TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Kici wani abu kafin mu fita” kai ta girgiza

“‘Bazan iya ba bestie, tunda nazo garin nan sau daya
nake iya cin abinci” ido ta fiddo

“Saboda me?” Kafada ta dage

“Ban sani ba afifa, kawai inajin cushewar ciki ne,sannannayi loosing apatite gaba dayaa, bakina bashi da taste”

“Kuma a hakan sai a duka yawon shaqatawa
kikazo fatarki tayi wani mugun fresh da haske kamar
wadda ke wanka da madara” wani marayan murmushi tasaki tana kaiwa afifan duka

“Ke har yanzu baki girma ba wai?,ga baby kina shirin ajemana,mutumin da bai iya cin abinci yaushe zai samu irinwannan nutsuwar da kike fada?”

“Eh kika sani ko babies din namu tare sukeson isowa” afifa ta fada tana murmushin tsokana. Dan tsuke fuska tayi tana harararta

Zafafa biyar

[05/10, 11:55 am] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

•_ TABARMAR KASHI_

Book 02 Page 50

“An gaya miki kowana ayu ne irinki?, besides mani ba auren zama nayi ba wannan shine last aikina da zanyi na gama zama a wajen” dariya sosai afifa ta saki harda kama ciki, sanann kuma daga bisani ta samu guri ta zauna. Dariyar ta qular da sãahar

“Waye kikema dariya haka?”

“Astagfirullah,da wanda ya tsargu nake” ta fadi tana fuskewa. Bata taba gain wauta zalla irinta sãahar din ba,da gasken gaske autar ce ta gaske, duk yawan buda sagonnin toufeeq da yadda fuskarta kan saki a duk sanda ta gama karanta sagon afifan na karance da shi daga jiya zuwa yau din,amma duka wanna ta tattara ta ture, itakam zataso taga ya wanna drama zata kaya.

_muma zamu so mu gani ni da jama’ar zafafa_

Sai säahar din bata sake cewa komai ba don vau
din bata jin kowanne wasa da afifan zata yi mata zaiyi tasiri, amma hakanan maganar baby din data fada saita tsaya mata a rai. Ta yaya zata samu wani baby?, bayan ko kafin ta taho tayi period, kuma zuwa next week take sanya ran zuwan next period dinta,sannan ko a yanzun tana jin cramps a mararta, amma idan ya tabbata fa baby dinne? ta yiwa kanta da kanta tambayar,sai kawai ta samu kanta da subucewar murmushi a fuskarta wanda ita kanta batasan dalilinsa ba.

Kurba uku kacal ta yiwa tea din taji ya cika mata ciki fal, qamshin madarar dana Lipton din ciki yana son hautsina mata ciki,sai ta ajjiye tana duban afifa dake cin abincinta tuquru kan jiki kan qarfi. Kaman zatace wani abu sai kuma ta janye idanunta, tuni afifan ta ganta, murmushi ta saki

“Bestie wannan dan naki acici ne Allah”

Sai da dukkansu suka jira afifan na kusan minti
ashirin ta gama lodin abincinta sannan suka fita farfajiyar hotel din,inda taxi din da zata garasa dasu asibitin su ukun take jiransu.

Ko a hanya ma shuru ne nata,tayi nisa a duniyar
tunanin me ranar ta vau zata haifar musu? farinciki ko
akasin haka?, abinda ke qara sanyaya mata gwiwa daya ne,dukkan sakamakon da zai biyo baya ITACE SILA ALKHAIRI KO AKASINSA.

Da gudu fadeela ta sauko daga saman gadon ta
rungumeta tana kiran sunanta

“I missed you anty N” sosai sãahar ta rigeta hawaye
nason zuba a idanunta amma tana danneshi, ta tsugunna a hankali ta rungume fadeelan cikin jikinta hawayen na zartowa. Har an aske area din da za’a yi mata surgery din. Tsanar hajiya garama ta sake cika a zuciyarta sanda fadeelan ke fadin

“Abby bazaizo na ganshi ba?” Banda gudun sharrinta, ta yaya za’a yiwa fadeela aiki irin wannan toufeeq baya gurin? baima sani ba?.

“‘Zaizo in sha Allah my fadee, kada ki damu”

“Yaushe anty?” Ta sake tambayarta tana rungume a jikinta

“Yau in sha Allah” taji afifa ta fada tana riqe hannun fadeelan a tausashe. Ajiyar zuciya säahar din ta saki, har a ranta taji dadin yadda afifan ta kubutar da ita, don batason viwa fadeelan qarya.

Migewa tayi ta aza fadeela din saman cinyarta tana jin labaran da take bata na nurses din dake kula da ita,da sauran abubuwan da ke wakana a asibitin duk sanda ta tafi gida.

Awarsu guda nurses biyu suka shigo dakin nasu,cike da kulawa da sanin darajar mara lafiya suka shaida musu zasu shirya fadeela za’a shiga da ita theater room din. Dukkansu dai jikinsu yayi sanyi, banda ita abinka da yaro da kuma quruciya, tana ta yiwa säahar hira ita kuma tana qoqarin boye hawayenta. Har suka kammala shiryata hannunta yana cikin na sãahar, ba ita ta sake mata hannu ba har sai data isa gofar theater room din. A hankali ta zame hannunta cikin nata, amma idanunta cikin na fadeelan. Duk yadda taso dakewa ta kasa, muryarta na rawa tace

“Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya fadee na,in sha
Allah,in sha Allah from this day kin rabu da wannan lalurar rabuwa ta har abada. Murmushi kawai fadeela tayi mata,idanunta gyar bisa fuskar säahar din har suka maida gofofin suka rufe suka daina ganin juna.
Afifa ce ta matso tana dora hannunta akan kafadar saahar din

“Wannan damuwa ta isa hakanan-karkije ki yiwa kanki illa fa, damuwa a irin situation dinki bata kamaceki ba,an viwa mutane bila’adadin surgery din nan,kuma alhamdulillah they’re healthy and safe,suna rayuwarsu vanzu kaman kowa,ya riga ya zama tarihi ma,samu guri ki zauna” sai taja hannunta suka zauna saman kujerun dake shirye a gurin.

Sannu a hankali sakanni suka juye zuwa mintuna, mintuna suka juye zuwa awanni, awa ba daya ba har biyu shiru,zuwa lokacin sai ta dinga jin kamar hankalinta nason barin jikinta, da gyar ta iya daurewa aka cinye awanni uku cur.

Tuni duk wani fata nata ya yanke, confidence dinta ya soma zagwanyewa tsoro da firgici, ta waiwaya ta dubi afifa data dawo daga cin abinci, abincin da babu yadda batayi da sãahar din tazo suci ba amma tace ba zata iya motsawa ko nan da can ba

“Bestie lafiya kuwa? 3hours fa” dan murmushi ta sakar mata na kwantar da hankali

“Ba komai in sha Allah, suna aikinsu ne” kasa zama tayi,sai ta mige ta koma dakinsu ta daura alwala,sannan ta dawo gurinta,ta bude qur’anin cikin wayarta ta fara karantawa gasan ranta ko hakan zai taimaka mata ta samu nutsuwa komai qangantarta.

Sannu sannu sai gashi an sake shafe wata awa
dayan har da rabi, adadin awanni hudu da rabi kenan,zuwa lokacin karatun kawai takeyi, amma gefen lafayarta gaba daya ya jiqe da hawaye, idanunta kuma sun tasa sunyi jajur, kamar yadda fuskarta ta hada jaa musamamn wajen hancinta zuwa habarta, abinka da farar fata. Duk iya hilatar da afifa zatayi tayi matan amma kuma bata samu nasara ba dole ta zuba mata ido ta shiga tayata da addu’ar itama cikin zuciyarta.

Sajjad ne ya shigo gurin, ya tsaya daga baya ya yiwa afifa alamar tazo da hannu,dukka tana kallonsu,amma hankalinta baya kansu, har zuwa sanda afifan taie sukavi magana qasa qasa sannan ta sake dawowa wajenta,shi kuma ya juya ya fice a hankali.

›Wasu mintuna arba’in dinne suka zo suka wuce duka akan idanunta dake a rarrabe tsakanin qur’aninta da gofar theater room din.

A hankali gofar ta bude, abinda ya kusa tsayar da bugun numfashinta saboda wata qaqgarfar faduwar gaba. Ko ina a jikinta rawa yakeyi sanda likitan ya bayyana a gofar dakin. Zumbur ta mige har wayar hannunta na subucewa ta fadi a gasa, dukkan idanunta a kansa tanason zuwa ta riskeshi taji daga bakinsa amma tsananin tsoron abinda zataji daga gareshi ya hanata aikata hakan.

Lokaci daya kuma gabanta ya sake faduwa fiye da na dazu sakamakon tsintar muryar da bata taba zaton ji ba. Da wani irin sauri ta juya tana kallon qofar farko ta shigowa gurin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected