Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what’sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Shidda*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA❤️**
“Wa’alaikumussalam warahmatullah sannu da zuwa Mammi”
Cewar Fauxa tana me sakin murmushi.
Jaddah ma sannu Da zuwa ta mata, Seda ta amsa na Jaddah kan tace
“Fauxa ke kam ba zan amsa ba, riƙe kayan ki”
Dariya suka yi duka tace
“yi hakuri maa in shaa Allahu zan zo”
Tace
“na gaji da ji, ke kam gidan mu kaman wadda aka yiwa farraku dashi idan ba’a compound ba ko nan sashen Jaddah ba’a ganinki Sam?”
Dariya kawai take yi, wlh ita tana rasa dalilin da yasa take kasa shiga sashen na Baba prof, duk matanshi ma dama banda gaisuwa Mammi ce kawai take sakewa sossai, tana son matan ba tare da ta san dalili ba.
“Ina yini Jaddah? Fatan mun sameku lafiya?”
Cike da so Jaddah ta amsa mata, duk cikin surukanta babu mafi soyuwa a gareta irin Aisha, matar ta dabance cikin mata, tana da kawaici sossai gata da fara’a bazaka taɓa ganinta bata murmushi ba, tana da son mutane da jan kowa a jiki bata damuwa da kai nata ne ko ba nata ba, tana da kirki fiye da zato, duk cikin matan na Baba prof babu me shiga kitchen da kanshi yayiwa Jaddah girki na musamman ya kuma tako ya kawo ya zauna suyi hira sossai irin Mammi.
Dukda tana yawan fama da matsanancin ciwon kafa se ta kwana biyu uku ma bata iya tafiya idan ciwon ya tasar mata amma hakan be sa tayi kasa a gwiwa wurin kula da mijinta da surukanta ba, kuma ita da kanta take taya baba prof kula da mahaifiyar tashi mace ce da a duk lokacin da mijinta ze shigo da wani abu a Leda bazata taɓa karɓa ba se ta tambayeshi ina na Jaddah? Idan har ya manta ko be saya ba sbd ganin ta girma da abun ko wani abu haka zata sa ya koma ya sayo, tana da wani ƙima na daban a zuciyar mutanen gidan musamman mijinta da surukuwarta.
“Aisha ya ciwon kafan? Fatan kin ji daaɗin maganin nan na Gamborun gala?”
Tana murmushi tace
“wlh na ji daaɗinshi sossai Jaddah, kafa yayi sauƙi sosai”
Jaddah tace
“Toh Allah ya qara afuwa”
Suka amsa da Ameen.
Chan cikin hiransu Jaddah tace
“ni kam Aisha kina ji daga wurin wannan Miskilin nawa kuwa? Kwana biyu be kirani ba fa”
Maa tace tana murmushi
“eh Jaddah, ya ce min ze shiga ƙasar da bashi da simcard ɗinta idan har ze fi kwana biyu to ze saya Sim ɗin sbd mu ji lafiyar shi idan kuma ba ze wuce hakan ba in ya bar ƙasar in shaa Allah ze ƙira”
Jaddah tayi tsaki tace
“ba ga irin ta ba, mutum ne kullum a sama kaman tsuntsu fisabilillahi idan ya zo nan fa ya zube Sima simai se ki dauka kamfanin mtn ne, wani idan ya manta na wace kasa ce kuma be da lokacin gwadawa sede kiji katttt ya karya ta”
Mammi na dariya zata yi magana kenan Fauxa ta miƙe Tsam tayi ɗakin Jaddah fuskanta babu yabo babu fallasa, da idanu duk suka bita Seda ta shige kan Jaddah ta zabga tagumi cikin jimami.
Mammi tace
“Jaddah Dan Allah ki dena sa damuwa a ranki sbd yaran nan kar kije wani ciwo ya kama ki, har yanzu dukkansu yara ne in Shaa Allah gaba ko ance su yi baza su yi ba”
Jaddah tace
“se yaushe kenan Aisha? Karki manta Faizan ya baiwa Talatin da biyar baya wannan ta fi sha shida amma ace se gaba? Wani gaban kuma bayan wannan? Wlh Allah ya gani babu abunda ke ci min tuwo a ƙwarya irin tsananin rashin jituwar yaran nan, har tsoro irin ƙin da suke yiwa juna yake bani kwata kwata ɗaya baze taɓa bada fuska ayi maganan ɗaya a gabanshi ba?”
Mammi tace
“ni na fi ganin laifin shi babban kwabon nasu ai, na yi faɗa har na gaji amma ya kasa fahimtata”
Jaddah tace
“ya Allah ka kawo mana karshen wannan abun nasu”
Mammi ta amsa da Ameen suka kama wani hiran kuma se dab magrib kowa yayi alwala suka tafi masallaci a tare.
Bayan kwana biyu
Tunda ta tsefe kanta bata yi kitso ba gashi har yau Sunday, barta dae da neman tsokananta wadda bata rabo dashi, ita da fa’iza ce tafe suna hira sbd duk gidan babu wacce suke shiri kuma suke ƙaunar juna kaman fa’iza babu wacce kuma ta tsana irin Fatima in ka cire Faizan.
Abun nata kaman jinnu, tana son fa’iza sbd haƙurin ta ta kan yi hakuri da duk wani halinta tana yawan kare ta, in kaga sun yi faɗa to akan Fatima ne, Fatima na son nuna mata uwarsu ɗaya da fa’iza ita kuma ta tsani hakan, idan kuma fa’iza tace mata kar ta biyewa Fatima su yi ai jinin dake yawo a jikinta shine yake yawo a nata jikin tunda uba suka Haɗa se ta ce ai fa’iza ta goyi bayan Fatima alhali Agola take a gidan Anan zasu yi faɗa su Rabu Toh Fauxa da zuciya se ayi kwana biyu bata huce ba hakan yasa shirin su da fa’izan yake yawan ja baya.
Sashen Jaddah suka shiga tana zaune tana jan chasbi Fauxa ta zube kan kujera tace
“Jaddah wainar fulawa nake son ci na manja da yaji me tafarnuwa”
Jaddah tace
“se ki ci ai, ni kam ban yi tunanin akwai fulawa a gidan nan ba”
Fa’iza tace
“kash! Ya kenan Fauxa gashi namu ma babu ya kare”
Mikewa Fauxa tayi tace
“mu je wurin Mammi mu yi, dama wlh tun jiya ban je na gaisheta da ciwon kafan nan nata da ya tashi ba”
Ficewa suka yi Jaddah bata ce komai ba har suka fice, ko da suka isa a ɗaki suka sameta kwance a ƙasa an shimfiɗa mata bargo me taushi da pillows, ƴar yayarta da zata ɗan girme su da take hannun ta tun bayan auren farida ita ke taimaka mata tunda bata karatu.
Sashukan nan basu da maraba da sashen su Fauxa, se na kitchen da akwai cikin kowanni sashe saɓanin nasu, se kuma na yawan ɗakuna wadda nan kofa biyu ke fuskantan biyu, na Mammi ne na farko wadda babban parlor ne sossai da kitchen da ɗakuna biyu, hakan ne kuma a kowanni ɗaki, sannan akwai kitchen na waje da kowacce me girki a sashen take girki ranan girkin ta, tsakar gidansu bishiyar cashew ce me ni’imtacciyar inuwa.
“Fauxa yau ke ce a sashen namu? Lallai za’a yi ruwa da kankara”
Fauxa na murmushi ta zube kasa tace
“sannu Mammi ina yini? Ya kafa?”
Mammi tace
“Alhamdulillah Fauxa da sauki sossai har ɗazu ma na taka zuwa toilet”
Fauxa tace
“Allah ubangiji ya ƙara sauki”
Da Ameen ta amsa, fai’za ma ta gaisheta.
Fauxa tace
“Mammikina da fulawa? Wainar fulawa nake son yi bamu da fulawa haka Jaddah ma”
Ta karashe tana karya wuya
Mammi tace
“Ah Kice abunda ya kawo ki kenan ba zuwa na musamman da kike cewa ba”
Tana dariya tace
“Allah ba haka bane dama nayi niyyar zuwa”
Mammi tace
“ba za’a rasa fulawan nan ba ku duba a kitchen na cikin nan se kuyi, dama akwai yaji da Zuwaira(kanwar ta) ta kawo min ma jiya da alama ze yi daaɗi”
Cikin jin daaɗi Fauxa ta mike, fa’iza ta bi bayanta suka yi kitchen.