TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

Wani rudu ne ya shigeshi,a hankali yaji zuciyarsa ta motsa da wani irin qarfi ta matse guri daya

“Aure zatayi?” Ya tambayi kansa,kamar ba yanzun nan kunnuwansa suka jiye masa abinda tace ba

“Idan tayi aure ta tafi,yaya makomar rayuwar fadeela?” Muhimmiyar tambayar data tilasta masa furta abinda ko a mafarki bai taba zaton zai furta ga kowacce diva mace a doron duniya ba

“Will you marry me?”. Wannan kalmar idan ta kirata da saukar ajali lokacin mutuwar fuju’a a kunnuwanta to batayi kuskure ba. Kalmar data ji girmanta ya wuce girman dutsen dala a kanta. Kunnuwanta suka bada wani shuuu,sai ta kasa daga qafafunta daga gurin,kamar an dasata

“Will you marry me?” Ya sake maimaita maimaitawa a karo na biyu. Wannan karon wata faduwar gaba da sautinta yakai har ga kunnuwanta taji,numfashinta yadan so ya fara fita da sauri amma saita yi qogarin saitashi. A nutse ta waiwayo tana dubansa kai tsaye

“Absolutely no” ta zare idanun nata daga kansa tana qoqarin ci gaba da tafiya. Saidai taku biyu kacal tayi ya cimmata,ta fahimci hakanne ta hanyar qamshin turarensa da ya mamayeta,taja baya da sauri tana rabewa gefe,saboda yadda yayi bake bake a bakin gofar,kwarjininsa ya daketa da wani qarfi,ya sanya wannan magnet din sosai a kanta da ya sanya ta kasa duban idanun nasa a yanzu.

Nasa kallon ya dauke daga kanta yana zaro complimentary card dinsa,yayi taku biyu zuwa inda take,abinda ya kusa dauke numfashinta kenan,saboda bata ga card din hannunsa ba,saura qiris tace masa ya dakata, Allah yasa batakai ga fada din ba ya zura mata card din a gefen jakarta dake maqale a hannunta

“Idan kin canza shawara you are always welcome,zamuyi aure don ki kula da fadeela kawai, wannan shine manufar,ni kuma zan baki dukkan ‘yanci da mafakar da kike nema” daga haka ya juya a cikin nutsuwa da kamewa ya fice.

A qalla sai da yabar gidan ta motsa daga gurin,ta gama tsorata da yadda ya kafeta da kallomsa,batajin ya taba mata irin wannan kallon kai tsaye,yadda ya nufota kanshi tsaye baya ma ko tsoron ya muhyiddeen ya dawo ya ganshi ya bata mamaki. Tsaiwarta ta gyara tana kallon card din, butter milk color da aka yiwa ado da ruwan gold. Tsaki taja,ta sanya hannu ta zaro card din ta watsar a wajen. Wai ta aureshi saboda ya raina mata wayo,shi baisan ko bashi bama ba zata iya auren kowanne namiji ba? ta rasa ma wa zata aura saishi? har abada,Allah yayi mata tsari.

Dukka ta gama wadan nan maganganun cikin banbami a ranta ita daya,ba tare da tasan gaddara tana sauya komai cikin qasa da sakanni ba kamar dai qiftawar ido. Kusan hakance ta sameta,bayan ta samu yaa muhyiddeen kamar yadda ya umarceta,ya kuma shaida mata a satin nan mahmud zai turo magabatansa da komai nasu,aurenta duka duka bazai wuce watan gaba ba,so basa son mata auren da bataso,idan tana da wanda takeso tayi gaggawar gabatarwa da abban nasu. Tashin hankali,shin a dazu ta gayawa toufeeq wannan maganar kenan da harshen malaiku? ,wata gudan data ambata shine ke neman tabbata a kanta cikin mintunan da basu wuce talatin ba?.

Fadin irin mawuyacin halin data fada ma bata bakine idanunta suka soye sai qirjinta dake zafi, batasan me yasa suka dage sai sun aurar da ita ba,bayan har yanzu bata gama healing ba,tana buqatar lokaci sosai,a galla shekaru goma ma a gaba idan sun bata dama.

Ita dava cikin dakin,qarfe biyu na dare tazo ta risketa ba tare da bacci ya ziyarceta ba,sai tarin fargaba da kalmar auren da yaa muhyi ya furta mata daketa yawo a saman kanta. Ta wacce hanya zata samu ta kubcewa wannan qaddararren auren?,dama dukkan wani aure a nan gaba har sai lokacin da taji zuciyarta ta gamsu ta aminta da aure?.

