Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“Kina da wani matsala ne?”
Ya tambaya.
“A’a amma don Allah ina so zan yi waya da su Jaddah yau sati biyu kenan rabon da in ji muryarta”
Ta karashe tana Kallonshi da idanun baccin ta waenda suka kara girma da haske ba kaman na normal wasu mutanen ba da in sun tashi idanunsu yayi ja.
Wayanshi ɗaya ya fitar daga aljihunshi fara sol design ne da bata taɓa gani ba don ba iPhone bane ba kuma dangin su tekno bane.
“Yanzu yayi sassafe da ƙira, anjima se ki ƙira su”
Hannu tasa garin saurin karɓa hannayensu suka shafi na juna, duk ɗaga kai suka yi suna kallon junansu kan ya ɗauke nashi yana furta
“saura ki kira waenda basu dace ba ki ga ikon Allah”
Yana kai nan ya juya ya fice.
Baki ta karkace tana tuna su waye ne basu dace ba? Kwafa tayi su sakina ne kilan yake nufi, ajiye wayan tayi taje tayi alwala ta zo tayi sallah.
Bayan ta idar ta koma ta kwanta se seven ta tashi ta fara gyaran ɗakinta tana gamawa taje tayi wanka ta shirya cikin wani Hot red top da black wando ta ɗaura black ɗan kwali, bakinta ta sanyawa red lipstick se tayi wani irin kyau, kwalli ta zana a idanunta kan ta ɗauko wayan ta zo kan kujera ta zauna.
Sliding tayi se wani hotonshi hadadde ya bayyana, sanye yake da kayan aikinshi cikakke yayi wani irin kyau gashin kanshi na sheki yana dariya ne tsaye a matakalar jirgi aka ɗauke shi, kurawa hoton idanu tayi na mintuna masu yawa kan ta sauke ajiyar zuciya tana shiga call logs.
Bata san da me yayi saving number ɗin jadda ba se kawai ta shigar da numbobin tunda tana dasu a kai.
“Jaddah na”
Ta faɗa bayan an ɗaga wayan ko sallama bata yi ba.
Jidda da ita ma muryarta ya bayyana jin daaɗin ta da jin muryar Fauzan tace
“Na’am Fauza ta ya kike? Ya gidanki?”
Shagwabewa tayi tana cewa
“shine ko kewata baki yi ba ko Jaddah”
Jaddah tace
“na isa ban yi kewar baki abun magana ba? Ai ba karamin kewanki nayi ba babu me sakani magana da shari’a, babu me nemo faɗa in tare, babu wacce kullum ke sakani kumbiya kumbiya idan professor ya aiko nemanta”
Dariya Fauxa tayi tana jin tayi missing old life ɗinta, rayuwa fa kenan! Waye ze yarda yanzu Fauxa tayi sati biyu bata nemi faɗa ba, ai da a da ɗinta ne ko Fatima bata nemeta ba wallahi ita se tayi yadda tayi ta nemeta faɗa, amma gani take yanzu ta wuce level ɗin sede in an nemeta a samu.
“Jaddah to meyasa bakya nemana?”
Ta faɗa tana tura baki.
“Kullum sede wannan me katon kan yace min baya gida ko kin yi bacci…”
Hannunta ɗaya ta ɗan sa baki tare da zaro idanu tace
“khaihh Jaddah Ya Faizan ɗinne me katon kai? Wlh kanshi daidai ne”
Salati Jaddah ta ɗauka muryarta cike da farin ciki da dariya tace
“innalillahi.. Fauziyya yau ke kike karbawa Faizan faɗa? Azzalumin?”
Da sauri ta katse wayan kunyar duniya na kamata, me ya kaita? Wlh ta ma rasa ya aka yi tayi wannan subutar bakin, ai se ta shiga bakin duniya in dae Jaddah ce.
Jaddah kuwa a ɓangarenta har sujada tayi na jin daaɗi, ko basu zama kaman yadda take so ba alamu sun nuna lamuransu akwai haske, da Faizan na cutar da ita ta tabbatar ita ce ma zata fara kawo sukarshi yau wace rana!
Sake kiran layin tayi da kyar Fauziyya ta ɗauka..
“Eyyaa Jaddah kewa!”
Ta fara kawo maganan dake ranta.
“Ina jin kaɗaici da kewa sossai, babu inda nake zuwa babu wadda ke zuwa guna banda waya bare in dinga jin muryarku, jadda ko Ya fadyaa da kika ce zasu zo basu zo ba har yau”
Jaddah tace
“haka aure dama ya gada barin ma a wuri me nisa, kiyi hakuri zan mishi magana ko wayan ne se ya saya miki ai ba wani matsala kuma bayan wannan ko?”
Kai ta gyaɗa tace
“babu”
“Ina Fatima kwana biyu itama bamu gaisa ba”
Tace
“Ina ga ta tafi school”
Hira sossai suka yi jadda tayi ta faɗa mata abubuwan da suke faruwa a gidan, wadda ya mata ta dara wadda be mata ba ta tofa albarkacin bakinta wani kuma tayi Kwafa, barin ma su ya Farhan kam.
Da kyar suka yi sallama don har katin Jaddah ya kare ta sake kira da wayan Faizan ɗin.
Bayan ta sauke wayan fuskanta cike da annashuwa ta shigar da layin Mammi.
“FIRST LOVE”
Sunan da taga yayi saving kenan da emojis ɗin heart, murmushi ta saki tana tuna nata uwar wadda basu taɓa magana ba tunda ta zo.
Bayan mammi ta ɗauka suka gaisa take tambayarta kafanta tace
“Fauziyya kafafun nan se godiyar Allah amma kam da abunda yake nema”
Fauziyya bata gane zancen ba tayi mata Adu’ar samun lafiya, bugan cikinta mammi tayi tayi don taji ko Faizan ɗin na mata wani abu sai de ko ɗaya bata kawo wani laifinshi ba don be matan ba, shakuwa ne dama chan babu tsakaninsu, zaluntarta da ya kan yi in ta mishi abu kuma ya daina tunda bata mishi koman ba.
Daga karshe da dabarun zama da miji da kuma nasihu mammi tayi ta mata kuma tana ɗauka wannan karo kam har tana mamakin kanta.
Bayan sun gama ta kira Ammi..
“Assalamu Alaikum Ammi”
Fauza ta faɗa bayan Ammi ta ɗauki call ɗin.
“Wa’alaikumussalam warahmatullah Fauziyya ke ce?”
Shiru tayi jin muryar Ammin nata babu ɗauki sossai kaman yadda muryar jadda da mammi suka bayyana mata kewanta da suka yi tace
“ni ce Ammi, kuna lafiya? Ya baba?”
Ta amsa da
“lafiya kalau ya gidan naki? Fatan dae baki bari ana hawa kanki kaman yadda kike da?”
Meyasa kowa ke mata nasiha ta zauna lafiya da mijinta amma mahaifiyarta kuma na shirin kawo rabuwar hankalinta?
“Ammi ai babu abunda suke min, muna zaune lafiya”
“mene? Ashe dama karyar kiyayya kike yiwa Faizan ɗin kenan, na tabbatar shi kuma a wurinshi ba haka take ba don kiyayyar namiji bata taɓa gushewa, kuma bata sauyawa, kiyi tunani dae… Sannan ki sani mijinki ba ke kaɗai ba har ni ba ƙaunata yake ba ke hatta mahaifinki don gani yake mahaifinki kusan rabi da kwatar dukiyarshi na Mahaifinsu ne shiyasa yanzu yake saka idanu akan harkokin business na babanki fiye da yadda yake sakawa Faraj da ya fara kula da na babansu”
Shiru tayi cikin dan nazari kan tace
“Ammi wannan duk ba wani abu bane, kilan ba yadda kike tunani bane don na san dukkaninmu da Baba Alhj da Baba prof duk iyaye muka ɗaukesu kuma matsayin abu guda babu banbanci, sannan Ammi ai maganan yaya Faizan baya kaunarki tun da nake na san yana zuwa gaishe ki amma baki taɓa buɗe baki kin amsa ba kuma har yau har gobe kenan be tsane ki b…..”
“Rufe min baki, ina nuna miki gabas kina yamma… Ke kika sani”
Tana kai nan ta kashe wayan..
Da idanu tabi wayan cikin mamakin Amminta, ta jima sossai tana nazari dayawa daga cikin ɗabi’un Ammin nata sede ta rasa a wani mataki ko matsayi zata ɗaura shi.
Baba prof ta kira shima yayi farin cikin jin tana cikin ƙoshin lafiya ya kuma yi mata albishir da result ɗinta na neco ya fito kuma yayi kyau don har yayiwa Faizan maganan yi mata registeration na jamb.
Taji daaɗi sossai tayi ta godiya da Adu’a ga baban, nasiha ya sake mata ya kuma gargadeta da Adu’a kaman yadda ya bata wani takarda da ke ɗauke da Adu’o’i masu yawa ya kuma umurceta da ta lazimcesu kuma tana yi ɗin sossai.
Bayan sun gama ta kira babanta shima ya ji daaɗin jinta lafiya ƙalau Dukda kullum a tsorace yake kar ta shukawa Faizan abunda ze zama silar tsinkewar zumuncinsu, idan har ze ga wayan Faizan se gabanshi ya faɗi da Tunanin ze ce mishi Fauza ta yi wani abun sede duk be ji ba, tun yana tsoracen yanzu har ya fara sakewa.