TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
tata. Ruqayya qawar maji ita tayi wuf ta aika da baaba ramatu,saboda yadda da amintar da tayi da ita,ta kuma tabbatar zata bawa yaran dukkan wata kulawa tare da kula da lamarinsu. A hankali baaba ramatu ta fuskanci yadda fauziyya ta kawar da hankalin yaran gaba daya daga ganin kima da jin maganar kowa,duk abinda ta shimfida ya zauna daram. Da farko maji na kiransu,idan aka kwana bivu bata kira ba zasu nemi babansu ya kira musu ita suyi magana sannu sannu sai gashi gaba daya daga yaran har babansun sun soma mantawa da wata mai suna MAJI sam cikin gidan,duk wata kewa da qulafucinta da sukeyi ta sanya anzareshi tsaf daga ransu,sai abinda tace sai abinda takeso.
Tun ba’a ie ko ina ba ta raba auren maryam qawarta da dr jarma,ta sake kutun kutun ta aura masa murja itama bayan wasu shekaru ta raba auren da salon kissa da kuma asiri. Cikin shakarun sai data aura masa mata hudu tana sanyawa yana sakinsu, mace ta garshe da ta aura masa mansura. Mansura itace babbar aminiya cikin gawaventa, kuma ta kashe aurenta ne don kawai tazo fauziyya ta aura mata Dr jarma,ta fito daga gidan baban labiba ta baro yara hudu labiba auta ta biyar,can qasan zuciyar mansura itama danqare fal da buri da nata qudurin na mallakar Dr jarma da uban dukiyar da ya fara tarawa a dare daya.
Mafarin rashin gaunar da toufeeq yake yiwa mansura din ya samo asali ne da zuwansa gidan wata rana,a lokacin duka duka shekararsa sha biyar ya samu tana yiwa Dr jarma barbaden magani, wanda kusan maganin nata ne data fauziyya,yawanci mansura ita ke sabuntawa fauziyya aikinta,saboda komai yana tafiya mata dai dai,rayuwa tana mata yadda takeso,bata bugatar Dr jarma ya koma Mahmud dinsa, ta tabbatar inda har yanzu maji na cikin rayuwarsa babu lallai takai matsayin da take kai yanzu a rayuwarta.
Komai yana iskar maji ta hanyar ruqayya,co sau daya bata taba sassautawa wajen yiwa yaranta addu’a ba,tasha hana idanunta bacci saboda sallah,ta sha hana cikinta abinci saboda azumi, duka tana yine saboda nemawa yaranta kariya,a kullum idan ta kwanta babu abinda ke mata yawo a kunne sai kukan nadeeya dana toufeeq, wani irin kuka me karyar da zuciyar me imani suna kiran sunanta,kukansu na qarshe da taji bata kuma sake ji ba saidai tayi hasashe.
Shekararta biyar da rabuwa da DR JARMA sannan tayi wani auren,saidai auren duka duka shekara biyar mijin ya rasu, bata kuma sake sha’awar sake wani auren ba,ko wancan matsantawa ce ta yayanta guda daya daya rage, shekara biyu kadai da yin auren kuma ya rasu.
Sau biyar hajiya qarama na yin aure bayan aurenta na fari da ya’aqoub, amma auren baya wani lasting sal ta fahimci ba don komai suke aurenta ba sai don abinda ta tara,saita sallami mutum tunda yawanci auren dauki sandarka ne. Allah ya jarabceta da sha’awar auren amma haka ta tattara ta haqura saboda tsoron kada abinda ta Jima tana yaqi akan tarashi ya salwanta. A karo na shidda ne taga DR GIREMA(mahaifin säahar), a lokacin suna abota sosai da Dr jarma kafin rayuwa ta cilla kowa wani sashe na daban. Ta mutu sosai akan dan mutanen borno shuwa arab na asali dake da kyau na burgewa,irin kyan da take ganin yayi dai dai da nata kyan. Ta soma shiga da fita akan a jawo mata hankalinsa,cikin ikon Allah duk inda take tunanin nasara babu ita,a hankali ta fahimci matarsa tsayayya ce,ta tsayawa kanta da mijinta da addu’o’in tsari,sannan gwanace kuma qwararriyar mace wadda ta amsa sunanta wajen iya kula da miji tare da dasa soyayyarta me zafi a zuciyarsa,don duk inda ka zauna dashi zama ya danyi tsaho sai yayi maka zancan AMINATOUnsa. Tayi barnar kudi akan dr girema kamar ba gobe amma kusan a banza za’a ce,don babu wani ci gaba ko nasara data samu,tana ji tana gani haka ta haqura da shi, don ta fahimci kallon ganwa kawai yakeyi mata, daga gaisuwa kuma babu abinda yake qara shiga tsakaninsu.
