TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Kada ka sake tabani,zan iya taimakon kaina” daga wannan ta fara takawa zuwa cikin gidan kai tsaye hannunta riqe da dankwalinta daya zame. Binta yayi da kallo cike da mamaki,wanne irin taurin kaine da ita?,tana tafe tana layi amma duk da haka bata fasa tafiya ba,normally yana da wani irin tausayi ga mara lafiya. Dab da zata shiga parlor din muryar Joseph ta qara tashi da alama suna hira ne shi da jacob cikin dariya da kakaci,sai a sannan ya tuna suna falon,kanta kuma babu dankwali,kuma a haka zata ratsa ta tsakaninsu ya tabbatar,wannan tunanin ya sanyashi daga qafa don ya risketa ya tsaidata,saidai tun kafin ya isa tuni ta shige abinta.
Sanda ta shigo din da kallo Joseph ya dan bita dashi,kallo daya yayi qas da kansa yana ci gaba da mopping din da yakeyi,lokacin da yake yunqurin dauke dubansa daga kanta dai dai lokacin toufeeq din ke shigowa. Cak ya tsaya yana zura hannuwansa a aljihun wandonsa tare da hadiye wani irin yawu. Haka kawai yaji ransa yayi mugun baci.
“Joseph” yayi kiran sunansa da wata murya me kaushi,cikin rawar jiki ya amsa ya kuma ajjiye mopping stick din ya qaraso da sauri ya zube a gabansa. Fada sosai ya shiga zubawa cikin bacin rai,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Daga Joseph har jacob tsuru tsuru sukayi,don sautin fadan nasa ne ya fiddo Jacob daga kitchen shima,at last yace
“Get out from here,you All” ba wanda ya sake cewa komai sai ajjiye kayan aikinsu da sukayi suka jera suka fice,su duka suna mamakin abinda ya bata ransa,iya tsahon zamansu dashi bai taba musu fada irin haka ba.
Wayarsa ya fidda daga aljihu ransa a bace,ta yaya zata ratsa tsakanin masu aikinsa a haka?,tsabar taurin kai ne kawai da kafiya irin nata,kuma zaiyi maganin wannan taurin kan nata surely. Har ya fara kiran Dr anwar,sai ya katse ya koma kiran Dr raheema,bugu uku kacal ta daga
“Ki sameni gida yanzu” abinda ya fada kenan ya gintse kiran. A hankali ya koma saman hannun kujera ya zauna,har yanzu yana jin zuciyarsa na masa quna,ya daga hannunsa ya kalli tsadajjen agogon dake maqale a lafiyayyar fatarsa. Yana da schedules da yawa yau dinma,akwai baqin da yasa aka ajjiye a tahir guest palace amma cikin jikinsa yakejin kamar bazai samu zuwa ba. Kamar kuwa jibril yasan abinda yake saqawa sai ga shigowar kiransa,ya kalli wayar da kyawawan fararen qwayoyin idanunsa,sai ya daga wayar ya saka a kunnensa
“Sir,i think kamar ka manta,we have an important with the guest who is staying at the guest house,sunce morning flight zasu bi gobe,seven pm dot,They asked me to tell you, if you don’t mind, the conversation should be over tonight” kai ya gyada
“Alright,kazo ka daukeni after one hour,banason rakiyar kowa”
“Yes sir” jibril ya amsa masa cikin girmamawa. Yana sauke wayar dr raheema na shigowa. Kai tsaye yayi mata nuni da hallway na dakunansu. Nauyi taji sosai,saboda bata taba yin nan gefan ba hasalima part din nasa yaune karon farko data fara shigowa,so sai abun yayi mata kwarjini da yawa.
“Don’t mind,ki shiga tana ciki” ya furta calmly
“Okay madam ce?” Tayi tambayar tana murmushi,kai ya gyada mata,sai ta gyara box din kayan aikinta tana cewa
“It’s better to let her know first sir kafin na shiga” kansa ya daga a hankali yana duban hanyar,ya yadda da idea dinta,don haka ya miqe a nutse yana maida wayarsa aljihu ya nufi hanyar.
Tana jingine da fuskar gadon idanunta a lumshe,zara zaran gashin idonta sun yiwa idanun nata rumfa da kyau,sau daya ta bude ido ta kalleshi ta mayar ta kulle,ya qarasa kanta ya tsaya yana dauke dubansa daga kanta
“Ki shirya ga dr nan zata shigo,ki gaya mata matsalarki,i don’t want rudeness” ya qarasa maganar yana turawa Dr raheema gajeran tex akan ta shigo. Bude idanun nata ta sakeyi a hankali ta sauke a kansa,me ruwansa da rashin lafiyarya da zai kira mata likita,saboda tsabar girman kai da izza kuma yazo yana kafa mata dokoki kaman ita ta buqaci ganin likitan?.
Tare da nadeeya sukayo sallama da fadeela duka a tare.
“Oh sannu anty N” nadeeya ta fada cikin nutsuwa,tana gudun kada tayi misbehaving yanzu a sendata waje. Qaramin murmushin data fusgo da qyar ta sakewa nadeeya tana gyada kai,ta miqa hannu a hankali ta sanya hannun fadeela da duk take a dame cikin nata,ta tabbatar lokacin dawowarsu baiyi ba,tayi yaqinin fadeela ce taqi sakewa,ta gayawa nadeeya ita kuma ta tattarota suka dawo.
“Sunnu madam” Dr raheema ta fada cikin murmushi tana sake yaba kyan da sãahar din ke dashi
“Dama MT JARMA din sai mata irinku” ta fada a ranta tana murmushin gulmarsu da tayi.
“Yanzu ukhtie fadeela ta yaya za’a duba maman naki ehnn?” Dr raheema ta fada tana murmushi ganin yadda ta kafa ta tsare ta nannade hannun sãahar da kyau
“Karkiyi mata allura please dr” ta fada a shagwabe,dariya tadan saki
“Ah…..wai da allurar zanyi mata fa,kika sani ko qani maman naki zata baki ko bakiso?” Wani tsalle tayi hadi da sakin hannun sãahar da maganar Dr din ta sanyata kasa bude ido. Tuni fadeela ta maqale toufeeq tana dariya
“Da gaske daddy?,wai nima anty N zata haifo min qani?,daddy nima na daina wasa da teddy sai da qanina?” Gaba daya nauyi ya saukar masa,yasan halin Dr raheema ba wai tun yau ba,tana da mugun barkwanci da kuma kirki,amma haka kawai saita hada masa gwarama,ta qala masa abinda bai taba attempting aikatawa ba harda su wani ciki?
“Fadeeeeela” toufeeq yayi kiranta ganin ta dauki abun serious. Yadda yayi kiran nata ya sanya ta nutsu tana dubansa
“Ki nutsu za’a duba mara lafiya. Nadeeya come and take her,ku zauna a waje ku jira” ya fada yana wani basarwa saboda kallon da yaga nadeeyan tana masa,haka kawai zata janyo yara su rainashi,yadda yaga nadeeyan tana kallonsa itama tayi believing ne da abinda Dr raheema ta fada bisa alama.
“Kodai anyi abunne?” Ta fada qasa qasa tana duban idanun sãahar bayan ficewarsu nadeeya
“Da wa?” Sãahar din ta fada kai tsaye tana duban dr raheema din,don ko dazun da tayi zancan ciki bacin rai kawai ta dasa mata. Tambayar sai ta saka Dr raheema murmushi,tana zaton kunya kawai sãahar din takeji. Ga toufeeq kuwa ya fahimci sarai ma’anar amsar data bawa dr raheema din sai yayi folding hannayensa a qirjinsa yana duban fuskarta,zarginsa ya saje tabbata sanda ta juya kadan ta jefa masa wani kallo
“Ba maza ai a gidan” ta fada qasa qasa hankali kwance bayan ta dauke kai daga dubansa ta maida idonta ta lumshe. Dr raheema batace komai ba,ta bawa ranta zafin zazzabin daya fara hawa mata ne.
A nutse ta gama dubata,sai ta fidda PT strip
“Ko zaki kawomin fitzarinki zanyi pregnancy test,saboda nasan magungunan da zan rubuta miki” kai tadan juya kadan
“Ki rubuta maganin directly kawai” murmushi ta sakeyi mata kamar yadda yake nuna al’adarta ne hakan
“Sorry madam,indai matar aure ne dole tayi gwajin kafin karbar magani saboda gudun matsala ga qaramin cikin da ba’a san dashi ba” siriryar iskar ta furzar daga bakinta,itakam ta gaji da zancan cikin nan da taketa jawo mata shi d baki a gaban wannan dan izzar wanda ko a yanzun yana tsaye qyam kamar tsohon soja yana danne danne a wayarsa,sai ka rantse da Allah babu shi a dakin kwata kwata,ko kuma baisan abinda yake faruwa ba
“Am on my period ” ta fada qasa qasa cikin jin takaicin tona asirin kanta da tayi da bakinta. Duk yadd tayi qasan da muryarta sai da yaji din, sauke wayarsa yayi saboda shigowar kiran jibril