TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Ranta ya baci sosai, ba abinda a yanzun yake takura mata irin wannan gaisuwar data zame mata qadangaren bakin tulu,idan tayi ya amsa mata da qyar,idan kuma bata yin ba tana tsoron abinda ya furta zai aikata mata.
“‘Good morning” ta sake fada adan qufule, idanma bata maimaita ba tasan tsaf zaice bata gaidashi ba. Dukka gaisuwan nata yaji sarai, amma yadda ta juya baya tana fuskantar gofar sannan ta gaidashi kamar dole ya bashi haushi, yadan dauke idanunsa daga kan system din ya aza mata su
“Wani ne yace dole saikin gaidani?, ki riqe kayarki bana so daga yau,don ba qanfar gaisuwa nakeyi ba,na saka miki dokarta ne saboda na saitaki kan abinda ya dace” daga haka ya maida dubansa ga allon system din. A yau din karon farko taji jikinta ya sanyaya da yadda yayi mata magana,babu wannan fadan Sam cikin muryarsa sai wani irin softness har cikin ranta taji abun bai kamata ba,don haka ta gyara zamanta da kyau tana dan fuskantarsa
“Barka da asuba” fa furta itama da sanyin muryarta.
Tsigar jikinsa ne yaji ta zuba,ya daga idonsa a nutse sai suka hada ido,kowannensu ya janye dubansa da sauri
“Barkanki”
“An tashi lpy”
“Alhamdulillah” ya fada ba tare da ya sake dubanta ba, daga haka ta rasa abinda zata sake fade, saita ja bakinta tayi shuru tana maida dubanta ga hanyoyin da suke ratsawa da gudu.
[21/09, 9:16 am] Mimah Yusuf: “HUGUMA*
• TABARMAR KASHI
Book 02 Page 24
Har suka isa company din babu wanda ya sake cewa da dan uwansa komai. Jibril nayi parking a parking lot na company din ya kashe motar sannan yayi magana ba tare da ya waiwayo ba
“Akwai employees da suka shirya welcoming naku,da tayaku murnar aurenku,suna entrance na main building” system din ya sauke daga saman cinyarsa yana ajiiveta gefe daya,idanunsa akan jibril
“‘Waye ya sanar musu da hakan?” Ya jefa masa tambayar da salon tambayarsa din nan me cike da dakewa. Cikin dan daburcewa jibril din yace
“Yallabai sajjad ne” dauke dubansa yayi daga kan jibril,ya gama gano abinda sajjad din ya shirya, sai kawai ya bada umarnin bude gofofin motar.
Kusan dukka manyan ma’aikatan company dinne suka jeru sahu biyu hagu da dama, kowanne dauke yake da gift a hannunsa,wasu flowers wasu boxes,mafi akasari sunyi hakanne saboda säahar din, don babu wanda baii cadin mu’amalarsa da ita ba,basu sake tantance muhimmancinta ba sai bayan tafiyarta,yanzun kuwa data dawo musu a karo na biyu sai hakan yayi musu dadi gwarai.
Ta tsakiyarsu suka fara takeaway a nutse,duk wanda zasu gifata sai ya ranqwafa cikin girmamawa. Mr hamza shine mutum na biyu a sahun, sunzo dab dashi ya ranqwafa idanunsa akan fuskarta
“Sir, congratulations, congratulations sir” ya fada da dan murmushi saman fuskarsa,sannan ya miqa flower din ga sãahar.
Baisan ya akayi ba,yadai tsinciki kansa da sanya hannu ya karba flower din daga hannunsa ya miqawa elyas tare da yi masa inkiya, sannan a hankali ya sanya hannunsa ya lalubi hannunta, ba zato ba tsammani sai jin tafin hannunta yayi ya manne da lallausan tafin hannunsa guri daya,ta waiwayo da hanzari tana dubansa idanunta kuma suka fada cikin zagayayyun fararen idanunsa. Zame hannunta taso yi cikin hikima da dabara amma ya matseshi tsam cikin nata,saboda ya fuskanci idanun mr hamza na kan hannayen nasu
“All eyes are on us” ya fada qasa qasa,a hankali itama tayi noticing hakan, musamman daga idanun mata da yawa da dama can ba huldarsu take shiga cikin company din ba, da masu goqarin shiga gonarta amma tayi musu iyaka irinsu saima.
A gaggauce suka dinga wucewa,hakan ta bishi saboda hannunsu na cikin na juna. Bai sakar mata hannu ba har suka isa bakin elevator.
Zame hannunsa yayi a nutse,abinda sãahar keta qoqarin yi kenan,ba tare da ya dubeta ba kuma ba tare da yace da kowa komai ba ya danna button ta bude.
Baya yaja kadan tare da yi mata nuna da hannu akan ta shiga. Cikin nutsuwa tabi ta gefansa,har kafadarta na gogar hannunsa saboda yadda ya tsaya yayi bake bake a bakin elevator din,wannan ya sake bawa turarenta damar bugun fuskarsa,ya damqe hannunsa da kyau kamar wanda ya boye wani abu. Waiwayawa yayi baya,kallo daya ya yiwa su elyas taga sun janye baya,ya taka da sassanyan takunsan nan ga shiga ya rufe dasu suka fara haurawa. Shuru elevator din yayi sai qamshin jikkunansu daya cikata. Yana tsaye daga gabanta dai dai bakin gofa,wannan ne ya bata damar gare masa kallo da kyau,duk kuwa da yadda taso dauke kanta,amma halin zuciva, sai taji a karon farko tana son yin hakan. Tun daga kan lallausar nannadaddiyar sumarsa,murdadden hannunsa dake boye a aljihunsa, daya hannun nasa dake rige da waga qawatacciyar briefcase dinsa zuwa bayansa da takalman dake gafarsa wanda suketa daukan idanu. Tana gama satar kallon dai dai sanda elevator din ta iso dasu floor din da suka nufa wato gini na garshe na kamfanin. Ya danns button din sannan ya taka yana shirin fita
“Ki ringa kame ganinki,karki manta ni dan iska ne me yiwa mata fyade, muddin kika cika kallona zan iya dauka cewa ranki ya biya ne da ni, komai kuma zai iya faruwa”.
Idanu ta fiddo waje cikin mamakin maganarsa,sai tasa hannunta guda daya ta dafe kanta haushin kanta yana kamata,meye ma ya kaita tsaiwa ta kalli wannan mutumin idan ba jawowa kai matsala ba ta fahimci shi kullum baiso a zauna lafiya,batasan meye tayi masa ba,wai shi kunyar furta kalmar fyade ma baya jinta sam?. Gani tayi idan ta barshi ba shakka ya sha da ita, saita tako itama tana biye dashi sanda yake scanning key din a jikin qofar
“Wai shin me ma zan kalla hala? wannan kodaddiyar fatar ko kuma wanna gashin mara kyan gani?” Ta furta tana nuna singalilin hannunsa dake riqe da handle din gofar. A karon farko dariya taso qwace masa amma ya rage kaifinta ta hanyar murmushin gefan bakiya kalli hannun nasa data nuna sai ya sanya daya hannun yana shafarsa
“U’uzubi kalimatillahit taammati minsharri ma khalaga, da gasken dai qaremin kallo kikeyi, banda haka ta ya kika san da zaman gargasata iyee?” Ya jefa mata tambayar data sanyata fara raba idanu amma ta basar
“Bayan gashina mara kyan gani sai kuma meye kika gano?,oya tell me” ya fada yana murza handle din tare da tura gofar baya ta bude.
“Eheenn, ina jinki da meye da meye?” Ya kuma jefa mata tambayar yana matsota idanuwansa akan lips dinta da suke haifar masa da wani irin abu a jikinsa wanda yake sanya tsigar jikinsa zubawa,a duk sanda yaga lips din sai ya tuna da santsi da kuma laushinsu. Ba zato ba tsammani taii va cafketa ya kuma finciketa zuwa office din ya maida murfin da qafarsa guda daya. Jefata yayi jikin bango yana bin bayanta
“Saifa kin gayamin, kada naje wadan nan marasa kunvar idanun naki sun ganemin sirri na” yadda ya matseta da bango ya sanyata jin kamar iskar dake wajen tayi mata kadan,ta tabbatar ko da wasa ta motsa ba shakkan qirjinta shine abu na farko da zai fara gogar jikinsa.
Qangame jilkinta tayi guri daya tana rufe idanunta sanda taga ya taho da hannunsa saitin fuskarta, ta gama taga ya taho da hannunsa saitin fuskarta,ta gama saddagarwa may be maruka zata sha,sai taji yatsunsa guda biyu saman lips dinta suna zagayasu.
Tsigar jikinta ne ya zuba lokaci daya taji kamar wayar wuta ta jata