TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Good morning yaa moha”
“Morning” ya amsa mata a taqaice yana duban trays din
“Kayan dasu banaan sukayi breakfast ne na debo,kasan sun wuce”
“Ban tambaya ba.. ki wuce ki taho da
ita, kusameni a nan zamu shiga tare” ya fada cikin basarwar nan tasa. Dadi ne ya Kama nadeeya,dama tun dazun take jiran shigowarsu,don ta matsu taga aunty N din,fadeela kuwa baccin daya debeta da safen shi ya kawo sauqin rigimarta,maji ta hana kowa zuwako kai abinci ma tace a gyalesu tunda akwai cook a sassan. Cikin azama ta qwalawa daya daga cikin masu aikin gidan kira,ta qaraso ta jingina mata trays din tayi gaba
“Idan kuka dade ranki ne zai baci” ta jiyo muryarsa, saita gyada kai tana qara hanzari
kadan.
Muryar nadeeya da taji tana sallama bayan knocking din da take mata ya sanyata miqewa tana murmushi,ta isa bakin qofar ta bude.
Rungume juna kawai sukayi,fuskar nadeeya cike da fara’a kamar wadda ta shekara bata ga sãahar din ba
“Ina faddee na?”
“Tayi baccin gajiya,tun da safe tafarka tana rigimar zuwa gurinki,amma maji tace ba yanzu ba,babu wanda zai tasheku” murmushi säahar ta saki tana in nauyi da kunyar majin tun kafin ma su hadu
“Yaa moha ne yace muje nayi miki jangora,yana jiranki a bakin part dinmu” nadeeya ta fadi tana qarewa sãahar kallo.
Wani sassanyan kyau da tayi ita kanta yaja hankalinta ina ga yaayanta? tayi imanin nan kusa za’a yi barin wannan jan ajin da kamewar tasa tayi fata fata,fatanta dai daya lah ya kawo komai da sauqi,saboda ta sani shi din bai iya
Kama komai da sauqi ba.
Tare suka jera nadeeya din tana ta mata hira,kamar yadda suka saba a baya ba amsa sai murmushinta me sanyin nan da yake sake qawata fuskarta.
Tun daga nesa inda yake tsaye ya hangi tahowarsu bayan ya daga kai daga latsa wayarsa da yakeyi. A hankali ya zare idanunsa daga kansu ya mayar ga hadiman gidan,wanda kusan duka maza ne suna kai kawo kowa yana gudanar da nasa aikin.
Qwayar idanunsa ya juya kadan ya rufeta sannan ya bude a lokaci guda yana gogarin controlling kansa game da mayafin jikinta.
Cikin jininsa qin mayafin yake,tun daga lokacin da ya fara ganinsa jikin nadeeya ya hanata amfani dashi,bata kuma sake ba.
Iska yaja sosai yana fesarwa hadi da dauke kansa yana kallon gefansa,so yake ya lalubi zuciyarsa yayi kaya control,meye nashi na shiga sha’anin shigar da duk taga dana ta zabawa kanta? nadeeya qanwarsa ce,jininsa ce wannan kuma fa?.
“‘Matarka ce” yaji ana bashi amsa daga can wasan zuciyarsa. Kai ua girgiza a hankali
•ya juya da kansa yana sake maidawa kansu sanda suke gab da qarasowa inda yake.
Sarqewa idanunsu sukayi cikin na
Juna, kallon second biyu rak suka yiwa juna kiwa ya janye idonsa yana jun haushin kansa, toufeeq kam kasa jurewa yayi sai da ya saki qaramin tsaki yana jin hausnin abinda ya sake maidashi ga kallon fuskarta da tayi wani haske,skin dinta data dauki gyara fiye da zato ta hadu da hasken ranar safiyar,ranar da bata kammala budewa ba saboda gajimare daketa haduwa yana alamta haduwar hadari, irin hadarin farko farkon damina.
Suna isowa nadeeya bata tsaya jiran komai ba ta zame ta wuce ta barsu a gurin.
Shuru ya ratsa gurin,kowa a cikinsu yana ji da kansa,yana jin kuma faduwa ce ya yiwa dan uwansa magana. Iska ya sake furzarwa yana son abinda ya tsaya masa a maqoshi ya wuce,kamar bazai motsa ba kafin daga bisani ya fara takawa a hankali zuwa ciki. Bayansa ta gallawa harara,ta motsa bakinta zata ia tsaki amma saita hadiye abunta saboda tunawa da tayi da abinda ya faru da ita company sanadin tsakin,ta murguda bakinta wai duk ko zata huce sannan ta bishi a baya tana gunaguni gasa gasa
“Girman kai,fadin rai,bagin rai duk mutum shi daya” ta furta can qasan zuciyarta ba tare data bari ya fito sarari ba.
