Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Tana matukar son gayu da class sede su gidansu ko ba hijab baka isa fita ba, a daren ta fara tsara yadda zata sauya rayuwarta zuwa ra’ayin kanta ba ra’ayin wasu ba, sallamar Faazila ya sa ta ɗago idanunta da suka sauya ta zuba mata, birkicewa yarinyar tayi don ta san sarai yanzu se Adda Fauxa ta mammake ta yadda take a harzuke ɗin nan.
“Me??? Kin zo kin wani yi min kerere kina kallona?”
Baya ta ja tace
“Mammi ce tace in kira ki”
Dauke idanunta tayi ba tare da ta amsa ba ta juya ta dauki hijab ɗinta ta saka tare da fitowa zuwa sashen Mammi, tana shirin shiga ɗakin Fatima na shirin fitowa da gayya ta bangaje ta har Seda tayi baya tana kallonta sede ko kallo bata ishi Fauxa ba ta wuce zuwa wurin Mammi tana daidaita fuskanta Gaisawa suka yi Mammi tace
“Fauxa zo don Allah kiyi min tofi a kafan nan”
A ladabce tace
“to Mammi”
A gabanta ta duƙa ta fara se Fatima ta shigo da bowl na fruits a hannunta ta ajiyewa Mammi ɗin tana cewa
“Mammi Adu’a ce ake yi?”
Mammi tace
“eh wlh jiya da ta min baki ji yadda na ji daaɗin kafafun ba”
A fakaice Fatima ta aika mata da wani kalar kallo tare da taɓe baki, ina Fauxa ta ma san tana yi, wai harara a duhu, bayan ta gama mata ta fice don bata jin magana in kuma ta zauna inuwa daya da Fatima karshe se Mammi ta raba faɗa.
Washegari a class bayan an tashi break ta kalli rahama tace
“am interested in ur way of life taya nima zan fara?”
Rahama da sakina suka yi wani ihu tare da tafawa suka ce
“welcome to the club babe”
Sakinah tace
“dama akwai wasu Zafafan dinkunan da zamu yi har ma mun yi placing order ɗin materials ɗin amma tunda zaki yi bari na sa dake”
Fauxa tace
“amma fa bani da kuɗi kun san gidanmu ba wani bada kudi ake banza banza ba”
Rahama tace
“don’t mind dear! anything for you precious ”
Sakina tace
“bare ma kwana biyu zaki fara rike wasu makudan kuɗin da se kin ji tsoro just chill babe”
Aiko gwada ta suka yi suka turawa tailor ɗin su, nan suka fara nuna mata mahaukatan dinkunan tana kallo cike da yabawa..
Iyaye ya kamata mu san cewa duk fushin ka da yaro ba kowacce kalma ya kamata ka furtawa ɗa cikin fushi ba domin baka san irin influence da zaka yiwa yaro ba idan har Allah ya amsa.
MAFARI
Dukda rashin son karatun Fauxa ta kasance mace mai son karance karance, hakan yasa bata rabo da littafi ko na turanci ne, babu kalar abunda bata karantawa hakan yasa abubuwa dayawa tana da masaniyar already aikata shi a fili ne kawai bata yi ba.
Wani irin kalar Juyawa rayuwar Fauxa yayi cikin lokaci kankani, idan tayi dressing se ka dauka ba Fauxan gidan baba prof bace, Fallin balaga ya buɗe rashin M ɗin ta se abunda ya karu ga rashin daukar raini, se neman tsokananta da yayi sauƙi sede fa ba shi ya hana kana ce mata Kule ta ce maka chass ba.
Abunda take yi shine tunda yanzu Sam Sam ba cika zuwa part ɗinsu tayi ba se idan zata gaida Ammi don baba Alhj ma ta manta rabon da su haɗu tunda ya ce baya kaunar ganin fuskanta ta gwammaci ta dinga wasan buya dashi.
Idan an tafi school daga an tashi break zata yi bribing gate man sbd su Rahama ma ba cika zuwa suke ba se once or twice in a week, zasu ɗauke ta a gate su tafi gidansu rahama inda wasu abubuwanta suke a nan zasu yi dressing ɗinsu na class su fice yawo, samari kuwa kaman kuda a kan Fauxa hakan yasa ta juya wannan ta waina wanchan ga yadda take sha musu kamshi kaman ƴar shugaban kasa, ɓarin kudi suke mata ba na wasa ba har ta mallaki iPhone 13pro na kanta kuma har gida take zuwa da abunta.
Ta chanza mayukanta gabaɗaya zuwa wasu organic masu tsananin tsada, na kafa daban na gashi daban na fuska kala kala, in ta wuce ka se ka jima kana jin kamshin designers perfumes na jikinta.
Aka ce akuyar ɗaure in ta samu sake Habaaa, har Sakina da half rayuwarta outside tayi wani lokacin ta kan mutu da kalar gayun Fauxa sede a gida har yanzu babu wadda yayi noticing ana getting to five months.
Sau ɗaya fa’iza ta taɓa mata maganan rashin zamanta aji se da ta ja mata katoton layi tayi mata fata fata wadda har ta Haɗa da mahaifiyarta hakan yasa fa’iza dauke kai daga rayuwar ƴar uwar tata.
Se dab za’a tashi school take dawowa su koma tare da ƴan gida, wayanta kuwa kullum a ɓoye yake kasancewar ɗakin da take a sashen Jaddah ita kaɗai ce, yanzu damuwanta yadda zata fara fitan dare sbd ana kawo mata cikas sossai da ganin ƙarancin wayewarta sbd rashin zuwa night parties ɗin nan.
Zama tayi ta tsara yadda zata ke fita abunta bayan isha zuwa asuba, randa ta fara gwada luck ɗin ta Dukda yadda take a tsorace kuma cikin bugawar zuciya haka ta saka dogon hijab ɗinta bayan ta yi wanka ta gama duk shafe shafenta, fuskanta da ba ko Digon powder se wani ɗaukar hankali yake sbd kyaun da ta kara na musamman, wurin Jaddah ta je tace
“Jaddah yau wurin Mammi zan kwana”
Jaddah tace
“yau kuma ni aka yiwa Hijira kenan, to se da safe”
Tana murmushi tace
“Allah ya bamu alkhairi”
Sashen Mammi tayi ta gaisheta, tace
“Mammi bari na tofa miki Adu’ar nan”
Kasancewar kullum kaman ka’ida duk dare ta kan je ta tofa mata adu’o’in hakanan kan su wuce school kuma Alhamdulillah sossai Mammi take jin daaɗin kafan kaunar Fauxa sbd Allah na ninkuwa a zuciyarta, kuma duk wadda ya san Mammi se ya ji zancen Fauxa a bakinta sbd irin gudumawar da Fauxa ke bayarwa idan Mammi ɗin ba lafiya.
Seda ta shafa mata adu’ar kan ta mike ta nufo hanyar gate, Allah ya taimake ta daidai lokacin baba prof yake baiwa Lawal kuɗi ya amso mishi credit, a jikin flowers ta buya har Seda ya wuce ciki daga masallacin da shi se lokacin yake fitowa, Lawal kuwa yayi waje ta fito da sauri ta fice gabanta na dukan uku uku.
Wayanta ta fidda ta kira su Rahama suka zo da driver ɗinsu da shine yake yawo dasu dama suka wuce suna ihun ganinta at this time around.
Shiri suka yi suka wuce birthday party ɗin wani saurayin Rahama, wuri ne na manyan yara waenda iyayensu suke da kumbar susa, ado ne kala kala zaka gani da kalar dinkunan rashin kamun kai, kuɗi kuwa ba’a maganan adadin da aka zube don wannan party din musamman.
Fauxa ta ja hankalin matasa masu daloli dayawa a wurin kuma kowa so yake ta kula shi, sede fa in tana cikin ji da izzarta ko su Rahama shakkar mata magana suke, Fauxa ta riga ta zama hatsabibiya Dukda bata rabin abunda suke, su suna ɗan taɓa kayan maye hakanan su kan yi soyayyar shan minti sede ko ɗaya Fauxa bata yarda da wannan ba.
A nan wurin suka yi till down, gab asuba ta sa wani ya ɗauke ta suka nufi gida, Seda ta bari an shiga sallah kan ta shige da sauri, alwala ta ɗaura kawai ta nufi masallaci dayake ta chanza dressing ɗinta zuwa yadda ta fita, Jaddah dauka tayi ta makara a wurin Mammi tunda Mammi ba koyaushe take samun zuwa masallaci ba.
Ba se Fauxa ta samu abun yi ba, se ta kwana waje sau biyu ko sau uku a sati wadda hakan ya kara mata buɗewar idanu ba na wasa ba.
****
“Malam kwana biyar ne kawai Don Allah ka yarje mana ka taimaka ka Haɗa wannan plan din, in ba Fauxa ba zamu taɓa jin daaɗin wannan party ɗin ba”
Kallon Fauxa da tunda suka shigo bata ce komai ba yayi, yarinyar tana burgeshi tashen balaga ke dibar ta gashi Allah ya zuba mata sanyin kyau, ya jima yana bibiyarta tana wulakanta shi…