Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Dafa kafadanshi Faisal yayi ya bubbuga alamun rarrashi kan suka miƙe suka fito se ga Jafar shima suka haɗu suka fara yawon nemanta da polisawa, a Airport babu jirgin yola da ya tashi a ranar ma gabaɗaya ya gayamusu amma basu yarda ba seda suka je suka gama binciken su kan suka nufi tasha…

***

Ita kuwa Fauza bazata ce ga takamammen Tunanin da take yi ba, Sam kaman makuwa tayi ne ko yaya haka dae ta miƙi hanya ta tafi sossai Dukda wani irin sanyi da ake zabgawa na asuba, bakin wani masallaci ta zauna ana sallar asuba limamin na karatu cikin Suratul baqara ayoyin ƙarshe, a hankali take jin natsuwa na zuwa mata, itama ta karɓa taci gaba da binshi har ya kai karshe yayi ruku’u.

Da sauri ta miƙe ta shiga ciki ta samu ruwa tayi alwala kan ta gabatar da sallar itama nan fa ta ji bakinta ya iya fara ambaton Allah amma zuciyarta har lokacin baƙi kirin babu abunda ta tsana irin Abuja da gidan Faizan.

Fita tayi daga masallacin ta tafi ta tari taxi yana tsayuwa tace
“Park zaka kaini”
Yace ta shiga, tashar Jabi ya kaita.

Ta biya shi sbd akwai kuɗi a jakan, taje ta shiga mota nan da nan motar yola ya cika suka ɗauki hanya, Seda ta tabbatar sun bar yankin Abuja kan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya wani wahalallen bacci ya ɗauke ta.

***

Su kuwa tashar mararraba suka fara zuwa duk motocin yola babu irin sunanta ma kuma duk yadda ya musu misalin kamanninta suka ce basu ga me irin kamannin anan ba.

Daga nan Suka yi dei-dei park nan ma neman duniya da kwatance suka ce basu ganta ba, suka nufi jabi Dukda shi kam Faizan hankalinshi Sam be bashi gida ta tafi ba sbd be san abunda ya faru da zata tafi gida ba haka dae suka je, aiko first turn da aka duba list se ga sunanta, kurawa sunan idanu yayi kwarai itace ma ta rubuta da hannunta don ga rubutunta nan zarzar.

Me makon yayi farin ciki ba ɓata tayi ba se wani sabon ɓacin rai ya ziyarceshi, ta ɗaga musu hankali a banza…
“Karka ɗauki fushi ba tare da ka san dalilin ta ba Faizan”

Faisal ya faɗa a sadda suka nufi gidan Faisal ɗin, Jafar ke tuka su da motar Faizan ɗin, sun riga sun sallami police.

“Hmmm”
Shine abunda kawai ya iya cewa tare da kwafa.

Har suka isa gidan Faisal matarshi ta gabatar musu da abincin be iya cin na kirki ba, barin ma da ta tambayi lafiyar Fauza ji yayi kaman ya tashi ya bar gidan.

Haka dae suka ta lallaɓa shi har Jafar ya maida shi gida, ɗaki kawai ya shiga ya zube yana kallon POP duk Tunanin duniya be ga abunda yayiwa yarinyar nan da ta zaɓi daga mai hankali haka ba, shine ma za’a ce ya dace yayi wannan fushi da ita tunda ta aikata mishi laifi har sau biyu, amma don ta mugun raina shi shine ta kama hanya ta tafi yola, shi kuwa ze nuna mata ɗan halak yake.

***

Zaune Jaddah take ta idar da sallar magrib kenan taji sallama da murya kaman na Fauziyya, ɗaga kai tayi tana jiran a shigo parlorn kaman daga sama kuwa ta ganta tsaye daga bakin kofa tana kallonta.

“Fauziyya!!”
Jaddah ta kirata cike da dumbin mamaki.

“Faizan be ce mana kina zuwa ba, wani irin zuwa ne haka? Baki da lafiya ne?”
Da sauri ta karasa ta kwanta jikin jaddar ta fara kuka, shafa bayanta kawai Jaddah ke yi, yin duniyan nan ta ƙi tace komai.

“Kin yi sallah?”
Ta girgiza kai
“to tashi kije kiyo alwala ki zo kiyi sallah, tare da Faizan kuke?”

Girgiza kai tayi.
“A motan kasuwa kika taho?”
Ta gyaɗa kai.

“Faizan ɗin ya sani?”
Girgiza kai tayi.

“To tashi je kiyi alwala”
Mikewa tayi ta nufi ɗakin Jaddahn a chan tayi alwala tayi sallah a cikin ɗakin kawai ta kwanta shiru, babu abunda yake mata kai kawo a rai irin daren jiya, ya yaji da ya tashi be ganta ba? Ita dae babu abunda aka mata amma ta san ta tsani gidan da garin gabaɗaya.