Tun tana hararar bavan nasa har taji kamar idanunta na neman juyewa,a hankali ta janye idanunta,tana dan rufesu kadan sannan ta sake budesu,kai tsaye saman baqar sumarsa da a kullum take cikin gyara ta sauka,ta kwanta sosai da wani irin gyara daya dace da shigarsa ta wani creamy color din yadi na maza,mara nauyi wanda kana iya hangen vest din jikinsa ta zallar cotton fara qar gar da ita.
Yadda yake dauke gafarsa da saukewa kadai zai nuna maka yawan kuzari da baiwar lafiya da Allah ya bashi,wani irin taku me cakude da
‘yar sassarfa kadan wadda take sanyawa yake danyi mata nisa,har sai tadan qara nata saurin kadan. Shi kansa takun gani takeyi kamar akwai izza da gasaita a cikinsa
“Aikin kawai” ta furta tare da jan tsaki. A wannan karon tsakin nata ya bayyana,sai taga ya rage adadin takun nasa da yakeyi.
Gabanta ya fadi,ta dora zara zaran yatsuntsa da suka sha lallae saman bakinta tana dan fidda idanunta waje,ba tare da ya waiwayo ba sai taga yaci gaba da tafiyarsa,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya yaci gaba da bin bayansa tana kame kallonta daqa kansa,kada wani tsautsayin yasa ta sake wani abun da dukkansu shi da ita zasu raba hali gaban suruka.
Da sallama a bakinsa ya tura gofar dakin maii,ita da ‘var uwarta wassila suka hada baki wajen amsawa. Fuskar maji din fal da murmushi,wani farinciki yana sauka a zuciyarta. Ganinsu kadai tare ya haifar mata da farinciki me tarin yawa,tana ii a jikinta sãahar din itace addu’ar data jima tana yiwa toufeeq wajen roqa masa ubangiji yayi masa musaya mafi alkhairi da zai wanke dukkan quncin da ya samu kansa a ciki
“Qaraso mana ibnaty” maii dake duban sãahar cikin kulawa da murmushi ta fada. Tsananin kunya ce ta dabaibayeta,ta tako a hankali ta qaraso gabanta,sannan ta zame saman gwiwoyinta tana fadin
“Barka da asuba” gogarin dagota maji keyi amma sãahar din ta kasa sakewa bari ta mige kamar yadda maji keda buqata,dole ta barta fuskarta da murmushi tana dubanta tace
“Barkanmu ibnaty,ya kwanan bagon waje?”
“Alhamdulillah” ta amsa da gyar tana wasa da yatsunta
“Allah yayi muku albarka,yasa albarka a tarayyarku” maji ta fadi. Kasa amsawa tayi,sai daga kanta da tayi a hankali tana gaida wassila wadda suke magana qasa qasa da toufeeq,bata kuma iya jin ainihin abinda suke fadi. Itama kamar maji din,tana da matuqar kirki,hakanan ta karanci kamar akwai kyakkyawar mu’amala tsakaninta da toufeeq.
Qasa qasa maji ke janta da hira,saidai sam ta kasa sakewa da ita,surukuta sosai takeji,a gefe guda wanzuwar sa a waien yasa take jinta gaba daya a takure,saboda basu saba zama a muhalli guda ita da shi ba har irin haka. Duk da ta gefen idanunta tana lura da yadda ya karkata hankalinsa ga wayarsa,abinda ta karanta kwata kwata babu sabo ko shaquwa me yawa tsakaninsa da mahaifliyarsa. Inda itace tayi missing maama haka,ta tabbatar zuwa yanzu tana magale da ita.
Cikin harshen larabci wassila tayi magana da maji sannan ta juya ta yiwa toufeeq shima magana,ta cewa da saahar cikin gurbatacciyar hausarta
“Zanje na dawo surukata” sai ta gyada kai caking jin nauyin sunan data kirata dashi. Zata fita baaba ramatu na shigowa, fuskarta itama yalwace da fara’a tayi musu barka da fitowa suka kuma gaisa
“Ki hado mana breakfast din duka tare dasu,a nan zamuci” maji ta bada umarni, cikin girmamawa baaba ramatu ta juya ta fice.
Ba jimawa ta shigo ita da masu taimaka mata dauke da manyan trays guda uku,ta ajjiye a gabansu ta juya ta fita. Wayar hannunta maii ta ajjiye bayan ta kashe,ta jawo dukka trays din tsakaninsu ta dubi sãahar