“Akwai” taji zuciyarta na gaya mata,amsar da taja hankalinta ta kuma sanyata neman baasin maganar

“zamuyi aure don ki kula da fadeela kawai wannan shine manufar,ni kuma zan baki dukkan ‘yanci da mafakar da kike nema” kalamansa suka dawo tarwai cikin kunnuwanta,kamar a sannan yake furta mata
SU.
[12/09, 5:41 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI *

Book 02 Page 06

Wani irin zuzzurfan nazari ta shiga yi,tanason ta yiwa kalaman nasa duba na fahimta,ta kuma nazarci ma’anarsu da kyau.
“Indai hasashenta yayi dai dai,indai ma’anar fassarar tana nufin abinda ta tsinkaya ne…..zai aureta ta kula da fadeela,ita kuma tayi rayuwarta tamkar macen da bata da miji,babu doka,babu oda,babu auratayya,babu sawa babu hanawa…a idanun duniya sunanta matarsa,amma a tsakanin su din bagin juna ne,kowa zaiyi harkar gabansa” wannan hasashe kadai ya haifar da kyakkyawan murmushi saman fuskarta

“Yes… yes” ta fada gasa gasa tana sakin murmushi

“Ta samu cikakkiyar mafaka,ta kuma samu dama irin wadda zata bata damar yin rayuwarta lya adadin tsahon shekarun da takeso ba tare da takurawa ko sanya idanun kowa ba”. Sosai taji al’amarin ya kwanta mata,wanann din wata idea ce me kyau. A daren ta fara laluba card din da ya bata cikin jaka,sai ta tuna ta yasar dashi a falon batama fito dashi ba. Ji tayi a daren kamar ta fita ta dauko card din,amma dole ta haqura zuwa safiya.

Haka kawai kuma wani sashe na zuciyarta ke umartarta tayi addu’a. Bata wofantar da wannan shawarar ba,sai ta mige ta daura alwala, don dama ita din gwanace ta wannan fannin,dai daikun darare ne suke wuceta,farinciki ko baqincikinta tana juyeshi ne saman abun sallah, wanda hakan yake qara mata nutsuwa tare da hasken rayuwa,matsalolinta masu yawa kuma warwara take zuwa musu a qanqanin lokaci.

Raka’a shida tayi,tana gamawa taji wata nutsuwa na shiga ruhinta,kamar iskar dadin na dada sanyi da dadi,tana yiwa annabi salati idanunta suna lumshewa,a haka har wani daddadan bacci data jima batayi irinsa ba ya sureta.

Washegari bata tashi da wuri ba,saboda bacci tayi sosai,bayan ta farka tayi brush tare da alwala,ta dawo cikin dakin nata ta sakawa wayarta charge,ta kunnata ta zauna daga gefan gado,ta buda inbox ta turawa afifa sagon da tasan dole ne ta dawo gida koda bata nemeta ba,duk da jiya da magriba ta tafi zooroad

“Bestie aure zanyi”_ abinda ta tura mata kenan ta sauka tabar wayar a charge ta fito falo.

Masu aiki keta hidimar kimtsa gidan,da )alama aikinsu na safe yazo qarshe saina rana dana dare. Cikin sakewa suka gaisa kamar yadda suka saba,baaba rabi ta gaya mata maama tace a shaida mata idan ta farka,ta tafi gidan uncle ismail,yau din za’a kawo lefen zeenat qarfe uku na yamma,idan ta gama komai ta sameta a can saisu dawo tare. Tana amsa mata tana ficewa,tanaso ta samu card din kafin masu gyaran gurin su hada dashi su share.

Sai data danyi dube dube sannan ta ganshi,ta tsugunna ta dauka tana kallon rubutun dake a jiki. Rubutu ne dake cike da tsari da kuma ban sha’awa,full name dinsa email and phone duka a jiki. Dan tabe baki tayi,tana tuna irin izzarsa da jin kansa,wai yama akayi yasan wasu abubuwa haka a kanta?,ya akayi yasan ita din bazawara ce?,ya kuma akayi yasan gudun auren kowanne namiji takeyi?. lya hasashenta bata iya ganewa ba

“Oho masa,shi ya sani” ta fada a fili tana komawa cikin gidan,ta shiga dakinta ta yiwa card din waje,sannan ta shiga hidimar gabanta.

********Sanye yake da long sleeve kaftan thobe button down, wadda daga qasa gefe da gefe yake a tsage,fara ce qal kamar yadda mafi yawa zabinsa kenan a kaya,hannun rigar ya tattareshi zuwa gwiwar hannunsa,yana riqe da mug na coffee kamar kullum yana kurba,idanunsa akan fuskar fadeela daketa faman gogarin zana wani dan tsuntsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected