Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Takwas*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA❤️**
Karshe dae Aunty bata iya bacci ba seda Baba Alhj ya danne mata goshin aka shafa man zafi, takaici ya hana shi cewa komai, ya aika a kira mishi Faozia ɗin aka tarar bata nan sede Jaddah bata ce bata nan ba kawai cewa tayi a ce tayi bacci Dukda bata san wani laifin ta sake aikatawa ba.
Ita kuwa Faozia tana zuwa wurin Mammi ta shagwaɓe tana faɗamata abunda ya faru, Mammi tace
“Gaskiya Farhan da Faraj basu kyauta ba ai da lafiyata ƙalau babu wadda zan bari ya taɓa ki su da suke gantalinsu akwai wadda ya hana su ne?”
Cikin jin daaɗin goyon bayan da aka bata tace
“ai shine”
Mammi tace
“Faozia am ki rage nemarwa kanki magana kin ji? Bana son yadda kowa ya buɗe baki yace Faozia, Faozia ɗin nan wallahi har raina bana jin daaɗi”
Fauziyya tace
“In shaa Allahu Mammi bazan sake ba”
Mammi tayi murmushi Dukda ta san labarin kanzon kurege ne kullum haka take cewa baze hana gobe tana fita ta jajiɓo wani tashin hankalin ba.
Ƙin zuwa wurin jadda tayi wai tana fushi a lokacin da su Farhan ke bugunta jadda bata zo ta karɓeta ba kuma ta tabbatar sarai tana ji.
Asiya mammi ta kira akan ta zo ta dubo wa Fauzan abunda zata ci.
Faozia tayi Charab tace
“Mammi bari na shiga kitchen ɗin da kaina”
Har ta fita ta dawo tace
“ke fa Mammi kin ci abinci?”
Tace
“Ina ga Tea zan sha Faozia kubewa suka girka a gidan ni kuma ba so nake ba, je kiyi abunda zaki yi ke kam”
Kitchen ta wuce, Asiya dake zaune a parlorn ta bita da harara ko Kulata Faozia bata yi ba don ta jima da sanin Asiya irin mutanen nan ne da suke bari hassadar wani ya gurɓata musu rayuwa, ba tun yau ba ta fahimci Asiya bata ƙaunar ta shiyasa itama bata shiga harkarta.
Hijab ɗinta ta ajiye ta fara dube dube a kitchen ɗin Seda ta fidda duk abunda zata bukata na aikin da take son yi kan ta fara aikin, Yawan bin kawaye da take har ana dukanta duk akan girki ne tana matukar kaunar girki babu abunda yake bata nishaɗi a rayuwa irin ta ganta a katon kitchen tana girke girke, idan kaga Faozia a school ta natsu to kallon recipes take a wayan kawaye don gidansu kam ba’a abubuwan zamanin nan.
Shawarma da suka yi ɗazu har sanadiyar shi aka Chasa ta tayi guda biyu na beef, banda kamshi babu abunda ke tashi a kitchen ɗin tana yin Shawarmanta kuwa tana biski ba me yawa tayi ba ɗan kaɗan ne sosai da kidney sauce, fancy plate ta ɗauka ta zuba biskin daga gefe in a stylish way kan ta zuba kidney sauce ɗin shima a gefe ta watsa parsley a kai kaɗan yadda ya bada wani garnish na burgewa.
Shawarmanta guda biyu ta ɗauko suma ta saka su a plate ta ɗaura Duka a tray ta ɗauko ruwa masu rangwamen sanyi tare da daukawa kanta wani mango drinks ta nufi ɗakin Mammi, tana zuwa ta ajiye tray ɗin tace
“Mammi guess what I made?”
Mammi tana murmushi tace
“Ina zan sani ina zaune a nan na dae ji kamshi na tashi kuma duk hasashe na na rasa gane menene..”
Buɗe plate ɗin biski da kidney sauce tayi tana dariya cike da jin daaɗi tace
“Tadaaa..!”
Tana dariya sossai wadda ya saka Mammi murmushi tace
“Masha Allah, Kice daughter na na shirin zama Chef eyee a ina kika koyi irin wannan delicious ɗin?”
Shagwaɓe fuska tayi tace
“ba irin su bane na bi Zee koyo a gidansu kuma da nisa shine ban dawo da wuri ba su ya Farhan suka bugeni ba..!”
Mammi tace
“masha Allah, am impressed gaskiya karki damu in shaa Allah na miki Alkawari da kaina zan saka ki a catering school ƴata ta zama Chef Faoza..”
Murna Faozia ta fara harda tsalle, Mammi na ta dariya Faozia is such a wonderful child da zama da ita kaɗai ka iya saka ka farin ciki she’s so lively in har ka san yadda zaka tafi da ita, Mammi ta matsarwa plate ɗin tace
“bismillah Mammi”
“thank you bitty”
Spoon ta sa ta fara ci tana yabon hannun na Fauza a girki, itama Shawarmanta taci tas ta cinye ta sha mango juice ɗin kan ta tattare wurin ta fitar, da taimakonta Mammi taje toilet tayi duk wani abunda zata yi ta dawo da alwala, ita ta taimaka mata har ta kwanta…
Tana shirin shiga wanka se taji sallaman Baba Prof hijab ta saka, Seda ya shigo ta gaishe shi ya amsa da kulawa kan ta fice ta bar su da Mammi, ɗakin yaya farida da babu abunda Mammi ta taɓa ciki ta shiga, akan gyara akai akai hakan yasa ta nufi toilet ɗinta tayi wanka, bayan ta fito ta duba wardrobe ɗinta ta kuwa samu kayan bacci sabo dal a Leda Dukda ya ɗan yi mata yawa haka ta saka.
Seda ta ɓata lokaci mai yawa kan ta fito ta koma ɗakin Mammi ta samu Baba prof ya tafi, Har zata juya Mammi tace
“Fauza”
Dawowa tayi tana cewa
“Na’am Mammi ko kina bukatar wani abu ne?”
Mammi tace
“A’a ki hau gado ki kwanta, kiyi Adu’a kin ji?”
Kai ta gyaɗa tare da rage musu hasken ɗakin ta hau gadon na Mammi ta kwanta tare da jan bargo.
Chan cikin dare Fauza ta tashi saboda fitsarin da ya matse ta se ta hangi Mammi zaune dafe da kai, da sauri ta mike tace
“Mammi!”
Mammi bata ɗago ba, sauƙa tayi ta nufe ta ta duƙa a gabanta tace
“Mammi lafiya? Baki jin daaɗi ne?”
Tayi maganan hawaye na cika mata idanu Mammi ta ɗago idanunta duk sun sauya tace
“Na kasa bacci Fauxa kafana se harbawa yake”
Hawaye ne ya zubowa Fauxa cikin tausayin Mammi, zama tayi gaban kafan tace
“bari na miki Adu’a Mammi”
Bismillah tayi sau Uku kan ta ɗaura da
بِسْمِ الله! بسم لله!! بسم الله!!!
“أَعُوذُ بِااللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شِّرِ مَا أَجِدُ وَأُهـَٰذِر”
“Bismillah! Bismillah!! Bismillah!!!
Auzibillahi bi qudratihi min sharri ma ajidu wa uhadhir”.
Kafa bakwai ta shafa mata a kafan ta kara da qulhuwa uku, falaki uku, da nasi uku.
Manzon Allah yace babu wani ciwon dake damunka da zaka dafa wurin ka karanta wannan Adu’a ba tare da Allah ya yaye maka ba, walau ciwon ciki, ciwon kai, ciwon kunne ko ma wani irin ciwo ne.
Cikin ikon Allah bayan ta gama yi mata ta ci gaba da massaging kafan har Mammi ta Samu bacci ya ɗauke ta, wani irin ciwon kafa ne wannan Fauxa tayi maganan a zuciyarta tana kallon tarin magungunan na Mammi, daga na Asibiti har na gargajiya zuwa na musulunci, komawa gadon da Fauxa bata yi ba kenan a nan kasa ta kwana se da Asuba taji Mammi na tashinta.
Mikewa zaune tayi tace
“Mammi ya kafan?”
Mammi tayi murmushi tace
“sannu Fauziyya! Sossai na ji daaɗin Adu’ar da kika min kwanana hudu rabona da baccin dare se gashi yau nayi harda mafarki”
Murmushi Fauxa tayi tace
“to bari na sake miki”
Adu’ar ta fara mata yayinda ma ta zuba mata idanu tana kallo, ta rasa me take hangowa a rayuwar Fauxa wadda kowa baya hanga kowa kawai ya tashi Fauxa bata ji, Fauxa kaza Fauza kaza ita Sam banda haske babu abunda take gani a rayuwarta, yarinya ce me tarin ɓoyayyen baiwa amma influence na mutanen dake zagaye da ita ya hana shi bayyana.
Jin za’a shiga sallah yasa tace
“Fauza tashi je kiyi alwala ki tafi masallaci bari nima na miƙe”
Da taimakon Allah ta kai kanta bayi tayo alwala yayinda tuni Fauxa ta fice masallaci, anan tayi sallah ta sake kishingiɗa tana me sake samun wani baccin saboda sauƙin kafan.