Har aka yi isha ta tashi ta gabatar tunaninshi kawai take yi.

“Fauziyya taso ki zo kici abinci”

Mikewa tayi ta fito, tun tea ɗin jiya ne cikinta kuma har yanzu bata ji tana sha’awar cin wani abun ba, ruwan zafi Jaddah ta fara bata kan ta saka mata tuwo da miyar lalo da yaji haɗi ta bata.

Kaɗan kawai taci ta ture, Jaddah tace
“kin koshi?”
Kai ta gyaɗa.

“Tashi muje iyayen ki na son ganinki”

A tare da Jaddah suka nufi parlorn baba prof, Ammi, mammi, Baba prof, Baba Alhj se su ya Farhan ne zaune a ciki sauran matan gidan duka ba’a gayyace su ba.

Bata kalli kowa ba ta karasa gaban baba prof dake daga kan kujeranshi ta zauna daga ƙasa kanta a ƙasa, daga babanta har yayyinta wani irin kallo suke aika mata sbd ko da Jaddah ta gaya musu zuwan Fauza duk sun ajiye wani abun tayo, ko tayiwa Faizan ɗin ya koro ta.

Mammi kuwa kallon yadda ta ƙara kyau da haske take ba laifi Abujan ya karɓeta sossai alamun dae hankalinta a kwance yake kan yanzu ɗin.

Baba prof yace
“Fauziyya..! Se kawai mu ganki ba sanarwa? Ke da wa kuka zo?”

Shiru tayi, Jaddah tace
“Tun fa bayan sallama da tayi bata sake cewa komai ba professor”

Ya dube ta yace
“Faizan ne ko?”

Ta girgiza kai
“Toh Fatima ce?”

Nan ma ta girgiza kai.

“Ke don ƙaniyarki ana magana bazaki buɗe baki kiyi magana ba? Me ke damunki ne? Idan duka babu kowa to uban me ze sa ki bar gidanki ki kamo hanyar Abuja ba tare da kowa ya sani ba? Amma shi mijin naki ya sani?”
Cewar baba Alhj cikin zafi.

Kuka kawai ta fara kan ta girgiza kai.
Wayanshi ya fiddo ya kira Faizan ya sa a handsfree.

Yana kwance salla kawai ke ɗaga shi ko ruwa be sake sha ba, Tunanin duniyan nan yayi be san me ya saka yarinyar nan tafiya ba, ganin kiran baba Alhj ya sa ya san ta isa gidan.

Ɗagawa yayi cikin muryarshi da yayi sanyi sossai yayi ƙasa kaman me jin bacci ko wadda ya tashi daga baccin.
Cikin girmamawa ya gaida shi, bayan sun gama gaisuwa baba Alhj yace

“Faizan kawai se muka ga Fauziyya kaman daga sama mun yi mun yi tayi magana kuma ta ƙi shine nace bari na kira ka kila kai ka san abunda ya sa ta bar gidan ta biyo hanya”

A natse yace
“Ko ɗaya baba, nima bani da masaniyar barinta gida jiya tayi zazzaɓi kuma har karfe ɗaya na dare na bar ɗakinta, na tashi da safe kawai na neme ta na rasa har police station mun je da su Faisal sbd ban san me yasa zata tashi kawai ta tafi gida ba tare da laifin tsaye ba bare na zaune, a chan ne cikin bincikensu muka je har tasha muka ga sunanta cikin passengers ɗin yola, time ɗin karfe kusan 2 na rana shiyasa ma ban kira ku ba”

Duk kallonta suke, tana sheshekar kuka a hankali, shima kuma yana jinta.

A hankali yace
“Baba ku barta kilan akwai wani abunda aka yi mata anan ɗin in ta huce zata yi magana amma please ban amince kowa ya taɓamin ita ba”

Ƙara karfin kukanta tayi, se a lokacin ta buɗe baki ta fara magana
“Babu wadda ya min komai… Ni baba kawai na tsani gidan ne, na tsani garin…! Baba ji nayi in ban bar garin ba zan iya mutuwa… Yaya Don Allah kayi hakuri nima ban san sadda na fita ba..”
Kuka ne ya ci karfinta.

Baba prof ya dafa kanta yace
“kiyi shiru Fauziyya, yi hakuri bar kukan nan… Kin yi wani mafarki ne? Ko wani abu ya faru kan kika ji bakya son Abujan?”

Yana kwance lub yana sauraren ta, a hankali ta basu labarin abunda ya faru na tun tsakiyar dare bata yi bacci ba, bata samu natsuwa ba kuma seda ta bar garin wlh ko sunan garin bata sha’awar taji an kira.

Rarrashinta baba prof yayi tayi akan ta bar kukan haka, ita damuwanta tana ta ɓata mishi rai kusan kwana huɗu kenan koyaushe ranshi a ɓace sbd ita, Baba Alhj yace
“Toh me ke faruwa ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected