TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

Mamaki ne qwarai ya kama sãahar, ta yaya za’a yi kira a wayar office office din da ba nata ba amma farat daya a kama sunanta?

“Eh itace”

“Good,na buga dai dai kenan…..kina magana da
Ameesha,ex_wife din mijinki muhammad
toufeeq,maama ga FADEELA” sosai ta gyara tsaiwarta ba tare da tace komai ba

” Zuwa yanzu nasan fes kin fahimci wacece ni din”

“Me kike bugata” garamar dariya ta saki

“Naji dadi dana sameki me saurin fahimta,hakan na nunamin bazan sha wahalar fahimtar dake lokaci yayi na dawowata gida na ba”

“Dashi ya kamata ku garasa wanna maganar” tà gintse ameesha din daga abinda ta kira da soki burtsu a waienta. Waiwayawa tayi gareshi bayan ta dauke wayar daga kunnenta suka hada ido dashi, idanunsa zube fes akan fuskarta yana son ya karanci wani abu. Bata bashi dama ba don dauke kanta tayi, ta qarasa gabansa ta rangwafa daga saman table din tana gyara masa zaman wayar a gabansa,wannan ya baiwa ragowar gashin kanta damar qarasa warwarewa,iskar dake shigowa daga window ta buso masa dukkan gamshin dake magale a jikinsa harda tsarabar shafar gefan fuskarsa. Ido ya lumshe a hankali yana jin yadda zuciyarsa take bada wani sautin bugu, sanda zai bude idon harta ja da baya tana sanya takalmanta ba tare data dubeshi ba tace

“‘Baguwa keson magana da kai” bata tsaya sauraronsa ba ta dauki hand bag dinta da wayarta ta fita daga office din.

Kamar zaman jiran ganin me shiga da fita daga office din saima tayi tana fitowa suna hada ido,saita dauke kai tana nufar living room dinsa dake cikin office din. Ta dora hannunta zata murda handle din living room din sai aka budo ainihin gofar da zata sadaka da sashen saima. Sai ta waiwaya tana duban qofar.

Sanye take da wata gown na Vintage clothing, saman kanta lullube da siririn scarf data nadeshi daga kanta zuwa wuyanta kawai,fiye da rabin fuskarta sun glasses ne ya mamayeshi, sai wani rufaffen takalmi me tudu data sanyawa qafarta, daya hannun na maqale da hand bag yar mitsil, daya hannun kuma wani foldable basket ne da aka shirya qananun warmer’s masu kyau a ciki. MEENAL YA’AQOUB AJI kenan,sananniya ga duk me ta’ ammali da kafofin sada zumunta,wanann dalilin ya sanya saima miqewa tsaye cak suna kallon kallon a tsakaninsu. Koda batace ba tasan gurin toufeeq tazo,don duk wanda ya santa,yasan ita daya ce tallin tal dake wallafa hotunansa kusan koda yaushe saman shafukanta na sada zumunta. Batayi mata kallo na biyu ba ta murda gofar room din ta shige ta barsu suna kallon kallo tsakaninta da saima.

“Madam ina zuwa haka?” Saima ta tambayi meenal cikin gatse. Dawowa tayi da baya tayi qasa da glasses dinta ta qarewa saima kallo,sai ta saki wata dariyar rainin wayo

“Jealousy”‘ ta fada cikin nishadi sai kuma ta dora

“Zanyi mamaki gwarai idan kikace wai baki sanni ba…
Meenal ta fada cikin izza da jin cewa ta kai ta kawo ta kuma shirya gogawa da kowa akan TOUFEEQ,tasan da saima already tasan kuma zaman me takeyi a gurin…
[22/09, 10:23 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 26

