TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“‘Baki yarda da gargadin dana yi miki ba?” Duk da zuciyarta ta qone sosai da kalar rungumar da ya yiwa sãahar din wanda ita daya tasan gardinta da dadinta, da
kuma sirrin dake tattare da wannan ingarman girjin nasa
data jima tana kewa,ta kuma gaza samun
kwatankwacinsa acan inda take harin
“Babu me rabani da kai sai Allah moha….. you are mine
forever” cikin nutsuwa ya dauke kallonsa daga
kanta,yasa hannu daya ya jawowa sãahar kujera ya
zaunar da ita a kai
“‘Huta a nan” ya fada cikin kulawar da sai da Ameesha
taji kamar numfashinta zaiyi skipping na wasu daqiqu.
Tasan toufeeg ciki da bai fiye da kowa,soyayyarsa
kulawarsa da tsantsar iya ririta mace wani abune da ta
gama lalube daga gurin kaffff mazan data hadu dasu
bata samu wanda yake da koda rabin rabinsa baya
tattara abubuwa masu yawan da sai an tara maza dari
ba’a samu qwaya daya rak irinsa ba.
Wayar da ake kiran security kawai ya danna ya koma
ya tsaya kusa da sãahar kamar wanda yake bata kariya
“Inason ka bani dama mu fahimei juna, nayi maka kuma
bayani mu yafewa juna na dawo na kula da ‘yata” runtse
ido yayi,ju yayi kaman ta soka masa wuqa a qahon
zuciyarsa,har bayason ta furta fadeela diyarta ce.
Bazai iya bata yawun bakinsa ma a kanta ba sai yaja waya yayi kira zuwa wajen saima
“Come in” ya fada a kausashe yana ajjiye wayar saima da security uku suka shigo, mata biyu namiji daya
Migewa yayi sosai iyakar tsahonsa yana dubansu,hatta säahar satar kallonsa take ta qasan ido,yadda lokaci daya ya koma Muhammad toufeeq jarma din data sani farkon haduwarta dashi, kaman ba shine yanzun nan ya gama karyar da wuya da murya a gareta ba
“Who allowed that women to enter?” Kallon kallo aka fara a tsakaninsu,kowa yana tsoron magana yana kuma tsoron gaddarar yau ta fada kansa ta kora daga aiki, duk da cewa tunda ya dawo din ko ma’aikaci dava bai kora ba.
“We are sorry sir, don Allah, bamusan bakason ta shigo ba” daya daga cikin matan tayi qarfin halin fada zuciya a karye
“Take her outside, and daga yau,idan na sake ganin gilmawar fuskarta cikin kamfanin nan ku tabbatar kun rasa aikinku” yana kaiwa garshe suka cafketa su biyun,don kuwa ba zata jaza musu asara ba,don kaf fadin kano dama Nigeria basajin akwai company da zasu samu me dadin aiki da kuma albashi me tsoka wanda yayi kamanceceniya da kamfanin MT JARMA.
“Ni ka wulaganta haka?” Abinda ta iya fadi kenan saboda tuni suka garasa yin waje da ita. Sai a sannan ya waiwayo ga saima ,wadda kallon idanunsa kadai ya sanyata taji kamar zata saki fitsari a wandonta
“You are fired” ya fada kansa tsaye. Ya jima yanason rabuwa da zaman yarinyar cikin office dinsa,amma ya rasa da wanne irin laifi zai kamata,sai yanzun da wannan dalilin yazo.
“Nan din ba Bar bane ko club da zaki dinga barin mata anyhow suna shigo min,bayan kin sani tare muke aiki da iyalina a ciki” yayi mata bayanin yana juya baya ba tare dava dubeta ba. Kuka ne ya hanata cewa komai, kawai saita juva da gudu gudu ta fice saboda ta gama tozarta tako ina a gaban idanun matar da take bala’in jin zafinta da tsananin kishinta,wanda ita sam saiman bata cikin damuwarta a rayuwa.
[28/09, 9:21 am] +234 903 576 5837: “HUGUMA*
_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 38
Tunda ya shaida mata ta daina fita company ya
zamana kamar gaba ita ta kaita. Gaba daya tayi qaura
daga sashensa ta koma dakin fadeela ta tattara
hankalinta akan yarinyar, gefe guda kuma tana soma
musu shirin fita asibiti ita da fadeelan ba tare da kowa ya sani ba.
Cikin ilkinsa ya fara jin rashin dadin sassan gaba
daya,a hankali ya fara taba ruhi da zuciyarsa,tun yana
tunanin ba komai bane, sabo ne kawai da hausawa ke
fadin turken wawa ne, har ya karanci lamarin ya fara zarta haka. A hankali ya fara rasa baccinsa saidai ya yita juyi saman gadon yana tuna sweet moment din nan,wanda yabar masa wani irin tunani me yawan gaske da kuma dadi da sanyaya zukata.
*******Shi daya ne zaune a falonsu, sai tarin ayyukan da suka sanyashi a gaba,wanda gaba daya sam sam baya jin dadinsu,yana yinsu ne bisa tilas. Gefe daga kuma abinda ya faru dazun tsakaninsa da meenal ke dawo masa,yarinyar ta koma masa tamkar wata zautacciya,tun tana bashi dariya da mamaki abun har ya fara qureshi, bata kunyar fadi masa komai a gaban kowa, ko a dazu sai da yayi kamar zai mammareta ya samu ta fita a sashen. Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye aikin da yakeyi din,jikin kujerar ya koma ya jingina yana dan lumshe idanunsa, babu laifin wadda yake gani sai nata, itakam wai kamar babu zuciya a qirjinta?, da gaske bata damu da al’amuransa ba,bata kishinsa haka yana nufin bata sonshi fa kenan. Ya baiwa kansa da kansa wannan amsar, abinda ya sanyashi sakin ajiyar zuciya me nauyin.
Fadeela ce tayi sallama ta shigo,ya daga kai yana duban yarinyar sai ya saki murmushi. Da gaske qiba takeyi abinta,abinda suka debe tsammani kwata kwata daga shi,sun dauka jikinta ne a haka.
Da sassarfa ta iso gareshi, ta fada saman cinyarsa tana kiran sunansa, hancinsa ya shaqi wani daddadan qamshi daga jikin yarinyar
“Ya akayi kika fito at this time haka? bakiga dare ya fara ba?” Juyi tayi a jikinsa
“Ko aunty N batasan na fito bafa?, hmmm cewa tayi itama dare yayi tunda munyi shirin zamu kwanta, kaj ma har turarenta ta shafa min” ido ya lumshe ya bude,yana jin dadin qamshin qwarai, zuciyarsa ta motsa shi qwarai,sai yaji bazai iya jurewa ba,don haka ya miqe yana cewa ina zuwa
Dakinsa ya shiga ya dauki wayarsa ya saka slippers sannan ya kama hannun fadeela suka fito Sassansu suka nufa kai tsaye idanunsa suka sauka a sashen hajilya qarama,yau kwana biyu kenan baiji motsinta ba duka kwanakin ya gaza takawa sassanta ya gaidata kamar yadda ya saba, haka kawai yakejin kamar an cire hakan fit daga zuciyarsa, sake tunawa yayi da kiran da nadeeya tayi masa dazu tana shaida masa,taji hajiyan na magana cikin waya,gobe yinin bikin qawarta, kuma kamar a can zasu wuni. Kansa ya dauke daga gurin,cikin kamewar nan tasa yayi sallama cikin falonsu nadeeya
Tun bai gama yin sallamar ba ba kuma tare data daga kai ta dubeshi ba gabanta yayi wani irin faduwa, kafiya da taurin kanta ya sanya taqi daga kai ta Kalleshi,sai taci gaba da sabgarta. Idanunsa a kanta har ya qaraso falon. Nadeeya ce ta fara gaidashi, ya amsa yans miqa mata hannun fadeela tare da yi mata alamar su tashi a gun lokacin yana gaisawa da baba ramatu.
Sai a sanann ta dan daga kai ba tare data kalli sashen da yake ba tace
“‘Barka da dare, ina yini?” Sai ta mige da nufin barin gurin
“Inda ban wuni ba zaki ganni?, dawo ki zauna” ya fada da husky voice dinsa. Haka kawai jikinta taji ya mace mata,sautin muryarsa ya nuna a dakensa yake, kamar sautin da ta sani lokacin yana MT JARMA dinsa na asali.
“Zaman me kikeyi a nan?” Ya jefa mata tambayar kai tsaye yana soke hannuwansa cikin aljihun wandonsa, tambayar ta sanyata daga kai abisa dole ta dubeshi, sai taji bata da zarrar ci gaba da kallon nasa
“Kula da fadeela” ta bashi amsa tana kau da kai,don ta fuskanci izza ce sosai yau din akan fuskarsa. Kai ya girgiza, bayason yayi fushi wani me yawa yayi gogarin dai daita muryarsa
“Ki fidda komai naki kizo ki wuce part dinki,can din shine gidanki ba nan ba,karki bari na maimaita miki hakan,just five minutes na baki” daga haka ya wuce ciki. A daki ya samesu ita da nadeeya. Wani kallo ya jefawa nadeeya da ya sanyata shiga taitayinta