Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Kusan tambayar da kowa ke yi kenan a ranshi har Faizan, Baba prof karan kanshi a dame yake don wannan kowa ya ji ya san ba Alkhairi bane aikin asiri ne to amma wa ze mata? Sun san dae Fatima ciki da bai yarinya me natsuwa da hankali, ta taso a gidan cikin tarbiya irin na yaran gidan to Alamar tambayar tana kan waye?
A hankali Faizan ya sa hannu ya yanke wayar, se ya miƙe ya nufi ɗakinta.. Ya jima tsaye yana karewa ɗakin kallo kan ya fara gyarawa a natse har ya gama tsab tsab kaman tana nan.
Bayan ya saka turaren wutan da ta saba sakawa yaje kan kujera ya kwanta idanunshi na kallon sama.. Fatima ce tayi knocking ta shigo.
“Abinci fa ya gama ɗazu na leƙa ka a ɗakinka na samu kana bacci!”
Idanunshi ya buɗe ya zuba mata Su kawai ba tare da ya ce uffan ba.
***
A yola kuwa cike da damuwa suka yi ta Rarrashinta har tayi shiru, Baba prof ya rubuta abubuwan da bashi dashi a gidan ya ba Farhan akan ya je ya samo mishi ze Haɗa mata maganin kariya.
Farhan ya mike ya tafi, Ruwan zamzam ya bata wadda akwai ayoyi ciki ta sha yace taje ta kwanta ta huta kar tayi Tunanin komai.
Mikewa tayi ta nufi sashen Jaddah, Amminta da tun aka fara bata ce komai ba se lokacin tayi kwafa ta mike kawai ta fice duk da kallo suka bita.
Sun ɗan kara tattaunawa akan matsalar ta sede basu bada kofan zargi ba sun dae ajiye kila akwai aljanin da ya aureta ko kuwa suna so su shafeta.
Farhan ya dawo da aikan baban, bawan Allah daren gabaɗaya be runtsa ba seda ya karance baqara kap a cikin ruwan zamzam da ya zuba mishi garin bagaruwa, ya cigaba da karatun ayoyi har uku kan ya gama se kawai ya hau jera nafilifili da Adu’ar Allah ya bayyana duk wani abunda ke boye akan Fauza sbd tun farkon fari dama shi hankalinshi be bashi haka kawai take ba.
Kaman yadda be yi bacci ba haka Fauza da Faizan, bayan dogon tunani kusan a tare suka miƙe suka fara jela nafilfili haka jadda ma tsakiyar dare ta yanke baccinta dama tun lokacin ƙadangaren nan bata wani sakankance ba Fauza take nemawa sauƙi a wurin Allah da ko ma menene yake rayuwarta…
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
29
*BAYAN SATI ƊAYA*
Yau satin ta kenan da zuwa garin yola, kuma sossai take jin daaɗin garin sbd yadda kowa ke ina za’a saka ina za’a ajiye da ita, daga mammi, Jaddah, babanta, Baba prof, su ya Farhan da su Fa’iza duk ji da ita suke kaman me sede in bata ambaci abu dayansu ya ji ba haka za’a je a nema mata, yanzu ita da kannenta ba duka ba zagi se jansu a jiki da take yawan yi, magungunan ta kuwa kullu yaumin safe da dare cikin kariya take na irin ayoyin da Baba prof ke mata anfani dashi, duk da waennan gabaɗaya a maimakon ta kara ƙiba tayi kyau ta Daena Tunanin komai se farin ciki duk hakan be yiwu ba.
Ta ɗan zube kadan sbd yawan tunani, be taɓa kira ya ce a bata ba kuma wallahi bazata yi karya ba zuciyarta ta riga ta gama yaudararta akan Faizan bata san ta kamu da mahaukacin soyayyarsa ba se da suka nesanta da juna ta san yana fushi da ita abunda ke hanata walwala kenan gashi ita kuma ta kasa ɗaga waya ko na Jaddah ne ta kirashi.
Tana kwance a parlorn na Jaddah a kan kujera Fa’iza ta shigo tana cewa
“Fauza kin yi bacci ne?”
Jaddah dake fitowa daga ɗakinta tace
“Ina ita ina lafiyar baccin yamma Fa’iza?”
Tana kallon fa’izan tace
“Ya aka yi ne?”
Fa’iza tace
“dama zan fita ne chan farkon layi zan karɓi handout ɗina wurin wata friend ɗina shine nake so in ji har yanzu kina sha’awar cin farar ne? Don ba’a rasawa ta wurin”
Mikewa tayi zaune tace
“Jaddah Eyya bata ɗari biyu in tana dawowa ta sayo min fara”
Jaddah tace
“Toh”
Ta fara duba gefen zaninta ta fiddo ɗari biyar, tana kallon Fauza tace
“To da kwanciyar nan ko zaki bita ne Fauziyya? Tunda kika zo ko gate baki kara leƙawa ba kika ɗan fitan kema zaki ɗan ji daaɗi”
Kaman zata ce bazata je ba se Fa’iza ta kama magiya akan su je tare ɗin wlh dama tana ta Tunanin tafiya ita kaɗai su faazila na islamiyya, ya Falaq kuma tace ita ba sa’ar mata rakiya bace.
Mikewa tayi kawai taje ta wanke fuskanta ta ɗan gyara kan ta fito tana ji su Jaddah na maganan shiru shirunta ko ciwon ne oho. Fa’iza tace
“ko tana kewar mijinta ba Jaddah?”
“Zaki tashi muje ko zaki zauna gulmata in fasa rakiyar?”
Ta faɗa tana maka mata harara duk dariya suka yi tuni ita tayi gaba, fa’iza ta miƙe da gudu ta bi bayanta.
A natse suke tafiya tunda suka fito taga motar dake bin su, fa’iza dae bata kula ba, mai motar kuwa tun yana bin su a baya a baya har ya iso saitinsu ya musu horn.
Kallo ɗaya tayi mishi ta ɗauke kai suka cigaba da tafiyar su, Fa’iza ma ba gwanar kula irin su ba ce se kawai suka maida kansu hanya, har suka isa gidan mai motan nan be bar binsu ba basu wani jima chan ba suka fito, suka tsaya suka saya fara tana lura da wasu dake gulmarta ana ta mamakin Fauziyya ce shiru shiru haka? Ita dae bata bi ta kansu ba suka ɗauki hanyar gida.
Mai motar nan again ya cigaba da bin bayansu, gab sun iso farkon layinsu ganin bazasu tsaya ba gashi yana hangen gidansu yasa yayi saurin parking ya sauka ya biyo bayansu
“Fauza…! Fauza!!”
Fa’iza tace
“ke fa mutumin nan ke yake kira”
Yi tayi kaman bata ji ba kaman daga sama taga mutum a gabanta.
“Fauziyya ni kike wulakantawa? Ni ne fa Zubair ɗin ki”
Ya karashe yana nuna kanshi.
Tana Kallonshi tace
“Na gane ka mana amma bani da business kuma da kai Zubair hakan yasa ban ga anfanin kulaka ba, please ka kyaleni karka manta da Aurena”
Hannun fa’iza ta kama suka fara yunkurin wuce shi ya sake shan gabanta..
“Fauza akan ki rayuwata ta shiga cikin barazana, a kan ki saida na shafe sama da watanni huɗu a prison amma sakamakon da zaki yi min kenan? Wallahi gayen chan ba son ki yake ba, na rantse miki da Allah ina son ki kuma in har ba zan sameki ba saide kowa ya rasa”
Ya faɗa cikin alwashi.
“Oh haka kace?”
Tayi maganan tana Kallonshi.
Yace
“eh don ban ga maraba ta da mugun yayankin nan ba, shi yayi min cune ina tare da drugs da gomnatin Nigeria ta hana Anfani dasu ya kuma san idan har an kama ka kisa ne amma ya cuna ni ina dawowa daga Russia aka kamani, ba don connections ba da se wani ba ni ba Fauziyya duk a haka kika zaɓe shi over ni?”
Tana shirin magana kenan idanunta suka faɗa cikin nashi, wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riske ta har bata san ta matse hannun fa’iza dake cikin nata ba, tsaye yake sanye da kananun kaya riga da wando daga gani ka san sun ci kuɗi hannayenshi zube a aljihu ya tsaresu da firgitattun idanunshin nan masu rikitar da ita yana kallo..
Ɓacin rai take hanga shimfide a fuskanshi me tsanani, yaushe ya zo? Ta jefawa kanta tambayar da bata san amsar shi ba, da sauri ta zagaye Zubair ta nufe shi da nufin yi mishi bayani ba abunda yake tunani bane, tana isa kawai ya sanya hannu ya fincike hannunta suka yi gida.
Jan ta yake ba tare da ya damu da saurin da yake ɗin yayi mata yawa ba. Basu zame ko ina ba se room ɗinshi da karfi ya jefa ta kan kujera yana kallonta zuciyarshi kaman ya Faso kirjinshi ya fito sbd yadda yake hawa da sauƙa na bacin rai…