Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Kowa yana ta kara yi mata nasiha har suka fito a yammacin zasu tafi Abuja inda nan ne gidanshi kuma anan suke zama da Fatima, bata taɓa Tunanin zata yi wani kukan rabuwa da gidan da tafi tsana ba se yanzu da take ji yafi mata sau dubu akan inda za’a kaita a kuma barta chan bata san kowa ba se maƙiyanta, kuka sossai take yi da kyar aka cire ta ɗaga jikin jadda se ta koma na Amminta, daga nan tayi kan mammi ta sha kuka kam, daga karshe ma fa’iza da kullum se sun yi faɗa ta rungume tana kuka sossai, Fatima tuni tana mota.
Cikin sassarfa ya fito daga sashensu ba tare da ya kalli ko sashen inda suke ba ya nufi mota sanye da wasu ɗanyen boyel me taushi da tsada farare sol, hulanshi light ash da fari tangaran ya zauna mishi sossai haka takalmin shi half cover ce me ainihin kyau da tsada ta bayyana Fararen digadiginshi da kaman baya taka kasa.
Baba prof da ya bishi da kallo yana murmushin yadda duk yayi kicin kicin da rai yace
“Faizan!”
Juyowa yayi se yayi kaman yanzu ne ya kallesu alhali tun fitowarshi ya san suna wurin, nufansu yayi kanshi kasa yace
“Na’am baba”
Jadda, momma da Baba Alhj duk babu wadda ya fito Amminta kuma ta juya mata baya, da Yaya Fadeelah da wata ƴar uwar su Baba prof zasu tafi, Kallonsu yayi yace
“ku je ku shiga mota ga mijinta ze zo da ita yanzu”
Kanta ƙasa tana shesheka duk masu rakiya suna tsaye cike da tsakar gidan ana ta mata Adu’o’i.
Hannunta baba prof ya riƙe ya sanya cikin hannunshi a tare suka ɗaga suka kalli baban se suka kalli juna, dukkansu suka ɗauke kai, gyalen ta baba prof ya sake ja ya rufe mata goshi yace
“Allah yayi muku albarka! Allah ya tabbatar muku da farin ciki a wannan tarayya ku je kuna cikin adu’o’inmu a kullum, Fauziyya karki manta duk abunda na ce miki kinji?”
Kai ta gyaɗa, hanya ya nunawa Faizan se ya juya riƙe da ita suka nufi mota, dole ya biye mata suna tafiya kaman ba zasu taka ƙasa ba don haka tafiyar ta, idanun mutane da Baba ya sanya ya saka hannu ya buɗe mata gefen ta shiga ya gyara mata kayan ta kan ya rufe kofar fatima dake gefe ɗaya ta ja tsuka me karfi, gaban motan ya shiga Farhan ya ja suka fice kan na su yaya fadeela ya biyo bayansu.
Basu tsaya ko ina ba se Airport, suna parking ya fita ya shiga ciki yana waya kaman yadda tun da suka fita daga gidan waya yake, Fatima fushi take dashi kaman shine ya ɓarar mata da ciki hakan yasa itama be kula ta ba, yaya fadeela ce ta zo ta riƙeta suka shiga ciki Fatima da Ya kaka suka biyo su cikin mintuna ya gama komai, ya zo ya Mikawa kowa tickets nashi suka wuce suka yi checking suka shiga jirgi.
Banda ajiyar zuciya babu abunda take saukewa, ba wannan ne karonta na farko shiga jirgi ba Dukda duk gidansu babu wadda ya sani sede tana yawan zuwa Abuja da friends nata kuma da jirgi hakan yasa bata ko nuna alamar tsoro ba, jirgin na daidaita a sama ta yaye gyalen ta sbd zafi, daga inda take tana hangar yadda Fatima ta kwanta a jikinshi yana riƙe da hannunta da alama rarrashi yake.
Kau da kai tayi tare da tsaki tana kallon window ta fara Tunanin rayuwata Daki-daki….duk me ya jawo waennan abubuwa da suke faruwa? Shin wacece ita tun daga farkon fari?
A take tunaninta ya daka tsalle yayi baya daga inda ta fara sanin wacece ita…
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what’sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Uku*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA❤️**
*SOME YEARS BACK*
“Fauxa! Fauxa!!”
Muryar ke fitowa daga tsakar wawakeken gidan yana amsa kuwwa a duk saƙo da saƙo na cikin gidan, har matsakaiciyar matar ta iso kofan ɗakin tare da yaye labulen sbd kofar dake wangale bata fasa kiran sunan ba.
Turus! ta ja ta tsaya tare da wara ido Kalmar
“kan uban chan!” Ya fito daga matsakaitan laɓɓanta.
“Fauziyya! Ashe sunanki daaɗi yake min da zan kama in yi ta kira kina ji ki min banza? Ni sa’ar ki ce? Ko kin maida ni irin su fa’iza ne?”
Kyakyawar matashiya ce me ɗauke da coffee colour skin, irin skin ɗin nan da ake kira glass skin da ake wa magana na zaune saman bed me yanayi da gadaje irin na hostel hannunta chocolate ne na bounty tana sha, a hankali ta ɗago manyan idanunta da kwayar suke kalar Grey ta watsawa matar tare da motsa kyawawan siraran lips ɗinta wadda ya saka cikakken girarta me cike da gashi suka haɗe wuri guda cikin kunkuni tace
“Ai an san inda mutum yake ba se a zo a same shi ba, sai an yi ta mishi kiran kasuwa!”
Ta karasa da murguɗa baki.
Wara idanu matar tayi tace
“Me kike cewa?”
Da karfi tace
“ni ban ce komai ba, gani..!”
Tayi maganan tana dirkowa ba tare da ta bi matakalar da aka tanada don hakan ba ta je gaban matar ta tsaya kerere, tsiririya ce me kananun shekaru bata da kauri da matukar wuya ta haura 16yrs karamin shape da take dashi ya haɗu da tsawon ta ya bata wani kyaun sura na musamman, manyan idanunta da dogon hancinta zuwa lips ɗin ta sun taimaka wurin fitar da ainihin kyaun da Allah yayi mata musamman in ka Haɗa da yanayin skin color ɗinta.
“Ki wuce ki je ki yi min wanke wanke tunda zuwa Islamiyya ya gagareki, Fatima bata samu tayi ba sbd lokacin islamiyya da ya shiga”
Baki ta turo tace
“ni ba zan yi wanke wanken da ba na rana na ba fa! Me anfanin rabawar to in an san za’a zalunci mutum? Ni de! Ni de……”
Ɓassss haka karar Marin da aka yiwa bakinta ya bada sauti da sauri ta ɗago don ganin waye ne ta sauke mishi tijarar ta da be bar kan kowa ba, se suka Haɗa idanu da Ya Farhan zaro mata idanunsu iri ɗaya yayi yace
“fitsararriya ana magana kina yi, ki wuce ki je maza ki kama wanke wanken nan tun ban sauya miki kamanni ba..”
Baki ta zumburu tana kunkuni
“mugu, azzalumi..!”
“Me kika ce?”
Tace
“cewa nayi to bari na fito”
Ta Raɓa ta wuce tana ci gaba da kunkuni musamman da taji Aunty Amarya na cewa
“da baka kai mata hannu ba ai Farhan, yaran ne se Adu’a yanzu”
“Munafuka, guntuwa..!”
Ta faɗa bayan ta sauka tana bin kan interlocks da suka zagaye sashen wadda har daga wajen karamar kofar da nake hange a buɗe su ke zube.
Tsakar gidan an yi kaman roundabout na interlocks inda tsakiyar kyakyawar bishiyar Almond wacce aka fi sani da umberalla ta kawata gidan, chan gefen kitchen da store ɗinsu aka yi wurin wanke wanken dake lailaye da tile, Fatima ta riga ta gama Haɗa wanke wanken har ruwa da komai, farawa tayi tana me cin alwashin wlh ranar wanke wankenta baza tayi ba sede Fatiman tayi.
Tana wanke wanken tana ta bubbuga kwanuka har Seda Ammi ta leƙo tace
“ke kam lafiyanki kuwa?”
Kallon farar matar tayi wacce suke ɗan yanayi ta tsawo da hanci tace
“ƙalau Ammi”