Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Jadda da mammi dae sun kwana cikin farin ciki yayinda baba Alhj ya kwana yiwa wan shi Adu’a ya tabbatar ba don shi ba da lamarin Fauza yanzu ya kaishi ƙasa, Ammi ya kira ya mata bayani tashi ɗaya ta nuna Allah ya kasheta wallahi baza ta kara Haɗa zuri’a da Mammi ba an yi mata fin karfi a lokacin fadyaa yanzu kam babu wadda ya isa, har gwara faahim sau dubu da Faizan a gareta.
Baba be kula ta ba ya yi kwanciyar shi don in yace ze biye mata se Amarya ta ji kuma yana so ya sanar da ita ta yadda zata fahimta babu cin fuska ko son kai a wannan tafiyar.
Washegari zaliha ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallar asuba bata samu Fauza ba, neman duniya da nurses suka mata bata cikin asibitin ko da Baba prof da jadda da kuma Aunty Amarya suka iso ana kan nemanta ne.
Alamu dae sun nuna fita tayi sede ina zata da rauni a jiki?
Ita kuwa tana tashi ta mike zaune tana kallon inda suka bare mata a fatarta da take matukar tattali, ranta yayi baƙi kirin da irin wannan tozarci da yayyun nata suka mata, ta tabbata duk gidan maƙiyanta ne banda mammi da jadda da Amminta, lallai abunda suke gudu se ta sake yi in basu kasheta ba ba su cika mugaye ba.
Dira tayi daga kan gadon ko hijab ɗin da ta dauka ganin yadda ya fashe yasa ta cillar, takalmin zaliha ta saka ta fice, abun hawa ta tare se gidansu sakina, ta sa me gadi yaje ya karbi kudin ya kawo mai, sossai hankalin sakina ya tashi da ganinta haka.
Anan tayi wanka ta sauya kaya tayi kwanciyar ta bayan ta ci abinci, duk yadda sakina ta so tayi magana kasawa tayi da ta matsa se ta kawo kuka ta sa, hakan yasa zaliha bare wasu tabs tace
“sa wannan a ƙasan harshen ki duka biyu ki barshi ya narke da kin yi bacci kin tashi bacin ranki ze kau”
Sawa kuwa tayi ta kwanta, a haka tayi bacci har sha biyun rana kan ta farka abu kam ya fi karfin jininta ga shi ta bata overdose ne, tana tashi ta gayawa sakina duk abunda ya faru ta kuma ce tana so ta kunsa musu bakin cikin da zasu saka wuyan ta gabas su yanka, wayan sakina tayi anfani dashi ta kira Zubair luckily ya koma da yau abunda yake so da ta bashi.
Haka ta diro ko mayafi taƙi sakawa kaman ba ɗiyar musulmi ba ta nufi fita, Sakina da kyar ta shawo kanta akan driver ya maida ta.
A farkon layinsu tace ya ajiye ta don tana so kowa ya kalleta yadda su Farhan zasu kara jin haushi, aikuwa kaman ta kimta daidai.
Farhan, Faizan, Faraj, Baba Alhj baba prof da polisawa ne tsaye ana batun yadda za’a samo ta shi Faizan kaman dole ce kawai aka mai na shiga case ɗin zuciyarshi na bashi wurin watsewarta tayi don mashayi daga ranshi ya ɓaci abun shaye shayenshi yake nema ya rage zafi.
Yana cikin wannan tunani ya ɗan kalli hanya har ya ɗauke idanu yayi saurin sake mayarwa ya zuba mata su yana kallo, tun daga nesa zaka san a make take mankas, so yake ya janye hankalin baba Alhj sede yana juyowa yaga duk suma sun zuba mata idanu, ga bandage a jikinta ta sa wani riga da da kadan ya sauka kaurinta, hannunta duk a bayyane gashin kanta a Parke cikin loose bon, Baba Alhj ne ya tafi ze fadi, Baba prof yayi saurin tare shi yace
“Menene haka Sulaiman? A kanka aka fara jarrabawa? Kana so se ka ɗaurawa yarinyar nan abunda ya fi wannan?”
Su Farhan yayiwa kallon duk wa ya janyo? Ba ku ba? Kan ya saki baba Alhj ya fara tattaki zuwa gareta.
Maganganu take maras kan gado tana faɗin laifin babanta ne da yayi mata baki kullum yake kiranta fitsararriya gashi fitsara ta bita, ba su Farhan sun ce zasu mata abunda bazata kara marmarin rayuwar banza ba? To gashi ta kara su sakata gabas su yanke yanzu yanzu zuwa tayi don su gani, Kaman Faizan ze yi kuka don tausayin kanshi yanzu da abunda Babanshi ze Haɗa shi kenan?
Har ɗakinta ya kaita a sashen Jaddah tare da taimakon ta ta shimfiɗar da ita se bacci, duk idanu suka zuba mata.
Jaddah tace cikin karfafa mishi gwiwa
“Adu’ar mu baze taɓa faɗi ba professor, ka kwantar da hankalinka abunda kake shirin yi in shaa Allah shi ze zama silar warakar komai, Allah maji roko ne me jin ƙai ka fini sanin cewa baya taɓa juyar da Adu’a sai de in ya musanya da abunda ya fi alkhairi, ya kuma amsa ta hanyar da tafi kowacce daidai, sadaqa maganin masifa ne, haka kuma Qur’ani waraka ce, Adu’a kuma takobin mumini ne duk bamu daina akan Fauza ba kaga kenan muna da yakinin Allah ze karɓa ko ba daɗe ko ba jima”
Yace
“hakane mama, bana kokonto akan Hukuncin Allah sede a duk sadda zan ɗaga idanu na kalli yarinyar nan jikina yana bani wani abu na daban mama, gani nake ana zaluntarta amma ban san ta ya ba, tausayinta ke ratsa zuciyana har na kan zubar mata da hawayen tausayawa in na kalleta, ba ni kaɗai ba sau ba Adadi Aisha ta min magana makamancin haka akan yarinyar nan”
“komai ze tafi daidai professor in shaa Allah auren da ka Haɗa ze zama sanadiyar warwarewar duk wasu al’amuran ɓoye”
Mikewa yayi ya fita bayan ya tofe ta da wasu Adu’o’i, ko da ya dawo ya nemi Faizan ya rasa don barin garin yayi.
Satin shi uku da komawa Fatima ta sake ɓarin cikin wata guda.
Wannan karon har gida ta zo sbd yadda duk ta ɗaga mai hankali, ta kasa fahimtar komai na Allah ne.
Shi kam ya ma tafi chan wata ƙasa ne hakan yasa dole ba yadda ya iya ya barta ta koma gidan, a gidan bayan mutane shiddan nan har yanzu babu wadda ya san da maganan auren na Fauza da Faizan, a fakaice Jaddah ke mata gyara ba tare da ta sani ba, asalin gyaran shuwa Arab take mata.
Dayake yanzu ko parlorn Jaddah baba be yarda ta wuce ba necon tan ma karasa mata ake yi yasa bata fita rana, skin ɗinta ya kara wani irin kyau da sheki tayi fresh tayi kiba abunta, nasihohi take sha har ta gaji da jinsu amma tayiwa baba alkawarin bazata sake shan kayan Maye ba har abada.
Yanzu wayanta bashi da anfani don tayi ta neman Zubair bata samu se kawai ta jefa shi kasan akwati.
Ko da Fatima ta zo ma sannu be hada su ba har tayi kwana bakwai ranan ne baba ya kirata yayi mata nasihu masu yawa kan ya faɗa mata auren Faizan da Fauziyya da ya hada, ba karamin girgiza tayi da wannan zance ba, tsanar da ta yiwa Fauziyya me yawa ne matuka gashi zata aure mata masoyi ta zama suna shearing komai nashi, abunda ba zata iya amincewa dashi ba kenan.
Ta dawo wurin mamanta hankali tashe cikin matsanancin kuka, Fauza ya sa aka kira mai itama ya faɗa mata, abinka da shiririta irin na fauza dariya kawai tayi ta fito abunta bata taɓa dauka serious bane seda abu ya karato dangi suka fara zuwa nan ne musababbin tashin hankalinta ya fara…
Ko da ta nemi halaka kanta kawai kiran sakina tayi tace ga abunda zata sayo mata ba tare da ita sakinar ta san ita zata sha ba, ta sayo ta bi ribibin en buki ta bata…
DAWOWA LABARI
“FAUZIYYA!!!”
ya fadila ta faɗa tana jijjiga ta da karfi, firgigit tayi tare da ɗago kai se taga babu kowa a jirgin se su uku.
“Me haka? Me yayi zafi da zaki ɓata a tunani haka? Kin san tun yaushe muke tsaye akanki?”.
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba