi
“Ba komai yaa toufeeq ne bashi da lafiya zan sama masa wani abu yaci kafin a gama qara masa ruwa” gaban hajiyan ya fadi, saboda a yanzun bata shirya wani abu ya samu toufeeq ba sam, shine hope dinta, shine kuma matakala sannan kuma tsananta na dukka plans dinta
“Me ya sameshi?” Ta tambayeta cikin damuwa, dan goge zufar goshinta tayi da tafin hannunta
“Ban sani ba mommy, kinsan sanin ainihin ciwon yaa moha ba abu bane me saugi tun asali”
“Na sani, jeki kawo masan” ta fadi tana wuce nadeeya zuwa sashen toufeeq din.
Sallamarta kadai yaji ya maida idanunsa ya rufe, ko da wasa baison gain fuskarta, domin har zuwa lokacin bai gama yanke matsaya akanta ba ganinta da idanunsa a wannan yanayin da yake ciki na iya tunzurashi, kuma. komal yana iva faruwa
“Muhammad” ta kirashi a hankali amma sai yayi banza da ita duk kuwa da hannuwansa suna motsawa kadan kadan. Sake kiran sunan nasa tayl a karo na biyu amma ya bawa banza ajiyarta,saukar muryarta cikin kunnensa dai dai yake da saukar tafasashen ruwan dalma.
“Ko ya samu bacci? na dawo anjima” ta fadi qasa qasa sai ta juva tana fita daga falon. Tun bata gama fita ba ya bude idanun nasa, yanajin kamar ya jawota yayi mata mugun dukan da sai ta gaya masa laifin da fadeela tayi mata a rayuwa,amma dole yayi aiki da hankalinsa a dukka hukuncin da zai yanke, saboda ya riga ya sani girman matsayinta wajen mahaifinsa, after all hausawa sukace idan baka iya kama barawo ba shi sai ya kamaka, saidai daga rana irin ta yau, koda fadeela tana gasar, to ba shakka ya haramta mata ganinta kwata kwata.
A gurguje nadeeya ta hada masa duk abinda zai bugata, tana fitowa falo zata wuce meenal ta shigo, ba wani sabo bane me yawa a tsakaninsu ba duk da cewa shekarunsu tazarar kadance ga kuma dangantakar dake tsakaninsu amma ko yaushe kamar bagin juna suke. Ita nadeeya mutum ce me faran faran da son jama’a ko kadan bata dauki duniyarta da fadi ba bata kuma dauki kanta ta aje can da nisa ba yayin da meenal take akasin haka tana da matugar fadin rai da jin kanta cewa ita din wata ce ta daban, gwanar girman kai da fadin rai, kamar zata wuce sai kuma tace