.. Anyways, nazo wajen masoyina ne kuma mijina” daga haka ta juya ta nufi office din kai tsaye. Zallar mamaki ya hana saima cewa komai,sai kallon zallar mamakin da ta bita dashi. A cikinsu wace ainihin matar tasa?,ko mata biyu ya aure lokaci guda basu sani ba?.
A nutse take takawa cikin living room din dake tsare da sofas masu tsada da aka sake zubawa,sofas din da kake da ikon lanqwasa su duk shape din da kaso,daga kujera me qaramin table a hannunsa zuwa matsakaicin gado tare da pillows. Jakar hannunta ta ajiye saman sofa din a hankali. Kalaman ameesha ne suka fara dawo mata fes cikin qwaqwalwarta. Siririn tsaki taja gana jin zafi a zuciyarta da matar ta kasance mahaifiya ga fadeela, juma’ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta, kuma ita din ba qanqanuwar yarinya bace, dukkan alamu sun nuna zaiyi wahala a samu karamci kamun kai da sanin ya kamata daga gurin matar, kalaman bakinta kawai sun gama gayawa säahar wacace ita din. Sake jan tsaki tayi tana nufar gofar da
aka rubuta Toilet daga samanta da wani irin rubutu
ruwan azurfa. Tura bandakin tayi ta shiga tana binsa da
kallo komai kar kamar ka zuba abinci a ciki kaci. Fitsari
tayi ta daura alwala sannan ta fito ta tayar da salla. Ko’
bayan ta idar zamanta tayi saman lallausar abun sallar
dake ajjiye har guda uku a wajen. Tana azkar kadan
kadan tana tunanin abinda zata ci.

Fuskar haseena dake shigowa da kwanukan abinci
ne ta dawo mata,cikin shigarta dake nuna halittar
sirantakar da Allah yayi mata tako ina wanda wala’alla ita
bata ganin hakan. Gefe daya kuma fuskar saima ta
fado, duk yadda takeson kore tunanin komai daga ranta
amma sai ta gaza aiwatar da hakan?. Wai meye tattare da shi da sauran maza basu dashi suke wannan parade
din a kansa,kamar qarar wayarta shine amsar
tambayarta sai kira ya shigo mata,wanda shine ya zama
silar yankewar tunaninta ta dauki wayar tana dubawa.
Bestie afifa ce, saita saki murmushi sannan kuma ta tura
baki gaba,tabbas sai ta fanshe shakulaton bangaron da
afifan tayi da ita ta daga wayar ta koma saman abun sallar.

“bestie bana yi, bestie kinci amanata” sãahar ta fada
tana harara wayar tamkar dai afifa na wajen

“Don Allah bestie kiyi haquri, wallahi ban taba
experiencing irin wannan yanayin ba a rayuwata” afifa ta

fada da muryarta data gama komawa me sanyi. Ta fahimci maganar afifan, don haka ta sanya hannuita toshe bakinta saboda dariyar da take cinta

“Na miki uzuri bestie, Allah ya bada lafiya”

“Wai Allah bestie, naga rayuwa,sai yau na samu space da hayatee ya taho company” baki sãahar ta tabe, ita kwata kwata wadan nan sabgogin basa burgeta ko kusa ko alama,kafin tace wani abu afifa tace

“Amma bestie lafiyanki qalau kuwa? ,kina cikin hankalinki kike shirin sakarwa mata mijinki?,wannan na ciki wannan ta shigo?” Maganar tadan baiwa sãahar mamaki

“Kamar yaaya? dama na aureshi ne don na kula sa sabgoginsa ko kuma na kula da diyarsa?” Ta jefawa afifa tambayar. Goshinta ta dafe tana lumshe ido, sãahar dai bata canza ba?,a kwanakin d sukayi tare ta dauka komai ya fara canzawa dangane da junansu a zukatansu

“Saahaaarrrr……. please ya kamata ki koma cikin hankalinki,hayatee yazo office dinsa ya taras da hakan, saboda yana kishinsa yana kishinki kuma yana kishina yasa ya gayamin….i was so shocked…
…nasan

ba haka bestie na take ba, aure ai ba abun wasa bane

bestie, ko banza igiya ce me girma a tsakaninku…
…moha
ba normal irin gama garin maza bane,wannan abun da kike na shakulaton bangaro ba komai zai haifar miki ba sai d’a maras ido, ki tsaya kawai kiyi abinda ya kamata ki manta da komai” baki sãahar ta tabe

“Yaushe kika koma me bada shawari?, kinje kin kurbi giyar aure ko?,hmmm sannu farin shiga,to na gode da shawara,amma ni ba ruwana da abinda ya shafi rayuwarsa,wannan shi ya zabarwa kansa,ya auri mata dubu ma ya kula million a yau duka shi yaso, zan wuce gida yanzu lokacin tashi ya kusa,idan na isa zamuyi waya,inason mu tattauna akan wani abu daya fara tunani a kai”

“Allah yasa maji ta aura masa uku tsala tsala larabawan
Algeria”

“And so what!” Ta fada da lafazin da ya sanya fifa shegewa da dariya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected