TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

A yau din duk yadda yaso ya share kaman yadda ya saba sai yaji ya gaza dannewa. Wow din da Jamal ya furta sai yakejin kamar a kanta ne

“Dole ka kare martabar aure, ko ba komai sunnar ma’aiki ce daya kamata ace an tsare kimarta” wani sashe na zuciyarsa yaji yana gaya masa.

Cikin nutsatsen takunta ta iso bakin motar a hankali, kallo daya tayi masa ta janye idanunta tana rage kaifin fara’ arta,wanda wanna din wata dabi’arta ce da tuni ya gama ganeta. Hannu tasa a nutse ta budewa fadeela seat din ta daya side din, qasan ranta tana gulmarsa. Zata iya cewa tsahon lokacin da ta dauka dashi zata iya rantsuwar bata taba gain dariyarsa kamar yadda sauran mutane sukeyi ba,wannan baqin eye glasses din da yasa ko yau din kuma tsautsayin kora da sauke kwandon masifar akan wa zai fada?.

Tambayar da ta yiwa kanta kenan, wadda tayi dai dai da saukar sautin muryarsa

“Ji mana” ya fadi yana zube mata zagayayyun idanunsa dake da haske qwarai. A nutse ta juya suka hada ido,a hankali idanun nasa suka sauka akan lips dinta daketa ayallin lip gloss. Tun wancan ranar bata sake maimaita saka jambaki ba,tunda yayi mata wannan abun. Bata fata ya maimaita kusanto jikinta,shi yasa ta daina sakashi kwata kwata a bakinta.

Dubansa ya sauka daga cikin idanunta zuwa lausasan lips din nata,haka kawai yaji ya hadiyi wani yawu. Sai kuma ya fara qoqarin saita kansa yana sake hade ransa

“Wannan shigar bata yi ba,go and change” sosai mamaki ya kamata,sai ta sauke dubanta a nutse ta a kallon kanta tun daga yatsun qafarta zuwa ainihin gangar jikinta,bataga ta inda ake ganin wani abu nata ba. Yana daya daga cikin abinda ya sa take yawan zabar shigar

laffaya saboda yadda take suturta kaso saba’in na surarta

“But……me shiga na yayi,is like fa kana shiga hurumin da ba naka ba” ta fada tana hade ranta da kyau. Wani kallo da ya dago ya aje mata sai da taji tabbas tayi subutar bakin bashi amsar da tayi a yanzun. Bai sake bata damar yin tunani na biyu ba taji kawai ya damqi hannunta,bai tsaya jiran komai ba ya nufi sassansu yana riqe da tsintsiyar hannun nata,yana jin zuciyarsa na wani irin zafi,ba tun yau ba shigar ke tsole masa ido,daga yau kuma ta bar yinta kwata kwata.

“Ka sakarmim hannu mana,kama wuce ga’ida fa” ta sake fada da nata zafin sanda suka isa qofar dakinta. Fusgota yayi ya jefata jikin qofar yana binta da kallo. Take tsoro ya kamata cikin ranta tana mamakin abinda ya Sanya farar qwayar idanunsa sauya kala lokaci guda

“Idan na sake jin bakinki sai na shayar dake mamaki” ya fada da zafinsa shima,sai yasa hannu ya murda handle din dakin ya buda qofar ya tura saahar din ciki. Tamkar kurma haka ta zama,tayi tsaye tana kallonsa sanda ya bude closet dinta yanata debo kaya yana zubawa saman gadonta. Batace masa komai ba har ya kammala,ba tare da ya rufe ba ya tako a nutse ya tsaya gaban kayan

“Ba kwalliyar ki akace kije ki nuna musu ba da zaki dinga sanya wannan abar,tun randa kika fara zuwa aiki har yau,ki cireta ki zabi wasu daga cikin kayan nan ki saka ki fito” Sosai ranta ya baci, ita ko kadan bata taba sanya laffayar da sunan kwalliya ba,hasalima tana sakata ne saboda tsaro, batasan yawan kallo, tana da tarin kaya lace atamfa shaddodi da sauransu kayayyakin qyale ayale na mata, amma duk ciki tafi qaunar sakata muddin zata shiga taron daya hada hadakar maza da mata. Abinda bata sani ba,a duk sanda ta saka laffayar tana yi mata mugun kyau ne,tare da sake nuna zallar dangantakarta da shuwa

“Bazan iya canza kowanne kaya ba” ta fada masa kai tsaye tana dauke kanta daga sashensa zuwa wani sashe na daban hadi da goye hannunta a qirjinta.

Ko motsinsa bataji ba bare ta sanya ran yana dakin,har zuciyarta ta fara gaya mata ya fita ne,abun mamaki sai taji hucinsa dab da ita,kafin tayi kowanne motsi taji ya kama daurin lafayar dake qugunta data yiwa daurin zarge ya wareshi,a take ta fara warwarewa daga jikinta.

A mugun razane ta kama laffayar ta cukuikuyeta,don tabbas muddin ta warware din ta gama tozarta a idanunsa,zai ga shape na komai nata ne,don wasu rubber material ne a jikinta me golding masu tsayawa dai dai jikin mutum. Hannu daya ya sanya ya zare laffayar a jikinta qwayar idanunsa cikin nata yana karantar yadda hankalinta yayi wani mugun tashi,yayin da ita kuma ta dage tana gogarin tattarota, wani tashin hankali yana bayyana qarara cikin idanunta. Ko kusa ko alama garfinsu baizo daya ba,tayi imanin idan akaci gaba da haka dukka laffayar zata zame ne ta barta gayanta.

Dole badon ta shirya ba cikin rawar murya tace

“Am sorry i will change it please” yadda tayi maganar da mugun sanyi muryarta na rawa ya karya lagonsa,sai kawai ya sake mata laffayar yana cewa

“Kin dauka ni abokin wasanki ne?, Bayan na biya sadakinki duniya ta shaida ke din kin zama halal din da zan iya yin komai dake ba tare da na zama abun zargi ba shine har kike da zarrar tsaiwa kina fadamin wannan maganar na ina wuce hurumina?” Sake rigeta kawai tayi da kyau cikin tunanin mafita

“Bakisan zan iya mai dake naked ba kuma nace kiyita zama a hakan a gabana?, kuma banyi laifi ba har wajen Allah?” Daga furtawar kawai da yayi sai taji kamar ma ya maidata tsirarar, abinda ya sake mugun razanata kenan ta kasa cewa komai sai karyar da wuya da tayi. Ya gano ta karaya sosai,sai yaja baya yana qara nisan tazarar dake tsakaninsu

“na baki minti daya” ya fada yana sake ja da baya hadi da maida jikinsa ya jingin da mudubi. Cikin rudewa take dubansa,yana nufin a gabansa zata tube ta canza kayan? tashin hankali
[24/09, 8:19 am] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_

BOOK 02 Page 28

“Don Allah ka bani guri, zan canza” ta fadi kamar zata rushe da kuka, idanunta na fidda wani qyallin hawaye, da gaske dai mutumin nan dan iska ne. Idonsa ya lumshe kana ya budesu,duk sanda hawaye suka cika a idanunta wani irin haske suke garayi

“Zan dawo muddin kika batan lokaci” yana kaiwa nan ya juya yana fita a dakin. Duk da taso tare hawayen amma saida suka silaloAllah ta yarda baki afifa tayi mata

“Aure yana garawa namiji kwarjini a idon matarsa, duk wannan cika bakin da rashin kunyar taki idan baki wasa ba saikin nemeta kin rasa” daya daga cikin maganganun da sukeyi da afifa kenan,wanda ita a nata gurin dai dai yake da tatsuniyar gizo da qoqi.

A gurguje ta cire ta sauya da wata atamfa, plain zani da riga ne, ta dora daurinta ta maida mayafin kayan sannan ta fito. Cikin hallway din ya saka wata kujera yar garama ya zauna. Tana bude qofar yana daga kansa daga danna waya. A hankali take takawa saboda bacin ran da yake cin zuciyarta na irin kama karyar da yakeyi mata. Sati biyun da tayi dashi cikin MT JARMA company kawai tana danne zuciyarta ne, amma kama karya kawai yakeyi mata. A nutse ya sauke qafafunsa qasa daga dora daya saman dayan da yayi, still idanunsa suna kanta, kai ya girgiza

“Koma ki cireta,batayi ba” sai data kalli kanta,kamar zatayi magana amma kuma yadda ya kafeta da kallon nan nasa yasa ta kasa fadin komai,sai kawai ta juya din tana jin zuciyarta kamar zata fashe.

Karo na hudu kenan ta sake fitowar idanunta na mata radadi saboda hawaye,yau din kamar wata wadda kamfani suka dauketa contract na fashion show,ta tsaya a gabansa tana jifansa da harara a fakaice, cikin ranta tayi rantsuwar wannan ce qarshe, muddin yace batayi ba bazata sake komawa ba. Kallon da yayi mata wannan karon yafi na wadancan shigar, duk da abaya ce me sulbi “yar qasar Turkey amma ta fiddata a balarabiya zamm.Janye idanunsa yayi yana miqewa tare da jan sirirn tsaki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected