TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Haka zalika idan kwakwalwa na so misali ka daga
hannun ka zata Yi relaying sakon ne ta hanyar aika
electric signals ne ta nerves zuwa hannun sai ka daga
shi kawai,wnn shi ake kira voluntary movement, xaka iya yin shi duk sadda kake so kana da control on kayi ko Kar Kar kayi Amma kamar bugun zuciya kyafta Ido,
movements na kayan ciki wajen sarrafa abinci da sauran motsi da sassan Jimi ke Yi Wanda baka iya controlling shine involuntary movement dukan movements din nn akwai sassan kwakwalwa da ake da alhakin Yin su Guiyoyin kwakwalwa, NOTE akwai jijiyoyi kala kala a jikin mutum kamar na jini,na kwakwalwa,na ba jiki kariya daga cututtuka da sauran su suna da sunayen su na turanci, Amma dai bahaushe duka jijiya yake Kiran su).
Abun da yake faruwa a epilepsy shine ita kwakwalwar kwatsam zata saki wadannan electric signals din ne lokaci daya sai ta Kuma kasa controlling dinsu shi yasa
Zaki ga sun fadi kusan ko Ina na jikinsu Yana motsawa uncontrollably a Hakan was har fitsari ko bahaya Yana kufce masu
Yadda electric signal din ke faruwa lokacin attack din is similar to kamar wutar lantarki na spark ne abun da yake faruwa kenan a cikin kwakwalwar
Attack din Yana faruwa ne kusan kamar a stages 4
1) na farko ana Kiran shi aural stage wato kamar warning sign ne cewa anytime ka fara Jin wadannan alamun xaka iya samun attack Kuma kowa da yadda yake ji wasu zasu rika Jin cowon Kai,ko su rika gain was abubuwa,ko su rka Jin wava Kara ko harshen su ya rika Jin wani dandano ko jikin su ba dadi kowa dai da irin abun da yake ji sai mutum yayi preparing ya samu waje ya kwanta saboda gudun samun raunuka
Sai stage na biyu shi ake kira Tonic clonic stage shine actual convulsions din Zaki ga mutum ya fadi Yana jujiga Yana zubar da miyau da fitsari da sauran su dai actual seizure din
Stage na 3 shine post ictal stage kamar recovery k nn bayan seizure ya tsaya zasu zama confused suna ganin Jiri da cowon jiki snn bacci Mai nauyi zai dauke su.
Stage na hudu Kuma na farawa ne bayan sun Farka daga wannan baccin was da yawa basu iya tuna ma sunyi Amma zasu tashi da cowon jiki da raunuka na faduwa ko ciccije Baki da harshe da sukayi lokacin sezure din har zuwa lokacin da zasu warware gaba daya.
Epilepsy kala kala ne. Akwai Wanda muka sani
Wanda mutum zai fadi yayi ta jijiga shi ake kira generalized epilepsy,akwai Wanda Kuma iya sashe daya na jikin shi ke jijigar Kila fuska ko hannun ko kafa,wani
Kuma Zaki ga zuru zai Yi ya kura ma wuri daya Ido kamar yy hooking anywhere dai ya danganta da sashen kwakwalwar da ke da, matsala tunda ita kanta kwakwalwar akwai sashe sashe da ke controlling kowane fanni na jiki.
Akwai aune aune da ake yi a gane sashen kwakwalwar da ke da matsala da Kuma abubuwa da suka haddasa seizure din
Akwai hoton kwakwalwa kamar su CT scan,MRI,
Akwai awon dake duba electric signal din(EEG). Ana Kuma auna jini a duba ko akwai infection kamar sankarau (meningitis) tetanus,rabies da sauran infection dai da ke iya taba kwakwalwa.
Ana Kuma auna jini a San adadin wasu sinadaral kamar calcium,zine, phosphates,vitamin D,B da Kuma parathyroid hormone da karancinsu a jiki ko Kuma yswansu idan ya wuce misali yake haddasa seizure din, Akasin shekarun baya da ake tunanin seizure shafar aljanu ce ynz an gano cewa ciwo ne na kwakwalwa da zaa iya controlling din shi da magunguna ko surgery.
Akwai kalolin maganin da ake sha ko ayi allura da dama da ake kira anticonvulsants da ake anfani da su Kuma da ake nasarar controlling din ciwon da su.
Wadanda aka samu gano kamar tumor, ko scar ko fannin kwakwalwar da ke da matsala akanyi surgery a Yanke sashen da ke da matsalar ana Kuma dacewa musamman idan kwararru ne masu kayan aiki na zamani su kayi.
Amma surgery na iya zuwa da complications misali bayan anyi ya kasance mutum Bai iya anfani da wani bangare na jikin shi ko ya samu paralysis gaba daya. Yawanci epilepsy na Yara Yana farawa ne dg zafin zazzabi Zaki ga da sun fara fever jikin su ya dau zafi sosai zasu fara convulsing da yawansu sukan warke daga lokacin da suka Kai 5-7yrs haka. Duk da akwai wasu dalilan sake haifar da ita, kamar mummunar faduwa ko buguwa a kai.
Masu epilepsy na fama da tsangwama daga wajen mutane Wanda rashin sanin ainahin ciwon ke kawowa.
Akwai side effects na magunguna da suke affecting learning da behavioral abilities na musamman yaran, so wannan shine cikakken bayanin”.
[27/09, 8:42 am] +234 703 451 7171: “HUGUMA”
*_TABARMAR KASHI
Book 02 Page 35
Shuru sãahar tayi tana gyada kai, idanunta dauke da qwalla,tausayin masu ciwon yana ratsata
“Surgery shine best hanya nake tunani da fadeela zata rabu da ciwonta,saboda kamar nata ciwon hakan ya nuna a yadda naji daga bakin nadeeya,hajiya qarama ta gara iza wutar ba za’a tabata ba,ba za’a yi mata aiki ba….yanzu kuwa lokaci yayi,ko tanaso ko bataso” sãahar ta fada with confidence.
“Bestie,please nan da sati daya ki bincika min best asibiti a kowacce qasa yake da zasu iya yiwa fadeela aiki, zanji da komai,ko sajjad banaso ya sani sai an gama” kai afifa ta mirgina
“Anya bestie?,bakya gudun faruwar komai?” Kai ta girgiza
“‘Na yarda da Allah, kuma nayi imanin bazai tozarta ni ba,kyakkyawar niyya sa tsarkin zuciya shine a gaba da komai” ta qarasa fada tana daukar wayarta, ta bude calendar na period dinta don ta duba kwana nawa ya rage, saboda ciwo da taji mararta tana mata kadan kadan. Qatoton circle ta gani tare da manyan rubutun
OVULATION DAY,sai ta sauke wayar tana dan yatsina fuska
“‘Kina experiencing wani pain ne?” Kunyar afifa kadan tadan kamata,saita kau da kai tana girgizawa
“Na sha magani” murmushi afifan tayi, qasan ranta tana jin dadi da hakan ta faru, tana kuma sake ganin kima da martabar toufeeg, don wanna abun da yayi a wajenta ya tabbatar mata yasan abinda yakeyi,kuma shi ba shashasha bane,hakanan ya tabbatar mata cikakken namili ne da tunaninsa ya saba da na diya mace.
********Kamar ko yaushe,qarfe takwas saura minti biyar ta kammala shirinta,har ta fiddo mayafi zata yafa ta tuna da hijaban da ya aiko nadeeya ta kawo mata guda goma sha biyar a jiya. Tun ranar da su afifa suka tafi tunda ta rakasu bata koma sashen nata ba,tayi zamanta a sassansu,kwanaki biyu yau kenan ko fuskarta bata sake bari ya gani ba,ko hijaban ma sai nadeeya taga ta shigo mata dasu
“‘Inji yaa moha, ki fara using nasu on Monday” tayi maganar tana hadiye dariya. Da kallo ta bita,nadeeya da afifa sun hade kai,sai suyita mata magana suna boye dariya,sun maidata kamar wata ‘yar tsanar wasansu,amma taci alwashi itama duk ranar data kamasu ba zasuji da dadi ba.
Qaramin tsaki ta ja, batasan meye nufinsa da yin hakan ba,zama tayi ta zazzagesu,ta kuma cire color din da zai shiga da atamfar jikinta,ta qarasa gaban madubi ta saka tana daure igiyar kai data hannun hijabin. Lokacin fadeela ta shigo wadda ta barta ne tana qarasa yin breakfast a dining.
“Anty na gama”
“That’s good girl,oya let’s go” ta fada tana goya school bag din fadeelan a bayanta kamar yadda suka saba.
Tun daga nesa taga parking space din da yake cin motocin nasa wayam ba kowa, ba kamar yadda suka saba ba,a safiya irin wannan gurin zaka sameshi jere da motocinsa da kuma su jibril suna tsaye suna jiran garasowarsu. Yau din shi daya ta hanga,tsaye jikin BMW dinsa fara sol, wadda a wancan satin ta iso,sai daukan idanu takeyi tana tabbatarwa da me kallonta tsadar da take da ita.