TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Migewa tayi dole tsaye,tanajin kamar hawan jininta zai tashi ta zare rigar jikinta tana jin duniyar na juye mata cike da tashin hankali, tashin hankalin data jima bata afka cikinsa ba,tsahon shekaru batasan tashin hankali ba,saboda dukka abinda ta nema tana samu,zallar farinciki da wanzuwar kwanciyar hankali kadai ta sani,sai gashi yau yarinyar da suka dauka aiki a matsayin nanny tana neman ruguza duk wani lissafi nata data dauki shekara da shekaru tana yinsa. Inda ace tana da masaniyar abinda zai faru kenan,da kanta zata koreta kafin tabar gidan,amma inaa.…..sai gashi wani qatoton tsautsayi ya gifta wanda ba zata taba barinsa ya zama qaddara ba.
Dole ta qara gaba itama, haseena ce kadai tafi dacewa ta mallaki toufeeq din,yadda ta qarasa rainonsu har suka girma,lallai su sukafi cancanta suci amfaninsa.
Qara kadai wayarta tayi amma sai da gabanta ya fadi,bakinta yahau addu’ar Allah yasa ba haseena bace don batason tayi kiranta ta fuskanci akwai wani abu. Hajiya mansura ce,sai da taja tsaki sannan ta koma ta zauna,cikin ranta tana jin me yasa ma ta
¡awo matar nan ta maidata daya daga cikin ahalinta?,a shekarun nan gaba daya tsanarta takeji cikin ranta. Sai da wayar ta kus tsinkewa sannan ta daga. Akwai tashin hankali me yawa cikin muryar hajiya mansura sanda take magana da hajiya qarama
“Kinji abinda yake faruwa?”
“Naji,menene?”
“Baki tambayi halin da labiba take ciki ba,kin ganta can ta kulle kanta a daki,nayi mata maganar duniya taqi fitowa,ki taimaka don
Allah ki kirata kuyi magana ko hankalinta zai kwanta” yatsine fuska hajiya qarama tayi tana iin kamar ta rufeta da duka ta wayar
“‘Mansura!” Ta kirayeta da tsurar sunanta,mamaki ya hanata amsawa,itama kuma bata jirayi ta amsa din ba ta dora da jawabinta
“Yanzu labiba ta fara kuka ai,don bata dace sam da toufeeq ba” mamaki ya kusa sanyawa hajiya mansura faduwa,sai data lalubi gurin zama
“Me kike fada ne?,ko kin canza daga alqawarin da kikayi mata?”
“Tun wacce shekarar?,ai daga lokacin da haseena tazo hutu tun tana da shekara sha takwas,ta nuna muradinta akan TOUFEEQ alaqawarin dake wuyan labiba ya sauka ya koma kan haseena,ko don kinga inata muku kara ke da ita?,ban fito kai tsaye na nuna mata bazata sameshi ba?” Ta qarashe maganar da tambaya,tambayar da rawar da bakin hajiya mansura yakeyi yasa ta gaza amsa mata
“Ai na dauka kuna da qwaqwalwar da zata gaya muku gaskiya,me muka hada daku da zamu dauki TOUFEEQ mu jingina shi da yarinyar da har yanzun ba’a da tabbacin ubanta ubanta ne!”
“Ke fauziyya dakata!,ya isheki haka!” Hajiya mansura ta fada cikin matsanancin bacin rai.
Shu’umin murmushi hajiya garama ta saki tana jinjina kai
“Uhmmm,ni kike dagawa murya ko mansura? ni ba? inajin kin manta cewa ba yau na fara fidda matan wana daga gidansu ba,wadda ma take da zuri’a damu na kadata ta koma qasarsu ballantana ke da babu abinda muka qaru dake sai gatoton kashi da kike ajjiyewa suckaway,ki iya bakinki idan ba haka ba nan gaba kadan zakiyi nadamar da zata zame miki har qarshen rayuwarki”
[14/09, 7:44 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI_ *
Part 02 Page 8
gintse kiran hajiya qaraman tayi tana zake jan tsaki mai qarfi sosai,can gasan ranta tana in zafin tsawar da mansura tayi mata
“‘Lallai duniya tayi lafiya” ta gayawa kanta da kanta,banda haka mansura ko kallon banza bata isa tayi mata ba bare tsawa har irin wannan. Qwafa taja tana dukan tafin hannunta da dayan hannun,ko a yanzun ta tabbatarwa kanta bashi mansurar taci,sai kuma ta biyashi da abu mafi zafi.
*_DR JARMA_*
Suna gama waya da fauziyya din ya ajiye wayar a gefansa yana binta da kallo,cikin shekarun nan yana samun kansa cikin nazarce nazarce,kamar ana yi masa bitar wasu kura kurai da ya tafka a shekarun raywarsa na baya. A yanzun bayajin zai sake tilastawa wani cikin ‘yayansa yin wani abun daya zama ba bisa ra’ayi ko son zuciyarsu ba,hakan yasa duk yadda yaso ga kawo SÄAHAR cikin ahalinsa bai aikata hakan ba kai tsaye,saidai yayi wani abu da ya zama yayi pushing toufeeq din zuwa ga neman auren da kansa,ta yadda ko a gaba sunansa bazai fito cikin wanda yake ganin ya tilastashi ba,duk da yana jin alkhairai masu tarin yawa zasu fita daga gurinta tun saninta na farko da yayi a rayuwarsa kafin ma aje ga ganinta.
Wayar tasa ta sake qara a karo na biyu,ya waiwaya yana duban number da ake kiransa. Zumbur yayi yana sake zama sosai yana duban wayar,yakai hannunsa ya murza idanunsa cike da dumbin mamaki number wayar da ya mallaketa shekara guda kenan ya kuma gaza kiran mamallakiyar number, yau sai gashi number tana yawo saman screen dinsa a lokacin da bai taba zata ko kawowa ba. Haka kawai yaji ya gaza daga kiran,sai wani fat fat fat da girjinsa yakeyi,yau shi SHIFA ke kira? ,bayan tsahon was shekaru da suka shude da tarin galubale ZAQI DA MADACI?
Kamar wanda aka fuzga bayan tsinkewar kiran va sanya hannu hannun nasa yana rawa ya dauki wayar ta shiga bin kiran.
Shuru kaman ba za’a daga ba,yanata addu’a cikin ransa akan ta daga din,ya tabbatar bata da number dinsa ne kuma ko yanzu baya saka ran tayi saving kafin kiran nasa,yadda ta alqawarta masa a can bayan sai data tabbatar da halaccin haihuwarta,ta cika alqawarin,kamar yadda tace ta barshi har abada,amma akwai wata eana da zata waiwayi abinda ta haifa a cikinta. Ta barshi din,wanda kod wasa bata taba gwada nemansa ba,yaranta dai batayi fushi dasu ba ko ganqani,bata bari komai ya shafesu ba.
Tana dab da tsinkewa,kamar ba zaa daga ba sai kuma yaji an daga din,shuru ne ya biyo baya,abinda ya tilasta masa yin magana a wani yanayi dake nuni da kamar yana d’ari d’ari
“Assalamualaikum warahmatullah”
“Waalaikumus salam warahmatullah” ta maida masa amsa har sai da kowanne lungu na jikinsa ya amsa da muryarta,muryar da ya dauki shekaru masu tsaho ba tare da kunnuwansa sun jiye masa su ba,muryar da bazai taba mantawa da ita ba har abada
“Barka da wannan lokaci,na kira ke na shaida maka ni da ahalina zamu sauka a nigeria bikin d’ana kuma d’an uwa a garesu,zamu sauka cikin gidan d’ana in sha Allah,bawai ina gaya maka wannan labarin ba saboda neman izini
kamar yadda ake bugata,na shaida maka
ne saboda kayi magana da ‘yaruwarka,ka
gaya mata jiya ba yau bace,sannan muna
da buqatar zaman lafiya ayi biki lafiya
a gama lafiya kowanne bago ya koma
muhallinsa,gargadine wannan daga gareni,ina
fatan zaka isar mata” iva abinda ta fada kenan
ta yanke wayar.
Sosai qirjinsa yayi masa nauyi,ya fara jan
numfashi tare da fesar dashi
“Shifa,har yanzu tana nan da halinta bata
canza ba,babu daukan raini ko qasqanci,babu
gudu babu ja da baya akan gaskiyarta,sai
yaushe abubuwa zasu canza tsakaninta da
FAUZIYYA?” wannan din dukka halave da
dabi’arta ne. Bata yarda ta sakarwa abokin
adawa wasa ba,muddin ita ke da gaskiya sai
taga abinda zai turewa buzu nadi. Bai wani
damu da maganganunta ba,abinda yake kai
kawo tsakanin ruhinsa da zuciyarsa ya shafe
wannan. Gaba daya jikinsa ya saki,ya rasa
shifa shekaru masu yawa,kuma har yanzu
qaryarsa ta sha qarya yace ya samu koda rabi rabin madadinta ne. Shin meye abinda yasa ya kasa haquri da ita a wancan karon ne?.
FAUZIYYA sunan da yazo kansa, zalunci suka aikatawa shifa da gudunmawarsa kenan?, tambayar da tasa kansa sarawa har sai da yasa hannu ya riqe goshinsa da kyau. Dai dai lokacin da hajiya mansura ta shigo falon afujajan,zuciyarta cike da tsoro da fargabar abinda fauziyya zata iya aikatawa,gwara tun yanzu tasan wanne tudu ta dafa.