Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Misalta irin tashin hankalin da suka shiga a sannan ɓata lokaci ne, barin ma da suka fahimci a buge take, sossai jadda ke kuka abunda ya kara ɗaga hankulansu kenan.
Baba prof ne ya hana a taɓa lafiyanta, yace
“Aisha kamata ku je wurinki, karki bari kowa ya fahimci halin da take ciki zamu yi zama in an watse bukin nan, amma ko kofar parlor ban yarda ta taka ba”
Da kallon takaici da kyama kawai yake bin ta har Mammi ta cire hijab ɗinta ta rufe ta don se layi take yi a haka kuma duk wadda ya ganta se a ajiye alamar tambaya, ita kuma ta yafa mayafin kayan ta da ta ɗaura a kai ta rungumeta suka wuce cikin gida. Allah kaɗai ya san irin mazan da ta bi da irin surartan nan, haka dae babu daaɗin rai aka kira likita ya zo ya duba Baba Alhj da jikinshi ke neman yin tsanani ana gwadawa kuwa jininshi yayi mugun hawa.
Jadda ma jininta se da ya hau bata taɓa zato ko tsammanin hakan daga Fauza ba, yarinyar karama waye yayi influencing nata haka?
Rai babu daaɗi aka watse haka bukin auren ya rage armashi don abunda ya tunkaro su in basu yi da gaske ba akwai babbar matsala.
Haka mammi ta saka ta a gaba bayan ta kwantar da ita tana kallo hawaye na zuba mata, wani irin tausayin rayuwar yarinyar na rufe ta, me ta nema ta rasa? Menene ya tura ta ga wannan halaka haka daga gidan mutunci? Mammi ta hana kowa kusantar ɗakinta yayinda Ko motsi Fauxa bata yi ba se washegari da rana ya gama fita, amai da ciwon kai ya tasheta.
Mammi na zaune kan sallaya ta idar da wahala lokacin sha ɗaya taga tashinta da gudu zuwa bayi, da kallo ta bita har ta ɓace, yadda ta kwana bacci haka duka ahalinta suka kwana kan sallaya suna mata Adu’ar shiriya.
Ko da ta fito zata sake komawa ta kwanta mammi tace
“Fauziyya”
Ta amsa ba tare da ta iya ɗaga idanu ta kalleta ba.
“Koma ki watsa ruwan zafi”
Komawa tayi bayin, bata da wani tunani kuma da zata yi tunda abunda ya faru ya riga ya faru, kafin ta fuskance su ne take jin tsananin tsoro amma yanzu da bayan Kowa ya sani kunya ne ke ɗawainiya da ita.
Mammi da kanta ta aika aka ɗauko mata kaya, ta sa aka hada mata abinci aka kawo har ɗakin, sadda ta fito ta shirya mammi ta mata nuni da tray ɗin, haka ta janyo ta ci sbd yunwa dake dawainiya da ita, rama sallolin kanta tayi duk abubuwan nan bata yarda ta Haɗa idanu da mammi ba sbd kunya.
Bayan ta idar ta gaida mammi tana wasa da kasan hijab ɗin nata.
Mammi ta amsa kan tace
“Fauziyya”
“Na’am mammi”
“Fauziyya kin san irin rayuwar da kika jefa kanki kuwa?”
Kanta na ƙasa hawaye ya fara kwarara bisa fuskanta tace
“mammi Adu’a Zaku yi min, nima ban san me yake damuna ko meyasa nake fadawa halaka bayan na sani ba, wani lokacin kasa fahimtar kaina da rayuwa ta nake, chan kasan zuciyata bana jin daaɗin hanyar da na hau sai de wani zuciyar na tirsasani ƙarbar hakan ta wani fuska…”
Kuka ne ya ci karfinta.
Mammi ma hawayenta na tsananin tausayin Fauzan ta share, tace
“ɗauko Alqur’ani ki karanta Fauziyya”
Mikewa tayi tayi yadda mammi tace, tayi karatu har azahar suka yi salla tare, kan mammi ta sa ta sake kwanciya.
An yi walimar Fatima Dukda sun fahimci armashin auren ya ragu sossai sai de babu wadda ya san dalili washegari aka ɗaura aure aka yi saukar Qur’ani.
Ko kofar ɗaki kaman yadda Baba prof yayi umarni Fauza bata taka ba, ta ci abinci tayi ibada se tayi bacci, duk tunani ya fara cin karfinta ita yanzu ko wayanta bata san hannun da yake ba, taji mammi na maganar Amarya zasu kai wani sati kan su tare don haka daga washegarin ɗaurin auren mutane dayawa suka watse.
