TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Yaji dadi da bai samu meenal ba a sassan,ya samu guri ya zauna yana gaidata
“Ka kusa fin garfina ai toufeeq” hajiya ta fada tana tara hawaye cikin idonta. Mamaki abun ya bashi qwarai
“Me kuma ya sake faruwa,i thought kun gama magana
da Dr ko akan komai?”
[22/09, 10:23 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI *
Book 02Page 27
“Amma toufeeq kamar ni?, meye amfanina a cikin gidan idan ban kula da fadeela ba” ido ya lumshe sannan ya bude,ya gaji gaba daya bayason wani daru
“Karki wani damu, tattaromin magungunan ki bani, ni zan ci gaba da kula da hakan” a bazata maganar tazo mata,har hakan yaso ya rudata amma ta daure
“Haka ma zaka ce dani toufeeq? yayi kyau shikenan, kaje kawai” ya dauka ya kawo qarshen maganar, amma sal ta sake cewa
“ya kuke ciki da meenal?,dazu ta dawo tana kuka,ta bata lokaci tana bada direction na abincin da za’a dafa maka,sai kuma naga da takai maka babu abinda ka taba a ciki,me yake faruwa?” Idanunsa yadan rufe kadan,a yadda ya fuskanci yanayinta ko meye zai fada mata a yanzun zata bata masa lokacine ta qara masa hayaqi akai, saidai duk da haka yana bugatar ya datse dabi’ar daukar abinci takai masa company,alhalin suna da kitchen, sannan kowanne kalar abinci yakeso yana daga office jibril zai iya masa order dinsa
“Mun fita da madam dauko fadeela daga school” idanu tadan bude da kyau tana kallonsa. Tunda suke dashi bata taba jin ranar da ya zarce daga office dauko fadeela makaranta ba sai yau,yau din kenan har hakan ta fara?, har yarinyar taci nasarar juyar masa da hanakali da sauya masa ra’ayi da tsari?,duk kuwa da tarin taurin kansa da kafiyarsa akan tsarinsa?, wanda ko ita ba kasafai takecin nasarar canzashi ba?. Bata gama wannan mamakin ba ta ganshi ya miqe sannan yace
“So please hajiya ki fahimtar da ita basai tayi wahalar kawomin ba,i will be alright, bazan rasa duk abinda nake bugata ba” mamaki ya hanata cewa komai,shi sam baima wani zurfafa dubanta ba bare ya gane ya dora mata
“Zan wuce ciki.da wuri nakeso na kwanta”
“Jacob baya nan,ko a kai maka dinner?” Ta sake garfin halin fada tana ritsashi da ido tare da son tabbatar da zarginta akan säahar . Hannu yasa ya shafi tattausar sumarsa
“No, ba damuwa,i will get something to eat” sai yayi mata sallama yana ficewa. Labiba da haseena, tabbas yana gab da yi musu mummunan warning din da ko sunansa sukaji zasu san nayi,yana musu kara da alkunya ne kawai saboda iyayensa, hajiya qarama da dr jarma,don kwata kwata baya saka mansura a lissafinsa.
Yana shirin fita a sashen adama na isowa, hankalinta yayi gaba sosai don haka bata lura da shi ba har sai da yayi dab da ita, cikin zafin nama ta kauce masa abinda ya sanya ta bugi bango ledar dake hannunta ta. yage,magungunan ciki suka zubo qasa. Cikin tsananin rudewa tare da tuna kakkausan gargadin da hajiyan tayi mata wajen kula da maganin har zuwa sanda zata kawo mata shi,sai ta sulale a gurin tana tattarosu tana zabga salati.
Kansa ya dauke yana ci gaba da tafiya. Har ya gota yá dawo da baya sakamakon wani tunani da ya darsu a ransa. Akwai masu aiki a gidaje kamar haka da suke ta’ammali da kayan maye qwayoyi ba tare da iyayen gidansu sun sani ba,wasu ma idan aka samu tsautsayi har su koyawa yaran gidan
“Ke.. zo nan” kiran da ya sanya hantar cikin adama juyawa,ta dawo da hanzari ta zube a gabansa
“Wadan nan magungunan fa?”
“Eh… na’am” ta fada a rude tana tuna gargadi na biyu data yi mata,kada ta nuna cewa maganin yana da alaqa da ita ko fadeela
“Uhmmnn” ya fadi yana tsuke fuskar nan tasa me sanya shakka da tsoro a zukatansu
“Ko kin fara shaye shayen muggan qwayoyi?” Ya fada kansa tsaye yana tura hannunsa cikin jallabiyyarsa ganin bata ds niyyar amsawa. Fassarar da yayi matan ta razanata matuqa,har batasan sanda ta daga kai da sauri tana rantse rantse ba
“Wallahi A’ah yallabai,magungunan fadeela ne hajiya tace na karbo daga bakin gate”
“Bakin gate kuma?” Ya tambaya cike da mamaki, saboda yasan duka magungunan da fadeela ke sha ba na nan bane, hasalima order dinsu ake mata na kusan million daya,yana damqasu a hannun hajiya qarama har sai sun qare sannan ya sake yi mata order din da kansa (nasan zakuyi mamaki,maganin million daya?,harma fiye da hakan sukan sha,sannan kamar yadda nace wasu da yawa masu gata a cikin masu lalurar EPILEPSY order magungunan nasu akeyi musu,a qalla a shekara sukan sha maganin million daya din, fatanmu Allah ya rabamu da dukkan wasu cututtukan zamani,ya qaremu da lafiya,su kuma ya basu lafiya,wadanda ya zame musu na
har abada ne kuma rabbi yasa ya zamar musu kaffara
“Eh.. .eh” kai ya jinjina,ko sun qare ne tayi order ba tare data sanar masa ba, sai ya samu kansa da lissafa adadin kwanakin da suka rage su qare din.
Har ya daga qafarsa yaci karo da roba,ya
tsugunna yana dubawa sai yaga daya daga cikin robar
maganin da ya gani ne yanzu,ya waiwaya zai kirayeta
amma tuni har ta bace a gurin,ya juyata a
hannunsa,kwata kwata tasha banban da robar
magungunan fadeela,sai kawai ya jefata a aljihun rigarsa ya wuce.
******Dukka qafafunsa ya zuro waje yana juya zaman agogon hannunsa. Yau din shigar suit ce yayi wadda tayi matugar dacewa dashi,ta fidda kyana kai kace daya daga cikin jaruman Indian films ne. Yau din har da wani extra eye glasses daya mannawa fuskarsa me duhun kala,wannan ya sake qawata fuskar tasa qwarai. Karo na uku va kalli agogon nasa,ya fahimci tunda suka fara ajjiye fadeela a makaranta suke shanyashi,a kullum sai yayi zaman jiransu,duk sanda zata iso kuma tana yine kamar batasan ta sanyashi zaman jiran ba. Kaf duniya idan ka dauke Dr jarma babu wani mutum da yake iya zaman jira,sai ita data karya masa record.
Dago kan da zaiyi suna fitowa daga sassan, kamar kullum tana rataye da school bag din fadeela tana kuma riqe da lunch bag dinta, yarinyar itama na dauke da hand bag din sãahar. Sati kusan na biyu kenan da yake ganin fitowarsu a hakan, amma har yau ya gaza saba ganinsu a irin wannan yanayin,duk lokacin da suka fito din sal sun fisgi hankalinsa qwarai, saidai yau din hankalinsa ya dauku fiye da ko yaushe. Tuni ya sanyawa guards dinsa dokar zama cikin motocinsu a duk lokaci irin wannan har su fito su wuce. Shi kansa bazaice ga dalilin da yasa yayi hakan ba,kawai dai yana ji a jikinsa hakan shine abinda yafi dacewa.
•Yau din kamar murmushi da fara’ar fuskarta ya banbamta da na ko yaushe. Cikin shigarta da ko yaushe take fita zuwa office din da ita ta laffaya. Saidai kuma a yau din laffayar ta musamma ce. Wata irin lallausar farar laffaya ce me yarfin ruwan gold,wadda ta dace da siririn takalmin qafarta me tsinin dunduniya maras tsaho,wanda zara zaran dogayen yatsunta suka kwanta luf a ciki,komai nata a ranar kusan gold colour ne, sai hakan yayi masifar qara mata kyau da wani irin haske,lafiyayyar fatarta ta fita shar.
“Wow” yaji an fada cikin wani mugun zumudi, furucin da yaja hankalinsa aka fusgeshi har cikin kwanyarsa. A nutse ya waiwaya,ba kowa bane tsaye a wajen sai Jamal.
Saidai kuma wayace a hannunsa da alama wani abun daban yake kalla. Haka kawai yaji wani abu yazo ya tsaye masa a wuya. Ba yaune rana ta farko da yakejin kamar shigar bata dace da ita ba,amma sai yake gayawa kansa rayuwarta ce,bai kamata yayi mata shishshigi a ciki ba.