Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Wani irin kallo Fauziyyan tayi mata kan ta maida idanunta kanshi jin mai ze ce, se taga ya kauda kai da alama ita yake kallo ganin zata kalleshi ya kawar da nashi idanun, bazata ce ga expression ɗinshi ba amma da saisaitacciyar murya ya furta..
“Gate ban amince ki taka ba tare da izini na ba Fauziyya”
Abunda ya faɗa kenan ya sallameta, ta mike ta wuce ɗakinta ba tare da ta tanka musu ba.
Fatima tace
“Abunda zaka ce kaɗai kenan?”
Ya ɗan miƙe tsaye kan ya ce
“me zan ce to? Babu wadda ta sani anan garin da ze shigo har gidan nan ya ruɗe ta, hakanan tun da ta sanya kafarta cikin gidan nan na yiwa gateman kasheɗin bayan ni da ke kar ya bar kowa ya fita daga gidan nan ko ya shigo idan har ba da sanina ba”
Ganin ze wuce room nashi tayi saurin mikewa
“amma fa kai da kanka ka ce ka ganta a nan garin kenan ai baka san ko akwai wasu bad friends ɗinta a nan ba…”
Ya dakata tare da juyowa ya kalleta na seconds kan ya juya kawai ya wuce ɗakin shi, zama tayi kan kujeran dabas tana sake sake, ta so ya gayawa Fauziyya maganan da ze hana ta bacci wlh akan shaye shaye da yawace yawace da take yi amma ba komai da ita take zancen.
Itama mikewa tayi ta wuce ɗakinta don shiryawa ta dawo turaka.
Samun wuri tayi kan kujera ta zauna tare da ɗaga throw pillow ta ɗaura kan cinyar ta ta zabga tagumi, wai haka zata yi wannan zaman? In aiki ne be dameta ba don horon da ta sha kwanakin nan a gidansu na aiki ba kaɗan bane har ma ta saba, amma bata da waya ba abokin hira, shiru haka ze yiwu kenan? Chan ƙasan ranta kuma maganan Fatima ba ƙaramin kuna yayi mata ba amma ba komai zata yi lokacinta.
TV ta kunna ta rage daren da kalle kalle daaɗi sossai ta ji da ta ga ba wa’azu zuƙa bane, se karfe sha ɗaya ta kwanta don ma ita ba gwanar ci ba ce da dole se ta fita ta nemi abinda zata ci.
Buga kofan ta da aka yi da karfi shi ya tasheta a ɗan firgice, dalll haka aka kunna mata bulbs ɗin ɗakin duka Fararen waenda suke da matukar haske, da sauri ta sanya hannu ta rufe idanunta, duniya ta tsani a kunna mata wuta daga tashi daga bacci.
“Malama tashi ki sama min abunda zan ci karfe bakwai nake da lectures”
Dukda yadda ranta yayi mugun ɓaci bata tanka ba, haka kuma bata ɗaga idanu ta kalleta ba.
“Da ke fa nake magana malama!”
Har lokacin bata yi magana ba tana calming kanta ne, bayan ta gama Adu’ar tashi daga bacci ta sauka kawai ta shige toilet bata ce komai ba.
Se hakan ya kular da Fatiman, a fili ta furta
“kammm ni zaki mannawa hauka? Wato ga mahaukaciya tana magana?”
Kwafa tayi ta fito ta je ta zauna a parlorn saman ta ɗaura ɗaya kan ɗaya tana girgizawa, time ta dibar mata in bata fito ba kuma wlh se ta kai karata wurinshi.
Ita kuwa Fauziyya watsa ruwa tayi ta fito ta ɗan shafa mai da turare kadan ta saka cotton bubu ta fito, a kan kujera ta wuceta ta nufi hanyar kitchen ba tare da ta ko kalleta bane.
“Ke! Ina zaki je? Ba’a shiga min kitchen kije na ƙasa wannan ɗin abincin mijina kaɗai nake dafawa a ciki gudun barbaɗe”
Juyawa kawai tayi ta nufi ƙasa ba tare da tace komai ba.
Dankali ta fere me yawa ta zuba gishiri tuli guda kan ta soye shi yayi kararau ta juye a warmers ta ɗauka ta je ta ajiye kan dining kan ta wuce ta haura.
Har zata wuce ɗakinta Fatima ta ce
“Fauziyya..!”
Juyawa tayi ta nufi dining ɗin saman, ganinshi a ciki yasa ta ce
“Ina kwana”
Kaman yadda yayi mata umarni
“lfy”
Shine abunda ya amsa da kan ya cigaba da cin abincinshi.
Kallon kiran me kika min kawai take yiwa Fatiman, ita kuma se tayi shiru na seconds kan tace
“tunda ni ba zaki gaisheni ba, ina kwana? Fatan kin tashi lafiya?”
Wani irin kallo Fauza ke mata na kina kure haƙurina, ɗaga idanu yayi ya kalleta se tacewa Fatiman
“Ina kwana”
Fatima tace
“lafiya ƙalau ya kwanan bakunta?”
Bata amsa ba hakan ya sa Fatima cewa
“yauwa kin gama abincin ba?”
Kaɗan ya saura zuciyar Fauza ya zo wuya tace
“uhm”
“yana ina to?”
“Kasa”
“ka ji ki, ai anan ne muke karyawa, je ki ɗauko mana”
Seda ta lumshe idanu ta buɗe kan ta juya ta nufi sauka, shi karan kanshi da kallon mamaki ya bita a sanin halinta bazata bi umarnin Fatima kai tsaye haka shiru ba, ko ta fara sauyawa ne… Kafadan shi yayi shrugging kan ya cigaba da cin abincin shi.
Bata jima ba se gata da food flask ta zo ta ajiye kan dining ɗin ta juya zata tafi
“ke bazaki ci bane Fauza?”
Juyawa tayi ta kalleta kawai kan ta juya ta wuce ciki.
Tana shiga ta faɗa kan kujera tana ji kaman ta fashe da kuka sbd yadda ranta yayi mugun ɓaci gashi bata fitar da abunda ke ciki ba, ita kuma haka take in har bata rama abunda aka mata ba ranta yayi ta zafi kenan da kuna.
Kakari taji me ƙarfi se kuma taji ana kiran
“ke! Ke!!”
Ta san ita kaɗai yake kira da ke hakan be sa ta amsa ba, tana kwance kan three seater taji ya turo kofan ya shigo.
“Ke! Bakya ji ina kiranki ne? Ko yadda kwakwalwanki yake a toshe haka kunnuwanki?”
Miƙewa zaune tayi tare da fara kunkuni
“to ai ni sunana ba ke ba….”
Ɗallin bakinta da taji an yi ne ya sakata sakin ƙara tana dafe bakin sbd azabar zafin da ya ratsa ta, hawaye ne ya cika idanunta ta ɗago tana Kallonshi.
Kau da kai yayi yace
“kashe min mata zaki yi? Wani irin jagwalgwalon girki ne kika yin nan? Baki san tana da BP bata cin gishiri bane? Tashi ki wuce mu je”
Mikewa tayi ya sako ta gaba suka fito, Fatima na kwance kan kujera sama sama take numfashi sbd yadda take jin kaman zata mutu, murmushi me kyau ta saki ganinta hakan sarai ta ji yadda ake ta maganan jininta na hawa sossai sbd damuwar da ta sawa kanta na ɓarin da take tayi hakan yasa aka hanata cin gishiri, da gangan tayi labtawar da ko loma ɗaya tayi se ta ji a jikinta.
Da sauri itama ta karasa gabanta ta duka tana cewa
“Ya fati sannu! Me ya sameki haka?”
Harara ta zabga mata kan ta cigaba da numfashin ta hannunta dafe da kai.
Rufeta da faɗa yayi sossai kaman ze daketa, raurau tayi bayan ya gama idanunta na zub da hawaye tace
“Yaya Don Allah kayi haƙuri, ni ban iya bane, ban kuma san tana da hawan jini ba… Jiya jiya fa na zo”
Lumshe idanunshi yayi se ya sauke ajiyar zuciya kawai ya wuce ɗakin Fatima don ɗauko mata hijab su tafi asibiti.
“Na san ba haka kika so ba ko? To mu zuba da ni dake ɗan halak ka fasa, in makirci ne ke jiya kika soma amma Fauza kam ta jima a ajin don ina ga har ta gama ma ta fita da sakamako me kyau”
Jin motsin kaman yana dawowa ne yasa tayi saurin karasawa tana ɗagota tace
“I’m so sorry ya fati”
Hijab ɗinta ya miƙawa Fauza ta saka mata, sakawar ma na mugunta ta mata don seda ta karɓa da kanta ta karasa a hankali.
“Karki ci abincin nan, ki nemi wani ki ci bari na kaita asibiti..”
Kanta kasa tana zub da hawaye ta ɗan ɗaga, har ya kama Fatima a jikinshi sun nufi stairs ya ɗan dakata tare da waigowa kaman ya zamar mishi dole yace
“kukan nan kuma ya isa haka”
Yana kai nan suka fara sauƙa.
Wani kalar dariya Fauxa tayi tace
“gobe zaki maimaita abunda kika min munafuka kawai”
Dining taje ta samu abincin shin ma be gama ci ba ya tashi, ta kara akai ta ci tayi Nak ta tattare wurin kan ta zo ta fara kimtsa parlorn da ba wani datti sbd rashin mutane dayawa a gidan.
Bayan ta gama ta koma ɗaki tayi kwanciyarta cikin kewan jaddanta kan bacci ya sure ta.