A daren Ammi ta zo ta sashen mammi daga bakin kofa ta tsaya tace
“ke Fauziyya! Tunda ba a nan aka binne cibiyarki ba ki tashi ki wuce mu tafi, tun aka fara hidimar nan neman duniya na yi miki babu wadda ya iya buɗe baki ya ce min ga inda kike? Meyasa ne ake nema se an tauye min hakkina a matsayinki na ƴata kaman yadda aka tauye min sauran hakkokin nawa? Me kuma aka ce kinyi wannan karo?”
Kanta ta ɗago tace
“Ammi kiyi hakuri”
Ammi ta aika mata da wani kallo tace
“ban gane ba? Kinga tashi mu tafi mayi maganar kaman kowacce uwa da ƴa a ɗaki”
Mammi tace
“baba prof yayi umarni akan ko kofa be amince ta taka ba har se ya neme ta”
Wani irin kallo Ammi ke mata
“wani ta kashe ko mene?”
“Wannan kuma shi zaki tambaya Ammin su”
Neman tada zaune tsaye take wai baba Alhj ya ki ce mata komai, Jaddah ta ƙi ce mata komai sannan yanzu zata zauna da yarinyar ta ace ba haka ba? Akwai wadda ya haifa mata ne..
Baba prof be so hankalin kowa ya dawo kan abun ba amma saida Ammi ta janyo hakan Dukda yadda Fauza ke hanata maganan.
A take kowa ya san akwai abu a ƙasa, hakan tasa ya kira meeting kawai.
Kowa da kowa har da Amarya ta hallara, babu wani bare duk mutanen gidan ne.
Kai tsaye ya buɗe taro da Adu’a kan ya fara magana akan jarabawar yana misalai da magabata akan dole Allah ze jarrabeka ta hanyar ‘ya’yayenka wani dukiya wani mata babu yadda babu kaman yadda mahaifin Annabi Yusuf annabi yaqub yake annabi amma ‘ya’yanshi suka so halaka ɗan uwansu, kaman yadda annabi nuhu yake annabin Allah amma ɗan shi ya fita yana saɓawa Allah har Allah ya halaka shi tare da sauran masu saɓo, misalai dae kala kala.
Daga karshe ya ɗaura da
“Ina so duka mu ɗauki Fauziyya as zakka, ba kuma wai zamu sakata a gaba da hantara da kyara da kuma duka bane, babu wadda ze ɗaura hannu a kanta da sunan duka idan har ka cika cikakken masoyinta da halakarta ka iya jefaka cikin alhini to ka tsaya mata akan sallaya ka rage mata bacci musamman iyayenta”
“Menene Fauziyyar tayi?”
Ammi ta jefa tambayar don ita duk waennan wa’azuzzuka sun ishe ta.
Baba prof yace
“mun zauna da Faizan ya faɗa min ganin da yayi mata a wani hotel a Abuja wadda kai tsaye ya faɗawa mahaifiyarshi ita kuma ta ƙi aminta sbd sanin da sa hannun makaranta aka tura Fauziyyar excursion Gombe, wannan kaɗai alamar tambaya ne don haka muka yi tattaki zuwa makarantar Allah ya sa abokina wadda shine mai makarantar ya zo musamman daga Maiduguri ɗaurin auren Faizan, anan muka tabbatar da manuplating malamin Fauziyya tayi yayi musu takardar bogi suka tafi Abuja saide be san me ya kaisu ba”
Babanta yayi salati ya sallamar yace
“yanzu Fauziyya a iya shekarun kin nan har kin san kiyi manuplating malami ya barki ki tafe watsewa uwa duniya? Bazaki kasheni ba Fauziyya…”
Baba prof yace
“Sulaiman karka manta duk abubuwan da nace kan mu fara tattaunawan nan, malamin karan kanshi na da laifi don da be yi abunda zata yi manuplating nashin ba da bata yi ba, shima nemanta ya so yi tayi recording ta juyar kanshi ga wayan da bamu san tana da shi ba hannun Faizan komai na ciki don a motar shi ta bari”
Da sauri ta ɗago ta kalleshi shi kam ba ta ita yake ba, kawai yana zaune ne don ya san abun ya shafe masoyanshi da kuma gidansu amma da don ta shine wallahi ko a jikinshi, sarai ya san Zubair drug dealer ne wadda EFFC da NDLEA sun sha kama shi su sake saboda ɗaurin gindin da yake dashi, ya shata mishi katoton layi ya kuma gargadeshi a wayan na Fauza da yake ta kira akan in har yana cin ƙasa to ya kiyayi na shuri.
“Fauziyya me ya kaiki Abuja?”
Jadda ce tayi maganan har muryarta na rawa.
Shiru tayi kanta ƙasa, wani tsawa da babanta ya daka mata yasa ta ɗago kowa idanunshi na kanta se ta nemi rikicewa..