Abinda maji ta mallaka daga gadon iyayenta da tumunin takabarta data samu shi ya shiga kasuwanci dashi babu kama hannun yaro. Family dinsu babban family ne kuma sananne da suke da mutane masu tarin muqamai kala daban daban,wannan yasa bata wani sha wahala ba kasuwancinta ya samu karbuwa daga gurin matan manyan qasar ta Algeria, a hankali kuma sai ya fadada zuwa qasashen qetare maqwabta,harma da
Nigeria din kanta, amma bata taba yarda ta saka qafarta Nigeria ba saidai aike, duk da cewa Zuciyarta da gangar jikinta ko da yaushe tana kan yaranta,tana kuma bibiye da dukkan wata nasara ko faduwa tasu.
Taso zuwa auren toufeeq na farko amma hajiya qarama ta aike mata da saqon basa gayyatarta. A sanda sagon ya isketa tana asibiti bata da lafiya,saita saki murmushi kawai tana girgiza kai. Ta sani tabbas addu’a babu abinda ya kaita kaif,ta jima ta fahimtar wata muguwar shakkarta da tsoronta ya shigi hajiya qarama,gamuwarsu kuma shine abu na qarshe da bataso. Ciwonta shi ya hanata zuwa bawai barazanar banza da wofi ta hajiy qarama ba,ta barwa ranta akwai lokaci na gaba,akwai kuma dama ta gaba,don tana ji a jikinta dama lokaci yayi da zata tabbatarwa da fauziyya yaranta data bar mata,ta bar mata su raino ne kawai,ta gama yanzun kuma zata karbi ajiyarta.
Sanda taji matar toufeeq ta haihu sai taji kowacce soyayya tata ta tattara akan FADEELA, tun tana jaririyarta har kawo shekarun da take kai a yanzu,sai taji tamkar itace ta yiwa nadeeya qanwa. Wata iriyar soyayya ce da bata boyuwa sam sam,wannan ya sanya hajiya qarama karkade makaman yaqinta data binne,ta kuma tabbatarwa kanta lokaci yayi da zata dawwamar da hajiya qarama cikin toro firgici da kuma zulumi
_wannan kenan_*
_sauran warwarar lamuran suna nan a gaba kadan zakuji komai filla filla_*
“sauran duka abinda fauziyya ta aikatawa rayuwata data su moha wanda idanu basa iya gani ita daya ta sani,sai kuma ubangijin sama da qasa,wanda idan yaso bayyana komai zai bayyana shi ba tare da wani jinkiri ba,wannan itace fauziyya,wanann itace hajiya qarama, kina tunanin akwai yanayin da zaizo wanda zai sanya na manta wacece ita?,na baki goyon baya dari bisa dari ki fita da fadeela,ba’asan abinda Allah ya hukunta ba,zama ba shine mafita ba tunda har akwai chance na yiwuwar warkewarta” gaba daya jikin säahar ya gama yin sanyi,duk gwiwarta ta mutu,cikin ranta tsoron Allah yana sake kamata,ashe ire irensu adam da momee suna da yawa a duniya? ‚ashe har yanzu mutane basa ji a jikinsu bisa yarda da imanin akwai ranar sakamako?,a yanzun bata ko shakka ko kokwanto,hajiya qarama zata iya aikata komai ma,sannan qarfinta ya karkata dari bisa dari akan sanya hannunta da ta’azzarar ciwon fadeela,ta sake imanin akwai wata boyayyar manufa tata data sanya take matsa qaimi akan duk wanda yace zaiyi maganar a yiwa fadeela aiki,ita ta cusa toro da fargabar surgery na fadeela a zuciyar mahaifinta,hakan na nufin shi dinma yana kan wani TARKO nata ne kenan ba tare da ya sani ba?. A karon farko wani tausayinsa ya sauka ya lullube zuciyarta, idanunta da suketa zub da qwalla
suka saka tara sabon hawaye tana jin radadinsu dikin
idanunta,da gasken gaske maji taga rayuwa,ta hadiyi
abinda ba kowacce maca ce zata iya hadiyarsa ba
“Ki ajjiyemin account number dinki, zan saka miki duk iya
adadin abinda zaku kashe da wanda zaku buqata,wacceqasa ce?”