TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“She’s not brave enough,ba zata iya daukanki ba” ya fada muryarsa tana dan sargewa wanda shi kansa baisan da hakan ba. Itakam fadeela da batasan dawar garin ba dariya takeyi tana sake magale säahar
“Anty N,abby na ya fiki qarfi, amma zamu hada qarfinmu waje daya muma ko?” Kai ta gyada mata a sanyaye tana jin qafafunta babu qwari sam. Tsaiwa yayi kawai a wajen yana duban fuskarta,yadda lokaci daya hankalinta ya tashi fuskarta kuma cakude da bacin rai kadan. Kasa motsawa yayi shima yana qoqarin controlling kansa kafin yakai ga takawa yabar wajen,jikinsa a sanyaye ya ja da baya ya jingina da kitchen cabinet din yana sake binta da kallo sanda take rige da hannun fadeela bayan ta maida hijabinta jikinta.
“Ungo wannan ki fara sha kafin kiyi wanka,kizo kici abinci na gama” sãahar tace da fadeela tana bata drinking glass din. Harda tsallenta, ta dawo gurin toufeeq bayan zuga
“Yummy abby sha kail” ta furta tana miga masa.
Hannunta ya dafe yana girgiza kai,ta fahimci me yakeson cewa saita maqale wuya
“Please mana abby” a nutse ya durqusa ya sanya straw din a bakinsa ya zuqa. Har cikin kwanyarsa dadi da gardin fruit dana madarar ya ratsa masa,ya lumshe idonsa yana jin smoothie din yayi masa matuqa,saidai kafin ya sake sha fadeela ta janye abinta ta kafa a baki.
Su suka fara fita a kitchen din yabi warmers din da kallo daya tabbatar abinci ne a ciki,ya shafi cikinsa yana jin yunwa tana taso masa, tunda jacob yaje gida yake wahalar abinci,tun asali mutum ne shi da bakowanne abinci yake iya ci daga hannun kowa ba, gidan cike yake da masu girki da kuma nau’in abinci kala kala amma bai iya ci ba, da abincin jacob kadai ya aminta. Ba mai yawan ciye ciye bane, amma kuma baya wasa da cikinsa ta fannin abinci, idan ya tashi zaiyi masa ci me kyau,daga nan kuma sai lokaci na gaba. Da qyar ya shawo kansa sannan ya fita a kitchen din shima.
Sassan nasa babu kowa kamar ko yaushe,bedroom dinsa ya wuce,ya soma zare kayan jikinsa cikin wata muguwar kasala,ya zauna yana zare takalmansa idanunsa suka sauka aka robar maganin.
Hannu yasa ya sake daukota yana juyawa,sai ya maida ya miqe yana dauko system dinsa daga inda ya ajiye ya kunnata,akwai result da zai karba yau game da maganin daga gurin Dr anwar,don haka yabar system din tana daidaita ya wuce toilet don yayi wanka kafin ya fito.
“HUGUMA*
‘_TABARMAR KASHI*
Book 02Page 29
Sai da ya gama shiryawa tsaf cikin wasu lausasan pyjamas bagaqe a yau amadadin farare da yafi amfani dasu komai ya zauna luf a jikinsa,yaja stool ya zauna vana duba system dinsa.
Dukka hankalinsa va bayar akan bayanan da Dr anwar ya turo masa. Lokaci daya yaji wani gumi yana tsatstsafo masa,yasa hannunsa a tausashe ya share yana dungule hannunsa ya rufe bakinsa yana tsurawa system din ido
“‘Yaya akayi maganin ya kasance daga hannun haliva qarama? me yasa maganin da bai kasance na lalurar fadeelan ba amma take shansa? me hakan ke nufi?” Ya viwa kansa tambayar yana jin hankalinsa yana tashi
“Take it easy” wata zuciyar ta gaya masa
“‘Kayi bincike wisely” aka sake nanata masa. Miqewa yayi yana fita a bedroom din nasa a hankali, ya ciro wayarsa da ya bari a parlor ya fara kiran layin nadeeya. Bugu daya ta daga
“Yaa moha”
“Me sunan matar nan baga wata gajeriya me jiki dake aiki a sassan momy?” Dan shuru kadan nadeeya tayi sannan tace
“Ko adama?” Kai ya gyada
“Yes, kiyimin kiranta, amma banason kowa yasan na nemeta”
“To yaaya” ta fadi tana ajiye wayar, saita dubi su sãahar wanda suke zaune zasu fara cin abinci
“Ina zuwa AUNTY N” kai ta gyada mata,saita koma daki ta dauki mayafinta ta fice.
Tun daga yadda ta shiga parlor din zakasan a mugun razane take,ko ina na jikinta rawa yakeyi,gumi kuwa ya gama jiga mata jiki sharkaf. Yau ta shiga masifar da me fiddata sai Allah, dazun nan hajiyan ta gama yi mata kakkausar jan kunne kamar yadda ta saba a duk lokacin da aka karbo maganin, saidai kuma jan kunnen yau din yafi na kullum, kamar tasan abinda ya faru a hanyarta na kawo mata maganin. Da hannu ya yiwa nadeeya nuni akan ta tafi,ba musu ta juya,cikin zuciyarta tana taya adama alhini,ko wanne tsautsayi ne yasa ta shiga gonar toufeeq din? wanne irin laifi tayi masa haka?.
Tun kafin yace ta zauna gafafunta suka kasa daukarta, saita sulale tayi zaman dirshan a gurin. Kallo daya yayi mata ta fashe da kuka, tama mance da wani jan kunne na hajiya qaraman
“Wallahi bansan komai a kai ba indai batun magungunan ne” idanunsa kawai ya zuba mata yana mamakin rudewar da tayi. Sake debo rantsuwa tayi
“Na rantse da ikon Allah bansan komai ba”
“Tun yaushe ake kawo maganin?” Ya jefa mata tambayar
Shekara biyu…shekara biyu a cikin ta uku* ta bashi
amse kowanne sashe na jinta yana kakkarwa. Wani irin zafi idanunsa yaji sun fara yi masa, abinda zuciyarsa ke hasaso masa har bayaso sukai ga kwanyarsa bare ta sauya masa su ga dayan sashen na zuciyar tasa
*ki hada kayanki gaba daya,na sallameki daga aiki a gidan nan” abindia ya fada kenan. Faduwa tayi a gurin tana hurwa tana kuka sosai, saboda tasan muddin tabar aiki a gidan asirinta ya tonu,mutane masu yawan gaske ne suke neman damar yin aiki a gidan amma basu samu ba
Tsawa ya buga mata wanda ta sanya ba shiri ta tattara zaninta ta fice tana kuka. Shuru yayi yana maida jikinsa ga kujerar idanunsa a lumshe
“To maganin meye?” Tambayar da Dr anwar dinma bai bashi amsa ba, yace masa baida alaqa sam da ciwon fadeelan, suna kuma ci gaba da bincike.
“Wanne magani kenan ake bata yanxu?” Tambayar da tazo kansa kenan,ya kuma miqe a nutse ya sanya flip flops slippers dinsa yana baro sashen.
Tuni ta gama cin nata abincin ita da fadeelan, nadeeya ce tayi saura,don haka suka barta a falon suka wuce daki don ta shiryata ta bata maganinta tasha. Toilet ta kaita, kamar ko yaushe yanzu ta fara canza pattern na wankanta, zata hada mata kayan wankan gaba daya,tayi mata tsarki ta wanke mata bayanta da sauran inda hannunta bazai kai ba,sauran kuma saita tsaya tana kallonta tayi da kanta, tanayi tana gyara mata har su kammala. Sanda yayi sallama dakin basuji shi ba,suna bandakin tanata tsokanar fadeelan saboda yau ta dage bayan nata ma zata wanke da kanta.
A nutse ya garasa shigowa,ya maida murfin qofar ya rufe, idanunsa suka sauka akan dressing table din fadeelan inda kayan baccinta maganin nata da sauran tarkacen kayan nata suke.
Kai tsaye ya dauki robar maganin yana dubawa,sak irin maganin da yasan yana siyowa da kudinsa va damgashi ga hajiva garama har na tsahon watanni shid,bayan wata shidan kuwa baya taba batan lissafi zai sake kawo wani na wata shidan. Bude robar yayi ya zazzago maganin. Shine asin da asin babu banbamci, sai ya maida murfin maganin ya rufe ya maidashi inda vake vana fadin
“Hasbunallahu wani’imal wakil” wane sashe na zuciyarsa kuma na tambayar sa,waye yake bata kudin siyan maganin?. Lokaci daya komai ya rikice masa,lissafi yaso qwace masa,ga hajiyan da wani magani sabanin wanda ake baiwa fadeelan, ita kuma gata da irin maganin fadeelan ba tare da yasan waye yake siya ba.
Komawa yayi ya zauna saman sofa bed,har ta gama wankan suka fito tana tsane mata gashinta da hoodie towel din data rataya mata saman kanta.