Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Ita dae fadeela se dariya take yayinda Fauza ta shagwabe akan lallai lallai ita ba haka bane tana Haɗa ya Fadyaa da Ya fadeelah, sun sha hira kan suka yi sallama don ma what’sapp call ne da ta tabbatar ko biyar baze saura a wayan Ammin ba.
Anan kan stand ta bar mata ta wuce sashen Jaddah, kan ta shige ta hangi fitowanshi daga mota yana waya a natse yake tafiya yayi sashensu na ƴan maza, ta jima tsaye tana Kallonshi seda ya wuce kan ta juya itama ta shiga sashen, ɗakin Jaddah ta shiga suka ɗan yi hira kan taje ta kwanta bayan ta rufe kofan ta.
Washegari da safe ko karyawa bata yi ba ta dae yi wanka ta sanya wani cotton blue shiffon shirt da straight skirt baƙi se ta ɗaura black dan kwali a kanta, se kamshin khumras na sabon gyaran da Jaddah ke mata take zubawa, fitowa tayi ta shiga kitchen ta samu zaliha na yin kosai da koko, baki ta taɓe ta warware gyalen da ta ɗaura a kanta se ta yafa ta fice daga sashen.
Har ta nufi sashensu se ta juya ta nufi na mammi don tun shekaranjiya rabon da su haɗu ta aiko mata da kifi dafaffe ma da rana bata je godiya ba kuma kila abunda ta dafa se ya fi na jaddar nan daaɗi.
Da sallama ta shiga parlorn, Mammi na zaune tana karyawa itama maraba tayi mata fuskanta cike da fara’ar ganin surukar tata, zama tayi suka gaisa sossai kan mammi ta mata umarni ta isa akwai abincin a dining ta ci abin ta.
Tsam ta mike tayi dining ɗin ta diba kuwa me ɗan yawa ta fara ci a hankali.
Sam bata san mammi har ta gama ta mike ba ma, fitinannen kamshinshi da ya cika wurin ne ya sakata saurin ɗagowa se suka Haɗa idanu, da sauri ta ɗauke kanta ta mayar kan abincin ta da idanu ya bi abincin na seconds kan ya samu wuri ya zauna ya miƙe kafafunshi ya zuba mata idanu yana kallo.
Kasa cigaba da cin abincin tayi, se kawai ta miƙe da niyyar barin wurin kafa ya sa mata tayi gaba zata faɗi yayi hanzarin janyo hannunta se gata bisa kirjinshi, rungumeta yayi da kyau a cikin kunnenta ya raɗa..
“Ke kam baki san haƙuri bane Fauza? Pls kiyi hakuri mu koma gidan mu hakanan wallahi na miki alkawari ba zan ƙara yi miki komai ba idan har ba da yardar ki ba, am so sorry bisa duk abunda suka faru ki yafewa mijinki kin ji?”
Bata ce komai ba se kokarin tashi da take, ya kara matse ta cike da masifa ta fincike bata ce komai ba ta juya zata fita, she’s killing him da wannan shirun wallahi..
“I’m hungry ki sama min wani abu please”
Bata juya ba ta fice, sashensu taje suka gaisa da mammi kan ta koma sashen Jaddah, Jaddah na zaune a parlor ta mika mata wani cup da wani haɗi ciki karɓa tayi sbd yadda yaji madara da zuma ta zauna ta shanye tass ta ajiye kofin, Jaddah tace
“Fauza ki shiga kitchen ki sama ma mai gidanki wani abu duk abunda aka yi a sashukan biyu ba ci yake ba shima”
Baki ta tura tace
“me zaliha ke yi Jaddah?”
Jaddah ta mata dakuwa tana cewa
“zaki ci ƙaniyarki fa Fauziyya wai aka gayamiki zuba miki idanu da aka yi tsoron ki ake? Ki zauna kina Jawa mijinki aji mijin ma irin Faizan dake da matukar wahalar samu, wata macen na kyalla idanu ta kwace shi tsab ki zo kina min kuka wlh se na lahira ya fiki jin daaɗi, a kanki aka fara samun irin wanchan matsalar a da da se an dauko mu a ka a kaiwa miji a kullo kofa, to karki kiyaye ni kiga..”
Bakinta kaman ze taɓa gini ta miƙe ta wuce fuu zuwa kitchen girkin take sede ba da wani armashi ba, da gangan sbd ta san be son yaji kwata kwata tayi girkin da zallar attarugu ta saka a plate ta ɗaura a tray bayan ta rufe ta ɗauko ta fito ta ajiyewa Jaddah
“To wa ze kai mishi? Kin dae san Zaliha ta wuce kasuwa”
Sake ɗauka tayi Jaddah na kallonta har ta fice kan ta taɓe baki tace
“Zaku ji dashi dukkanku biyu wlh”
Don shi ya zo ya roki Jaddah da ta saka ta yi mishi girki please Allah yayi kewar taste ɗin abincin ta.
Da sallama ta tura ɗakinshi fitowanshi daga wanka kenan se lokacin ta tuna haduwar da suka yi a sashen Mammi da kananun kayan shan iska ne wando three quarter me taushi da kuma riga marar nauyi, ɗaure yake da towel iya kugu, saurin ɗauke kai tayi ta karasa gaban center table ta ajiye tray ɗin zata juya..
Sam baya so ta fice da sauri yace
“serve me please”
Dawowa tayi ta buɗe plate ɗin kawai ta sanya mishi spoon don ba’a wani coolar ta saka ba, ta wuce frigde ta dibo ruwa ta zo ta ajiye mishi daidai lokacin ya zauna ba tare da ya damu ya saka kaya ba Dukda Acn da yayi yawa a ɗakin zafi yake ji kasancewar damina kilan a samu ruwa zuwa jimawa don zafin yayi yawa.
Se ta tsinci kanta da kasa tafiya ta tsaya tana kallon abincin gabanta na faɗuwa, don ta san yadda yaji yake wahalar dashi.
“Yaaa…ya”
Da sauri ya ɗaga kai ya kalleta tace
“Karka ci”
Ta matso tana shirin ɗauke plate ɗin ya riƙe hannun ya kalleta sossai kan ya kalli abincin se ya lumshe idanu kan ya kai baki, wani irin radadin yajin da ya ziyarci kwanyarshi ne ya saka shi saurin kallonta ita kuma ta runtse idanu tana jin wani tashin hankali na bijiro mata.
“Idan har wannan shine hukunci na precious pearl na karɓa, zan ci har se kin ji hukuncin ya miki daidai da muradinki”
Yana kai nan ya cigaba da ci abunshi Dukda yadda yake jin kaman harshen shi ze tsinke, idanunshi a take suka rine jijiyoyinshi suka tattashi, a hannunta take jin yadda jikinshi ya ɗauki rawa don Allah yayi shi yaji ba abunshi ba gashi yana da masifaffen ulcer..
Ze kai cokali na uku tari ya sarƙe shi, numfashin shi na fita babu daaɗi hakan kuma ya sake diba ze ci da sauri ta buge spoon ɗin tana zub da hawaye…
Kokarin ɗaukar spoon ɗin yake tayi saurin jan gabaɗaya table ɗin ta maye gurbin table ɗin gwiwowinta a ƙasa ta ɗauko ruwa ta mika mishi a rikice tana cewa ya sha yana ture hannunta.
Tuna yadda suke tafe cikin ruwa ya yafa mata designer suede ɗinshi yana kare mata ruwa shi kuma ruwan na dukanshi amma kaman be damu ba har zuwa cikin gida tayi, ta kuma tuna yadda ya kula da ita a sadda bata da lafiya Dukda a lokacin ranshi a ɓace yake da ita, ta tuna yadda a duk sadda take neman taimako shine mutum na farko dake kawo mata ɗauki he’s her life savior, meyasa don ya mata laifi cikin rashin sani zata azabtar dashi ta wannan hanya, shin shi kaɗai ne yayi mata irin wannan zargi cikin rashin sani? Meyasa bata hukunta kowa ba se shi…
Faɗawa jikinshi tayi tana kuka tana cewa wlh ta hakura ta yafe mai yayi haƙuri, kankameta yayi idanunshi a runtse ganin har lokacin ruwan yaki ya dawo dashi daidai kawai tayi saurin haɗe bakinsu, kaman jira yake ya cabke yana jin his life depend on that yana saketa yaji ze ji, sanyin tongue ɗinta na ratsa dukkan sassan jikinshi a hankali ya fara dawowa hayyacinshi…
****
Kwano me ɗauke da tuwon datsan masara da wani bakin miyan kuka banda daddawa da gishiri babu abunda ke ciki da aka dangwalar musu ya saka Fatima rushewa da kuka tana kallon Aunty da fuskanta ke a kumbure sbd ciwon kai da ya matsanta mata tunda aka yi wannan hatsari tana cewa
“Wallahi na gaji Aunty, na gaji da wannan cimar dube ni fa, dubi yadda jikina ya fara komawa tsabar yunwa da talauci, ni dae Allah ki san yadda zaki yi dani ki kwatanta min inda zan je na samu maganin damuwata…”
“Fatima gwara dake kina iya cin abincin dube ni, babu abunda ke shiga cikina, bakya tausayina? Dubi yadda fuskata ta kumbure baki maganan muje asibiti a duba ni se wani maganan Faizan chan…”
Aunty ta faɗa a wahalce