TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Sassanyan kyansa me cakude da kwarini ne shimfide akan fuskarsa,zubin halitta da kyansa kuma yana ci gaba da fusgar hankalin duk wata diya mace.
Sãahar na tsaye a gefe cikin doguwar riga sakakkiya sosai wadda ta yiwa rolling da mayafin da ya sauka har mazaunanta ya rufesu sosai,shiga ta biyar kenan da tayi a safiyar kafin ya danne zuciyarsa ya haqura aka taho a hakan.
Haka kawai yau din ta samun kanta da satar kallonsa,kyakkyawan murmushin sa da wani irin aji cikin maganarsa da aikinsa. Karo na barkatai idanunta ya sauka akan fuskar ‘yammatan dake facing dinsu,ta sake samu idanunsu a kansa dukka su biyun. Janye dubanta tayi daga kansu tana jin wani abu yana tsaye mata a wuya. Sake maida kallonta tayi kansa a sace,sai takejin babu dadi cikin ranta, tunda suka fito cikakkiyar magana bata hadasu ba,yayi ma kamae baya ta tata, dukka attention dinsa na kan fadeela.
Zaman gaba daya taji baiyi mata ba,kallon da matan dake gurin suke masa taji ya fara hawa kanta,duk da wani sashe na zuciyarta nason qaryata hakan, amma tabbas tasan she’s not comfortable. Ajiyar zuciya ta sauke sanda lokaci da zasu wuce zuwa ciki yayi. Sai a sannan ya waiwayo suka hada ido,sai ta janye idanun nata gefe tana tura baki gaba wanda ita kanta batasan tayi ba,a qasan ranta tana cewa
“Dan rainin hankali sai yanzu yasan ina wajen” shi da fadeelan suka qaraso gurin,ya miga hannu a tausashe ya rigo nata hannun yayi kissing sannan ya dage hannun sama alamun yanason miqar da ita. Kamar ba zata tashin ba, amma idanun mutum biyun nan da sukafi kowa baci a gurin ta fahimci yana kansu,sai ta samu confidence sosai na miqewar, tana kuma miqewar ta fada jikinsa tayi hugging nasa tightly.
Zafafa biyar
[04/10, 8:52 am] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI *
Book 02Page 47
To dama shi din me neman kuka ne aja jefeshi da kashin awaki inji hausawa lea, maida hannuwansa yayi ya rufeta ruf
“Na baki amanar kanki da kanki, kiji tsoron Allah ki kulamin da kanki,Allah ya sani na barku kuyi tafiya ne a bisa harshen maji, saboda duk duniya babu alfarmar da zata roga na kasa yi mata, ki kularmin da amanar kanki da kanki,i love you and am gonna miss you” wadan nan sune kalaman da suka yiwa säahar abokan zama har cikin jirgi. Yana tsaye bai matsa a gurin ba har jirginsu ya tashi,ya kuma nausa dasu qasar Germany ba tare da Muhammad toufeeq jarma yasan abinda zasuje yi can ba.
_tofa, Allah ya kiyaye tsautsayi da asara,muje zuwa
dai,munata gangarewa_ 
*_GERMANY_*
HOMBURG
Zweibrücken Airport_
K’arfe biyu agogon qasar Germany jirginsu ya
sauka a Zweibrücken airport dake homburg, bisa
jagoranci da kulawar asibitin wanda sajjad ya hadasu da dukkan wanda ya dace da zai musu jagora akan komai kafin isowarsa da ya shirya yi ba tare da ya gayawa sãahar din ba suka sauka a leaonardo hotel dake kusa da Saarland university hospital main campus, inda anan ne suka suka shirya ganin prof Dr med Klaus fassbender wanda shine shugaban department na neurology and epileptology na jami’ar gaba daya.
Miss Sophia da mr Stephan sai da suka tabbatar da komai yayi settling, hatta da layin wata na kira suka bata sannan suka ce su huta, sai zuwa gobe ne appointment dinsu da Dr Klaus.
Ta window din dakin hotel dinsu akwai kyakkyawan view na garin Saarland,ta fidda kayansu tana ajjiyewa a inda ya kamata, ita kuwa fadee na daga can tana kallon garin tana zuba mata surutu har ta gama,gamawarta nata yayi dai dai da isowar ma’aikatan restaurant na hotel din da lunch dinsu.
Karba tayi tayi godiya ta rufe qofar tare da kiran fadeela tazo taci. Kusan duk wani motsi na fadeelan na kan idanunta,zuciyarta nata karyewa,sai a yanzun takejin kamar tayi wauta data taho gari ya gari ita daya da yarinyar mutane, zuciyarta a raunane tana duban yarinyar,Allah shine masanin gaibu, zata tashi ko kuma komai zai sake rikicewa ne?,ko kuma ita zata zamo sila na garuwar ciwon nata?. Da sauri ta kawar da wannn tunanin ta hanyar kiran sunan Allah, ta sauko ta jawo abincin suka fara ci tare.
Ko da suka kammala layin ta saka a wayarta,afifa ce mutum ta farko data fara kira sannan maama dinta,sai kuma mahaifinta Dr girema
“Baki kiramin abby na ba” fadeela ta fada tana karyar da kai. Dan murmushi ta saki tana juya wayar a hanunta,fadeela nason sakata yin abinda batayi niyya ba, amma tausayin yarinyar takeji, kowanne motsi na yarinyar tausayi yake bata,ta kuma kawota qasar da babu kowa nata sai ita,itace uwa da ubanta,to amma bata da tabbacin tana da number nasa a wayarta,don haka ta fara kiran nadeeya.
Kiran nadeeya din shi ya dauke hankali fadeelan daga kiran abby din,suka dinga hira kafin daga bisani sãahar ta karba wayar
“Nadeeya ki turawa fadee number abby” dariya nadeeyan ta saki a boye
“Fadee ko ummin faddee, aunty N kada dai ace har kin fara missing yaa moha?”
“Kinga sister nadeeya,kin fara rainani ko?”
“Tuba nake aunty N,waye ni da raina matar babban yaaya,so kike yayi tamaula da ni?, already na miki saving number din nasa a wayarki saboda rana me kama da wannan” sai kiran ya yanke. Wayar kawai ta sauke tana kalla,sai kuma murmushi ya subuce mata, yaushe har nadeeya din tayi saving number bata sani ba? ,sal ta fara binciken contact nata, amma ku suna me kama da nashi babu,daga qarshe tayi finding out suna guda daya da iya saninta dai ba ita tayi saving number din ba FOREVER. A bisa dole ta saki dariyar da batayi niyya ba,ko yaushe ya zama forever din oho?. Tana shirin editing ta canza suna taji fadeela na kiranta tazo ta kunna mata tv,dole ta ajjiye wayar ta fita gurinta.
Washegari miss Sophia da mr Stephan ne suka sake dawowa, already ta shirya saboda tasan da zuwan nasu. Tun daga yadda suka samu asibitin ta tabbatar afifa ta zaba musu gurin da yafi dacewa. Sun gana da Dr Klaus ya kuma yiwa säahar dukkan tambayoyin da suka dace,ya shirya komai ya kuma bada gwaje gwajen da za’a fara yi mata kafin a fara zancan surgery.
Cikin kwanaki hudun duka basu wani zauna ba,ta bada hankalinta dari bisa dari akan aikin fadeelan da zirga zirgar asibitin, don ma wasu abubuwan da yawa basu zasuyi ba daga asibitin ne. Kwana take saman abun sallah tana addu’a,sunyi waya da maji tun randa suka iso da daddare, kuma daga ita har afifa suna samun update na yanayin da ake ciki, dukansu kuma neman visa ta shigowa Germany sukeyi kafin ranar aikin,saidai dukansu basu gaya mata ba.
Cikin kwana biyar kacal komai ya kammala, Dr Klaus kuma ya tabbatar mata part na brain din fadeelan dake bada matsalan seizure din nata za’a iya removing nasa,so ta cancanci surgery, amma kafin nan zasu bata treatment na sati biyu, zasu rigeta a asibitin. Kukan farinciki ne ya qwace mata, bakinta ya kasa gajiya da addu’a da fatan samun nasara a gareta da fadeelan baki daya. A ranar suka bata daki da komai da komai, su zasu dauki nauyin kula da ita,basa buqatar majinyaci,akwai qararrun ma’aikatansu da zasu bata duk wata kulawa data dace. Tayita roqon alfarma su barta gurinta amma suka bata haquri kan haka tsarinsu yake,dole a ranar ita kadai ta koma hotel, saidai sam bacci yaqi zuwar mata,kewar fadeelan takeyi sosai,sai tayi alwala ta hau abun sallah kawai ta tsaya gaban ubangiji.